Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

(haka yake kiranshi) ka taya ni murna nima naga Aysha k'anwata" farin ciki ne ya bayyana a fuskar baba da kuma mamaki "a ina? Wace ita? Me yasa baku tawo tare ba?" Tambayoyin baba sun basu dariya Abba yace "mun tawo da ita mana" "tana ina? Ya baku shigo da ita ba?" Daddy ya kuma dariya saboda yadda k'anin nashi yake ta wani zumud'i "gata nan a gabanka, ai ba bak'uwa bace Umman Hibbah ce" "Umman Hibbah?" Baba ya tambaya cike da mamaki "eh ita ce" Abba ya bashi amsa sannan ya shiga bashi labari kamar yadda malam ya basu. Baba ya jinjina kai ya dubi Hibbah " ikon allah kenan, Hibbah kinga *RAYUWA* ko? Kinga sanadin kaiki aikatau da lami tayi kin nemo danginki ko?" Hibbah ta d'ago tana kallon baba da murmushi tace "haka ne baba amma ya akayi kazo k'auyen nan?" Aunty ta kalli Hibbah tana dariya "shine kika rigani tambaya" Saudat tace "ai gara da ta tambaya aunty don na k'osa naji yadda akayi" baba yayi murmushi, Hibbah ta tsaya tana kallon fuskar baba tana mamakin yadda baba yau yake yawaita murmushi, ko dan yaga 'yan uwansa ne oho. Baba ya katse mata tunani "ni kaina bansan yadda akai nazo nan ba nima kawai na tashi daga bacci ne na ganni a gidan su lami sai daga baya mahaifinta yake fad'a min a halin da ya since ni na hauka. Mahaifin lami shahararran malami ne a cikin k'auyen nan shine ya cigaba da bani magunguna har na samu sauk'i ya bani kud'i yace na koma garin mu saboda na bashi labari na. Kasa komowa nayi saboda gaba d'aya ji nake na tsaneku bana son kuma rayuwa daku na fad'a masa ni bansan komawa cikin dangina ya tambaye ni dalili na fad'a masa cewar ni kawai bansan komawa bai takurani ba ya barni a gidansa na cigaba da zama. Ya koya min sana'ar da yake yi nima na shiga taimaka masa, Allah sarki malam shehu shekarar mu d'aya dashi Allah ya karb'i ransa kafin ya rasu saida ya rok'eni da na auri 'yarsa d'aya daya mallaka Fatima wato lami na amince masa duk da tarbiyyar lami sam bata yi min ba don sun shagwaba ta sam bata da kamun kai amma bazan iya bud'e baki nace masa bana son jininsa ba haka na hakura aka d'aura aurena da lami ya bani wannan gidan da muke ciki. An d'aura aurenmu da sati d'aya malam Shehu Allah yayi masa rasuwa munyi kukan rashinsa. Ni na cigaba da Kular masa da dukiyarsa da matarsa baba mairo mata Mai mutunci da karamci, shekaramu d'aya da aure itama baba mairo Allah ya karb'i rayuwarta sanadiyyar ciwon cikin da tayi ta fama dashi. Tunda mukayi aure da lami bata tab'a haihuwa ba shine sanadiyyar auren Aysha da nayi har ta Haifa min Hibbah amma abin mamaki na kasa kula da su hasali ma tsanarsu nayi sam bana son ganinsu, sai gashi kuma Aysha tazo tana cin amanata. Ina kasuwa malam Haruna mijin k'awar lami yazo yana fad'amin cewar Aysha fa tana ta rayya da maza don ganin idanunsa shi shaida ne na zo gida Sam babu bincike na saki Aysha ashe tuggu lami ta had'a ita da kawarta delu, sai daga ba malam Haruna yazo yana neman yafiya ta ya fad'a min cewar sharri suka yiwa Aysha" baba ya d'ago ya kalli Umma da Hibbah "Ku yafe min