Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yarda take kuka kamar zata shid'e, sai taji ta bata tausayi duk da rashin kunyar Rahmatu tana son 'yar uwarta kawai bata nunawa ne saboda tasan halin Inna. Karasowa tayi kusa da Hibbah tace "Hibbah meya faru? Me kika yiwa baba yace kibar masa gidansa? Mene a goshinki?" Kukane yaci k'arfinta ta kasa magana, daga cen suka jiyo muryar inna lami tana cewa "karuwa ce mazinaciya fasik'a har gida take kawo su, yarda taga uwarta nayi." Zaro ido waje Rahmatu tayi tace "karuwa fa kikace Inna?" "Eh karuwa ce da kwarto aka kamata," inna ta bata amsa. Shiru Rahmatu tayi ta kalli Abu tace "Abu a gabanki akayi?" Da Abu batayi niyyar amsata ba, amma kanin yarda ta damu da Hibbah yasa ta Girgiza kai tace "a'a nazo dai na ganta ta fito da gudu daga dakin a gigice," Rahmatu tace "kinga kwarton?" Hibbah kallon ta takeyi da mamaki saboda Rahmatu bata tab'a nuna damuwarta akan Hibbah ba, ba Hibbah kad'ai ba harsu Abu da inna lami mamaki take basu. Abu ta kalleta tace "eh na ganshi," da sauri Rahmatu tace "waye?" "Sale direba ne," "sale direba?" Rahmatu ta maimaita tana kallon inna wadda yanayinta yad'an sauya tace"Anya inna baki da masaniya akan wannan abun kuwa?" "A gidan uwarki nake da masaniya?" Inna ta fad'a tana yi mata dak'uwa tace "malam yarinyar nan idan fa bazata bar gidannan ba ni Zan tafi" baba yace "kafin na irga uku kibar min gida" Rahmatu da sauri tace "allah baba kayi bincike naga fa inna dazu da sale a kofar gida." Gaba d'aya kowa ya waiga yana kallon Rahmatu, da sauri inna ta k'araso kusa da Rahmatu ta buge mata baki sannan ta fara janta, ciccijewa Rahmatu ta shigayi tana cewa "wallahi sai na fadi gaskiya, baba kayi bincike kafin ka yanke hukunci, da sa hannun inna a cikin wannan abun....." Kuma buge mata baki inna tayi tare da cewa "wallahi malam idan na kuma maimaita Hibbah ta bar gidannnan to ni zan barshi." Jin haka yasa baba da hanzari yazo gaban Hibbah yana masifa "ki tashi ki fita nace koh?" Cikin sark'ewar murya Hibbah tace "baba ka tsaya kayi bincike....." "Bazan yi ba d'in mai bak'in hali ki fita," ya buga mata kafa "baxa ki tashi ba so kike ki kashe min aure?" Ya kuma Kai mata duka. Ganin yana shirin ji mata ciwo yasa su dije da Abu suka d'agata don ta kasa tashi. Dak'ar take takawa har suka je bakin k'ofar fita juyowa tayi ta kalli baba taga ashe shima ita yake kallo, cikin murya mai rauni tace "baba me yasa zaka yankemin hukuncin barin gidanka koda ace lefin da kake zargina dashi na aikata? Baba ka rabani da mahaifiyata mai k'aunata, yanzu kuma ka rabani da gidanka bayan kuma idan na barshi babu inda zani nan d'inne kawai muhallina, me yasa baba kake son kuntata min? Me yasa kake son na rayu cikin kunci da kad'aici? Kafison *RAYUWA*ta ta lalace? Me yasa baba? Me yasa.........." Kukane yaci k'arfinta. Shi kuwa baba jikinshi yayi sanyi bakinshi kuma yayi nauyi ya kasa ce mata ta dawo. Su Abu ne suka jata suka bar gidan a k'ofar gidan Hibbah taja tunga ta tsaya tana kallonsu d'aya bayan d'aya hawaye na sintiri a fuskarta tace "yanxu Abu ina zanje da wannan daren me yasa baba bazaiji tausayina ba?" Abu ta dafa kafadarta tana goge mata hawaye tace "kiyi hakuri Hibbah ba lefin baba bane saboda baya hayyacinsa, yanxu kizo muje wajen gwaggo ( mahaifiyar Aysha, umman Hibbah ) kawai." _gwaggo kaka ce a wajen su Abu da Hibbah, Abu 'yace awajen malam Habu yayan Aysha. Tunda