Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 50

Chapter 50

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wacece wannan mai irin murya da kamannin k'anwarsa Aysha kodai 'yar Aysha ce? Ya tambayi kansa sai kuma ya girgiza kai a'a, a iya saninsu Aysha tun tana k'arama ta b'ata kuma baya tunanin yanzu tana raye, lallai ya zame masa dole yasan ko wacece ita. To amma me ta sani game da Daddy da har zata suma don tagansa mene a tsakaninsu? Dukkansu su biyun basu da amsoshin tambayar su don haka Daddy ya d'ago Kai ya dubi Hibbah dake kwance itama duk tunani ya dameta. "Hibbah ki fad'a min mene dalilin da yasa don kin ganni kika tsora har kika suma?" Hibbah tayi shiru tana nazari kenan baba bai ganeta ba kodai ba babanta bane kama ce? Ta dubi su momy duk jira jira sukeyi tayi magana, cikin yanayin tsoron da bai saketa ba tace "Baba, baba baka gane ni ba Hibbah ce fa, Hibbah 'yarka daka kora" sai kuma hawaye ya fara bin fuskarta. Daddy cikin yanayin nuna damuwa yace "Hibbah kiyi hakuri bani bane Wanda kike fad'a" Hibbah ta rik'e kanta don ya fara mata nauyi wannan wace irin *RAYUWA* ce ka haifi 'yarka amma ka kasa gane ta? Me ta canza da baba zai kasa ganeta? Faheem dake kusa da ita ya dubeta cikin kulawa "Hibbah kiyi mana bayani yadda zamu fahimce ki, kinsamu a cikin hargitsi" Hibbah hawaye nabin fuskarta damuwarta ta k'aru "babu komai Daddy zan cigaba da rayuwata ba tare da babana ba dama tun tasowata nafi sabawa da ummana akan babana saboda baya sona bai damu da rayuwarmu ba........." Sai kuma ta saki wani irin kuka. Daddy ya kasa fahimtarta ya kasa gane maganganunta, balle kuma Abba da idan tayi magana yake jin gabansa yana bugawa. Faheem kam wannan kukan da take yi jinsa yake har cikin ransa, Aunty ta janyo Hibbah jikinta tana rarrashinta. D'akin yayi tsit sai sanyin AC dake ratsa d'akin, Abba ne ya katse shirun da cewa "Hibbah dukkanmu nan bama gane abinda kike fad'a, amma ko zaki fad'a mana sunan mahaifin naki may be mu ganeshi," da kamar ba zatayi magana ba saboda kukan da yaci k'arfinta, dak'ar ta iya rage kukan cikin muryar kuka tace " *MALLAM MUKHTAR MUHAMMAD*" da hanzari Daddy ya nunata "kina nufin kice min Mukhtar yana raye!?" Daddy ya fad'a cike da rud'ewa, kansa ne ya fara juya masa a hankali ya kama gefan gadon ya zauna yana jin k'aunar d'an uwansa tana kuma ratsa zuciyarsa. Abba ma gefen Aunty ya zauna yana kuma tuno rayuwarsu ta baya gefen zuciyarsa kuma cike yake da rud'ani don ya k'osa yaji wacece Hibbah so yake yaji asalinta don kamar da suke yi masa da Aysha k'anwarsa ta b'aci. su mamy da momy ma suna cike da rud'ani ashe Hibbah'yarsu ce basu sani ba. Faheem, Aunty, Kausar dasu Hibbah sun kasa fahimtar komai game dat abinda yake faruwa, Faheem cikin damuwa ya dubi su Daddy "Daddy don Allah kuyi mana bayanin abinda yake faruwa mun kasa gane abinda kuke nufi" Daddy yayi shiru k'aunar d'an uwansa na kuma ratsa zuciyarsa ya dubi su Faheem "Faheem yau zan bayyana muku komai game da rayuwarmu." Kowa ya maida hankalinsa kan Daddy, ya cigaba da cewa "Kamar yadda kuka taso a garin kano muma a cikinsa muka taso iyayenmu mu uku suka haifa sab'anin yadda kuka sani, nine babba sai mai bina Mukhtar sai kuma mamynku Rukayya, mun taso cikin so da k'aunar iyayen mu sun jajirce wajen ganin sun inganta rayuwarmu ta hanyar bamu ilimi na duka b'angarorin. Ni da Abbanku mun taso tare kamar tagwaye komai tare mukeyi, haka ma Mukhtar da abokinsa Ibrahim sam ba'a jin kan d'aya daga cikinmu, muna level 4 a jami'ar bayero