Chapter 58
Chapter 58
kuma dandali ne kar aje d'in ai kema kina son zuwa bani kad'aice ke son zuwa ba" Safiyya tayi dariya "kuma fa haka ne nima Allah ina son zuwa" Aunty ta kalle su cike da sha'awa idan suna wannan fad'an nasu burgeta suke yi tace "au ke Safiyya da bak'in ciki zaki yiwa Saudat d'in kenan?" "A'a Aunty nasan Aunty Hibbah da Saudat ne ba'a jin Kansu shiyasa na fad'i haka nasan koda tace baza ta je ba zata dawo ta je d'in" Hibbah dake kwance tana game da wayarta tace "nifa babu inda zani" Umma ta dubeta "tashi maza ki raka su suje don kinga suna rok'on ki shine kike cewa wani baza kije ba" Hibbah ta d'an d'aga ciyar mamy ta dubi Umma "wallahi Umma ciki nane yake min ciwo har banson na zauna ma balle na tashi nayi tafiya" Daddy da suke can d'ayan tabarmar dasu Abba da baba yace "a'a ku rabu da ita tunda bata da lafiya ko zuwa dandalin dole ne" baba cikin kwantar da murya yace "a'a baza ayi haka ba ta tashi ta lallab'a ta raka su tunda suna so" Saudat cikin murna tace "yauwa baba" ta yiwa Hibbah gwalo "to ai saiki tashi mu tafi" Saudat ta mik'e tana gyara mayafinta. Ganin haka Faheem ya d'auki wayarsa yanata hello hello ya fita daga gidan baba yace "sai hakuri ina jin gidan ba service" Hibbah kuwa ba don ta so ba ta tashi ta yafa mayafinta ta gyarawa Nawaz kwanciya don yayi bacci Safiyya ma ta mik'e suka fita, su Aunty da Kausar daau momy suka cigaba da hirarsu. Saudat ce agaba sai Safiyya a tsakiya sai Saudat dake binsu a baya tana ta mita. Ji tayi an fizgota ta fad'a jikin mutum tana k'ok'arin bud'e baki tayi ihu ya toshe mata baki da hannunsa tare da mannata a jikinsa ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, ita kuwa Hibbah sai tureshi take tana son k'watar kanta a hankali ya lalubi kunnenta yace "ki nutsu a jikin mijinki kike" ita dai Hibbah bata kula shi ba ta cigaba da kiciniyar k'wace kanta. Kuma matseta yayi a jikinsa ya tura hannunsa k'asan cikinta yana shafawa a hankali cikin rad'a yace "meya sami cikin naki ni dai nasan banyi ajiya a cikin nan ba ko?" Ita dai bata kula shiba tayi lamo a jikinsa don bata da k'arfin ture shi ganin yadda ya k'amk'ameta, ya cigaba da shafa cikin nata "ki fad'a min me yake damun cikin ko saina duba da kaina?" Tayi masa banza ita duk kunyarsa ma take ji ga kuma mamaki wai daddy ne yake yi mata wannan abun, bata yi aune ba taji yana yi mata tafiyar tsutsa a jikinta sai jin hannunsa tayi a kan breast d'inta. Zazzaro ido tayi waje "daddy....." Tama kasa magana sai rik'o hannunsa da tayi tana girgiza masa Kai, murmushi yayi duk da a duhu ne yace "ai dubawa zanyi tunda ke kink'i fad'a min" da sauri tace "wallahi Daddy k'arya nake kawai don kar na raka su ne" dariya ta bashi sosai yace "my hrt desire dama kin iya k'arya?" Shiru tayi tana k'asa da kai ya kuma murmushi ya rik'e bakinta ya d'an matsa "ni ki daina maidani tsoho kina cemin Daddy idan kuma ba haka ba......" Yayi k'wafa ganin yadda ya kuma matseta da sauri tace "to na daina." Saudat ce ta lek'o "Hibbah ina kika tsaya ne ki fito mu tafi" Hibbah ta kuma zaro ido da k'yar tace "takalmina ne ya mak'ale gani nan zuwa" "to ki haska mana ba da waya a hannunki ba" Hibbah tace "gani nan fa" ta kalli Faheem "daddy su Saudat na jira na" ya had'e rai "baki ji