Chapter 35
Chapter 35
muyi aure." Ta gyad'a kai cike da mamaki don ita wasa ta d'auki abin "aure? Wani banbarakwai nake jin abin na fad'a maka abin da kamar wuya taya ma hakan zai faru?" "Insha Allah za'ayi, ki fad'a min *I love you* zanji dad'i," kamar ta kurma ihu take ji ta rasa wanda zata cewa tana so sai Faruq. "Kinsan halina sai na rumgume ki a nan ni babu ruwana gara ki fanshi kanki kawai kiyi abinda nace," tasan halinsa sarai zai aikata "amma ko na fad'a ka sani tursasani kayi kar kayi tunk'awo dashi *I LOVE YOU*" ya tuntsire da dariya, haushi yasa idanunta sukayi narai narai ya rik'o hannunta ta fizge don zuciyarta zafi take, da sauri tabar wajen yana ta shek'a mata dariya babu abinda yake so kamar yaga yasa Hibbah a gaba har tayi kuka, sai yaji wani sonta da k'unarta na shigarsa. Ranar ya nace mata yak'i tafiya ko zama zaiyi saiya dawo kusa da ita sai ya waske yana yiwa Nawaz wasa, shareshi take yi don bata son Faheem ya fahimci suna wani d'asawa ne da Faruq. Ya shigo fuskarsa a had'e kamar bai gansu ba, gani tayi Faruq ya daina rawar kai, "Faruq Ku had'a kayan nan mu tafi gida sun bamu sallama," Faruq ya kalleta "mene kike wani d'ari d'ari nifa bana jin kunya a gaban Ya Faheem sai na miki kiss kinga daya ga haka sai yasan yadda zai nema min aurenki, su bani abuna ko kuma na ja musu maga na b'allo ruwa." Ta marairaice "ka tabbatar min ka tsaneni shiyasa kake bin duk wanda nake da k'ima a wajensa kake zubar min da mutunci, Allah sai ya saka min," maganar ta shige shi ya janyo Nawaz ita kuma ta had'a kayan suka fito. A nota suka iske shi yana danna ways Sam ya rasa mai yake masa dad'i ransa a b'ace yake, Faruq ya bud'e motar yana sa kayan, Nawaz ya shige gaban motar. Ya kalleta "muje ga mota ta mu tafi tare" ta dalla mishi wata harara ta tsuke baki, ya Sosa sumarshi yana dariya ciki ciki, ta rasa wanda zata bi don tana matuk'ar jin nauyin Faheem d'azu ma da k'yar take numfashi a cikin motarshi, amma da ta hau motar Faruq gara ta hau gara ta tafi a k'asa, gani tayi Faheem yayi tafiyarsa. Faruq yaji wani dad'i a ransa shi yasa Faheem yake burgesa akwai jan girma yasan abu ya gani amma sai ya basar kawai don shi baison shiga sabgar yara. Ta k'urawa danjojin motar idanu har suka b'ace a duhun daren, hannunshi taji cikin nata "my dear," a fusace ta k'wace hannunta ta soma tafiya ko waiwaye bata yi har ta d'anyi nisa don zuwa bakin titi daga asibitin da d'an nisa. Faruq ya shiga motarsa yana biye da ita "Hibbah mene haka wai kinsan halina idan kika b'ata min rai," ko kallon shi bata yi ba, kwatsam sai ga wash d'irka d'irkan karnuka sun sharp a guje suna haushi, turus tayi ta ci wani mugun burki zuciyarta tana harbawa ta k'ame babu abinda tafi tsoro kamar kare, sai kace zakuna haka suka tunkarota ta kasa gaba ta kasa baya, gashi sun nufota gadan gadan ai batasan sanda ta bud'e motar ta rufe ba, ta tusa kanta tana ambaton Allah. Faruq ya kwashe da muguwar dariya mai ban haushi yana kad'a kai don wak'ar Machel Jackson yake saurara yana ya fara tuk'insa cikin nishad'i, ya d'ago kanta "my baby kin fiya tsoro, idan munyi aure da kin b'ata min rai police dog zan d'auko su yayyaga ki" tayi banza dashi "Hibbah" ya Kira sunan a hankali, ta kalle shi "gaskiya kin fa tashe ni daga aiki wai sai kimin shiru kin mai dani mahaukaci wato nayi ta sambatun sonki ni kad'ai, ki tausayamin wallahi da gaske nake aurenki zanyi" ta mishi kallon nutsuwa sai yanzu taji zuciyarta ta gamsu da gaske yake amma kuma yafi buk'atar jikinta akan komai, Allah mai yadda yaso gata dai a hannun Faruq duk abinda yaga dama yayi da ita. See Sweet suka iso yayi parking ya fita yaje ya siyo ice cream da fresh milk yana tahowa ta k'ura masa ido handsome bakinta ya furta, ya k'araso cikin motar. Ya mik'a mata ledar, ta kalle shi "gaskiya ba zan karb'a ba na gode in don nice da bakayi asarar kid'inka ba," ya had'a rai ya jefa mata jikinta "sai ki jefar tunda baki so," ya tashi motar bai sake magana ba har suka gida, ta fito ta bar masa kayansa a mota. Ya d'auko ya bita da shi, Faheem yana ta lallab'a Nawaz yayi barci ya dameshi bashi kansa ciwo yake masa. Hibbah tayi sallama yana jinta ya tashi, Faruq ya shigo ya zauna yana kallon news, yana tambayar Faheem kanun labaran Nawaz ya haye jikinsa yana tambayarsa me ya kawo musu a leda, ya mik'a masa wai ya kaiwa Hibbah. Hibbah kuwa kitchen ta nufa tana zuwa ta hango Kausar tana aiki a ciki "aunty sannu da aiki," tayi mata wani kallo dama tana jin haushinta a dalilin tafiyarta yaronta ya samu matsala har ta kaisu ga yin 'yar hatsaniya da Faheem don har yanzu basu shirya ba, "Kama aikinki donni bazan iya ba dama na gaji" tayi ficewar ta. Taji babu dad'i abinda Kausar take yi mata yayi yawa ka d'auki d'an Adam kamar dabba a wulak'ance, ta duba abincin ashe ma indomie ce take dafawa sai kuma dankali da ta soma ferayewa, ragowar mata shikenan abincin da ta iya. A bayanta ta ji shi ta juyo suna kallon juna, surarta ta ja hankalinsa duk da ba yau ya fara ganinta ba, ta juya amma ta kasa ci gaba da aikin don ita bata son kallo da takura. Nawaz ya shigo "aunty yunwa nake ji" ta zobo masa indomie dayake tayi ta bashi, Faruq ya kuma matsowa "Hibbah yaya zan kwatanta soyayyarku da Nawaz ne, gashi shi kad'ai ne a wajen ya Faheem daya bamu shi nasan bazai bamu ba don shi yana son yara, amma wannan Matar tashi ta fini yahudanci wai bata son haihuwa" ita dai feraye dankalin take bata ce masa komai ba "kin San abinda na tsana kenan kiyi min shiru ina magana ko?" Tayi shiru, kawai yatsunsa taji a gefen cikinta yana mata cakulkuli, wata zabura tayi ta zille gefe tasa kuka "Wallahi zanje na fad'awa Daddy'n Nawaz wannan wulakanci da kake min ya ishe ni," "ni d'in mahaukaci ne zaki k'yale ni ina magana ni kad'ai?" Kausar ta shigo tana wani muzurai "ke dalla ki bawa mutane abinci muna jin yunwa" taja tsaki, Faruq yayi mata wani kallo ya had'a rai, sim sim ta fita tana mita don tana shakkar Faruq. Yayi tsaki "stupid kawai 'yar rainin hankali ce matar nan, sai Yaya ya dinga min wa'azi ga rubbish nan a gidansa ya kasa sarrafata, dama ina ciki da ita" "to kai ina ruwanka da shiga tsakanin miji da matar sa haka yake son matarsa don gani yayi zai iya zama da ita" ya harareta "Allah ko uwar iyayi kin fini sanin hakan ko?" Tayi d'an murmushi "kaima ai ba kanwar lasa bace" "Wai ni na rasa girman lefina da ake gani har kuna hangen nauyin zunubi na bazai kankaru
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63