university kano inda muke karantar business administration dukanmu, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa mutuwar data gigitamu dukkannin mu, munyi kukan rashinsa sanadiyyar mutuwarsa ya janyowa hajiya hawan jini. Bayan rasuwar mahaifinmu duk wata d'awai niya ta gidan ni da Mukhtar ne muke yinta da yake dama mahaifinmu kafin ya rasu ya d'oramu akan kasuwancinsa da yakeyi a kwari sai muka cigaba da juya dukiyar. Shekarar mahaifinmu d'aya da rasuwa muka kammala degree d'in mu, hajiya kuma ta matsa mana akan muyi aure dama duk muna da wad'anda muke so yayinda Abbanku kuma yake son Rukayya, ba'a d'au wani dogon lokaci ba akayi bikinmu. Auran da mukayi sai Allah ya kuma hab'b'aka arzik'in mu, don haka hajiya tace mu raba gadon da Alhaji ya bar mana idan yaso kowa saiya tada jarinsa munyi na'am da abinda hajiya tace don haka aka raba gadon aka bawa kowa hakkinsa muka cigaba da juyawa. Kafin shekara arzik'in mu ya kuma burink'asa amma duk cikinmu Mukhtar ya fimu iya business don a lokaci k'ank'ani yayi suna a cikin garin kano har ya fara fita k'asashe babu wanda baisan *Alhaji Mukhtar Muhammad shagari* ba kowa ka tambaya zai nuna maka. Shekarar mu d'aya dayin aure Allah ya azurta matanmu nida Abban Ku da samun haihuwa kuma duk maza, sab'anin Mukhtar da matarsa Aysha Allah bai basu haihuwa ba. Ranar suna nasawa Faheem Muhammad sunan mahaifinmu kenan shima Abban ku yasa sunan haifinsa Ishaq shine suke kiransa da Haisam. Haka yaran suka taso cikin kulawa musamman ma Aysha da Mukhtar sunfi kowa basu kulawa. Cikin ikon Allah shekarar su Faheem uku allah ya azurta Aysha da samun ciki, kowa ya tayata murna sai d'auki akeyi da murnar wannan cikin, cikinta yana da wata shida Rukayya ma ta kuma samun nata rabon, a lokacin ne kuma Ibrahim abokin Mukhtar yayi aure. Kasuwanci yana cigaba da bunk'asa yayinda mak'iya suke yiwa Mukhtar bak'in ciki da d'aukakar da Allah ya bashi. Ranar wata laraba da bazan tab'a manta wa ba a rayuwa ta rana mafi muni a garemu ranar dana rasa d'an uwana na kuma rasa mahaifiyata ga kuma Aysha matar Mukhtar itama mukayi rashinta. Mun saba kullum da daddare bayan sallar isha'i muna zama da iyalanmu mu tattauna matsalolinmu, ranar tunda muka zauna Mukhtar yake cewa kansa yana masa ciwo Aysha ta kawo masa magani ta bashi yasha duk da cewa a lokacin tayi nauyi, bayan d'an wani lokaci kawai muka ga Mukhtar yana yi mana wasu abubuwa tamkar wani mahaukaci lokaci d'aya ya canza ya koma yana yi mana hauka tuburan sam ya fice a hankalinsa, hankalinmu ya tashi duk muka hargitse musamman ma Aysha wadda tsabar tashin hankali a lokacin nak'uda ta kamata, hajiya kuwa hawan jininta ya tashi muka rasa ya zamuyi kawai nida Abban ku muka samu dak'yar muka tura Mukhtar d'aki muka kulleshi hankali a tashe mukayi asibiti dasu hajiya. Muna zuwa cikin gaggawa aka karb'e mu sakamakon wahalar da Aysha ta sha wajen nak'uda yasa ta rasa duk wani k'arfinta suka ce saidai ayi mata aiki, a lokacin lafiyarta kawai muke da bukata ba tare da tunani komai ba na saka hannu, Ana shirin yi mata aikin ta haifo 'yarta sai dai tana haihuwa Allah ya karb'i ranta munyi kukan rashinta don Aysha macece mai kirki da sanin darajar d'an Adam, don haka Ana kawo yarinyar nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyarta. Hajiya kuwa dak'yar likitoci suka samu hajiya ta farfad'o har ta d'an ware likitoci suka bamu damar shiga mu dubata, hajiya tayi murna da ganin yarinyar da Aysha ta haifa,

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});