ba ko nace ki daina cemin daddy zan d'au mataki fa" "Allah ya baka hakuri na daina" ya cikata "to jeki ko nazo nayi rakiya?" Da Sauri ta girgiza kai, yayi dariya "matsoraciya" da gudu ta fita ganin ya sake ta, shi kuwa dariya ta bashi ya shiga cikin gidan yana murmushi yana kuma mamakin kansa yadda yaso ya kasa saita kansa don kawai ya manna jikinsa dana wannan yarinyar, ya d'anyi tsaki a zuciyarsa yace duk laifin Kausar ne wallahi ba don haka ba da ba zai susuce akan wannan 'yar yarinyar ba. (Ni kuwa nace eh akan yarinyar ka kasa nutsuwa har ka kwanta a asibiti saboda ciwon zuciya😏) Ta fito suka tafi dandali Saudat tana ta yi mata mita suna ta fiya ita dai bata kulata ba don duk abinda Faheem yayi mata yak'i goguwa a kwanyarta da haka suka k'arasa dandalin Ana ta kad'ekad'e 'yammata suna ta rawa wasu kuma sunata zuba tad'i. Suka k'arasa wajen suna ta kallon matan masu rawar, Saudat ta kalli Hibbah cikin tsokanar tata tace "Auntyna ke baza ki shiga kiyi rawar ba, da fa har dake ake yi ko?" Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat da Safiyya suka kwashe da dariya Saudat tace "kuma wad'annan k'olawan ne samarin Ku?" Saudat ta fad'a tana dariya har da rik'e ciki. Hibbah ta buga mata duka tana cewa "wallahi tashi mu tafi dama don kiyi min wulakanci ne yasa kika ce zaki zo ko?" Safiyya ita ma dariyar take tace "haba Aunty Hibbah ai ko da kina k'auyen nan kinfi k'arfin wad'an nan k'olawan" itama ta fad'a tana dariya, Hibbah ta tashi ta fara tafiya "idan kun gama dariyar ku same ni a gida" "ki tsaya mu mana Auntyna" Saudat ta fad'a cikin dariya banza Hibbah tayi dasu ta fara tafiya. Ji tayi an dafata ta baya ance cikin yanayin mamaki "Hibbah dama zaki dawo k'auyen nan?" Da sauri Hibbah ta juyo jin muryar kharime tace "kharime" "na'am Hibbah yaushe kika zo?" Farin ciki ne ya lullub'e Hibbah tace "yau nazo kharime ina dije?" "Dije suna tare da salahu, Hibbah kinga yadda kikayi kyau kika koma 'yar gayu kamar dama a birni aka haife ki" Hibbah tayi Mata hararar wasa "kai kharime kin fiya tsokana" "Allah da gaske nake, kinsan Abu tayi aure kuwa?" Hibbah ta janyo hannunta suka zauna akan wani benci tace "eh gwaggo ta fad'a min ke yaushe ne naki?" "Ai idan zaki kai wani satin a garin nan to dake za'ayi" "da gaske?" Hibbah ta tambaye ta cike da zumud'i kharime tace "Allah kuwa" Su Saudat suka k'araso suka gaisa da kharime, Hibbah an samu aminiya tuni suka zauna suna ta zuba hirar yaushe gamo, dije ce ta k'araso tana ta mita "wallahi kharime halinki saike gara ma ki canza hali gidan wani zaki" kharime ta kalleta tana dariya "Amaryar salahu me nayi kuma?" "Wato sai da kikayi yadda kikai kukayi magana da wad'annan 'yan birnin ko?" Dariya kharime ta kuma yi "Hibbah ce fa" "wace Hibbah karki raina min hankali mana" "Allah da gaske nake nima ta muryarta na ganeta" dije ta zubawa Hibbah ido lokaci d'aya kuma ta gane kamannin Hibbah, da sauri suka rumgume juna suka zauna Ana ta zuba hira. Su Saudat kuwa zuba musu ido sukayi suna ta sauraron hirarsu, sun jima suna ta hira badon sun so ba haka suka hakura suka rabu akan gobe idan su Hibbah basu tafi ba zata zo su je gidan Abu. Haka suka koma gida aka cigaba da hira kamar baza'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63