aka kawota yaye bata koma gidansu ba_ Dije tace "tabbas nan ne kawai zakije Hibbah," kallonta Hibbah tayi tace "kuna ganin babu matsala?" Karime tace "haba Hibbah kema kinsan KO kowa ya zargeki gwaggo bazata zargeki ba." Hibbah tace "shikenan nan muje." Kai tsaye gidan gwaggo suka nufa, abakin kofar gidan sukayi sallama dasu karime. Su kuma suka shiga cikin gidan, dakin gwaggo suka nufa lokacin ma har tayi barci Abu ta tasheta. Tashi tayi zaune tana kallon Abu da Hibbah tace "lafiya kika tasheni ina barci? Ke kuma Hibbah me yasa kika biyota baki ganin dare yayi?" Abu tace ina fa lafiya gwaggo? Baba ne ya koreta daga gidan," cikin mamaki gwaggo tace "ya koreta to saboda me?" Nan Abu ta fada mata duk yarda akayi. Tattafa hannu gwaggo ta shigayi tana sallallami tace "ai dama nasan za a rina matar da bata bar mahaifiyarki ba balle ke" Baban su umman su Hibbah ne ya lek'o yana cewa "lafiya ne naji kina sallallami?" Gwaggo tace "ina fa lafiya........." Nan ta shiga labarta masa komi kamar yarda Abu ta fad'a mata. Shi kanshi baba yaji ba dad'i amma sai yace "to ai shikenan sai tayi zamanta anan din tunda bata da inda zata." Yana gama fadin haka ya koma dakinsa. Gwaggo ta kalli Hibbah tace "ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan kinji? Kuma karki kuskura ki zargi mahaifinki don bashi da lefi baya hayyacinsa ne, *RAYUWA* ce wata rana sai labari kinji?" daga Mata kai Hibbah tayi tace "insha Allah gwaggo" gwaggo tace "yauwa 'yar albarka allah ya muku albarka" sukace amin. Tashi sukayi suka dauro alwala suka kwanta................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Washe gari Hibbah bata tashi ba sai wajen k'arfe 9 na safe, bayan tayi sallah asuba data koma abinda bata tab'a yiba kenan barcin safe, shima tayi ne saboda jiya da dare bata samu tayi isasshe ba saboda zazzabin daya rufeta kuma alhamdulillah yanxu ya sauka don garau take jinta. Bud'e ido tayi tare dayin salati tayi addu'a ta kalli gwaggo dake zaune kan sallaya tana jan casbaha tace "ina kwana gwaggo?" D'aga mata kai gwaggo tayi saboda bata magana idan tana lazimi. Tashi tayi ta wanko fuskarta da bakinta tare da d'auro alwalar sallah walha ta koma daki tayi sallah bayan ta idar ta jima tana kaiwa Allah kukanta akan matsalolinta kafin ta shafa. Bayan ta idar inna ta ajiye mata kwanon koko da k'osai ga kuma na d'umame a gefe wai taci wanda take so rabon da Hibbah taci irin wannan cimar har ta manta, kokon da k'osai taci taji harma ta k'oshi. Inna lami kam gari na wayewa ta zari mayafi tayi gidan Inna delu aminiyarta, bayan sun gaisa Inna lami cikin happy tace "uhumm albishirinki aminiyata," itama Inna delu cikin zumud'i tace "Kai muguwa nasan wata muguntar kika shirya tunda har kika kasa jurewa kikazo gidana, to goro bani nasha." Inna lami tace "hmm ai kedar bari, yafa saketa," gud'a delo tasa tace "Kai lami gaskiya kin iya mugunta to ita kuma waccen aljanar 'yar fa?" Lami tayi murmushin mugunta tace "itama a jiyan da daddare uban yace tabar mai gidansa," da zumud'i delu tace"ita kuma me kika yi Mata," shewa lami tayi ta shiga fad'a mata duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa "shima da uban naga kamar yana jin tausayintaa na fututtuke nace zan bar masa gidansa ba shiri yace ta tafi." Delu ta kalleta tace "gaskiya lami kin fini iya tuggu amma fa kinyi kuskuren

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});