don Allah" "na yafe maka ni tuntuni" "baba ni baka yi min komai ba" B'an garan Inna kuwa tana fita gidan delu ta nufa delu tayi mamakin ganinta da daddare tace "lami lafiya?" "Ina fa lafiya Hibbah ta dawo tare da wasu manyan mutane 'yan gayu masu kud'i har d'aya daga cikinsu yana ikirarin wai Hibbah matarsa ce," delu ta zuba Mata idanu cike da mamaki "Matar sa? Kice zama bai Kama mu bai kama mu ba" "ai dama na sanki aminiyata shiyasa na garzayo wajenki" delu ta janyo mayafinta tace mu tafi wajen halakakke" suka fito suka nufi wajen boka basa ko tsoran dare suka hau dutsen da yake kai suka cire takalmansu da d'ankwalayen su da mayafai suka doshi inda yake zazzaro ido sukayi waje cike da tsoro suka.......... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Aunty Garkuwa Allah ya baki lpy ya kuma yaye miki wannan ciwon idon da kike fama da shi ameen.* Suka dubi juna a hargitse lami tace "delu huta ce fa take cin jikinsa duba fa kiga" "na gani lami ai kuwa muma muyi maza mubar wajen" delu ta fad'a tana jan hannun lami suka sauko daga kan dutsen duk a tsorace suke. Lami ta kalli delu tace "wai yanzu mene abin yi ne?" "Bamu da wata mafita kawai ki hakura kina gani halakakke yana ci da wuta kinga ba wani aiki fa da zai iya yi mana" lami ta jinjina Kai haka ne amma ke baki San wani ba da zai yi mana aikin?" Delu tayi shiru tana tunani can tace "eh.....to akwai wani boka a can k'auyen gomma zai yi miki aiki kuma zaki ji dad'in aikinsa amma ke baza ki iya da aikinsa ba don na sanki" "mene matsalar tawa kema kinsan komene yau zan iya aikata shi matuk'ar Hibbah zata wulakanta a duniya" lami tayi saurin tare ta da fad'in haka. Delu ta dubeta "dole ne zai kwanta dake kafin yayi miki aiki kin yarda muje?" Ba tare da tunanin komai ba lami tace "Muje kawai indai zan samu biyan buk'ata" Nan suka d'auki hanyar gidan boka zulk'ulle dake k'auyen gomma, suna zuwa suka fad'awa boka buk'atarsu yace sunsan sharad'insa suka ce eh yace to ita lami ta tashi su shiga ciki ba ko tsoro a zuciyarta suka shiga ita dashi yayin da delu tana k'ofar wajen tana zaman jiransu. Can gidansu Hibbah kuwa bayan sunyi sallar isha'i zama sukayi suna ta hira cike da barkwanci da nishad'i kowa cikin farin ciki yake jinsa Hibbah har ta mance da wata Inna. Saudat ta dubi Hibbah "wai ni Aunty Hibbah ba'a zuwa dandali ne a k'auyen nan?" Rahmatu dake gefe da k'aton cikinta tace "zuwa kai kina son kije ne?" Cikin zumud'i Saudat tace "eh don Allah Aunty Hibbah kuzo muje naga yadda dandalin yake" Hibbah cikin tsokana ta kwantar da kanta akan cinyar mamy tace "tab kije ke kad'ai ni dai bacci nake ji". Saudat tayi kalan tausayi "Kai Aunty Hibbah don Allah ki tashi muje" "a'a karki takurata ki k'yaleta tayi baccinta" momy ta fad'a tana shafa kan Hibbah. Saudat ta dubi Hibbah tana k'arya kai kamar zata yi kuka, Hibbah tayi mata gwalo ta kuma gyara kwanciya a jikin mamy. Safiyya da Kausar me zasu yi inba dariya ba Safiyya tace "wallahi Aunty Hibbah karki je kiyi baccinki ita idan tana son abu dole sai anyi mata" Saudat ta kai mata duka ina "ruwanki yarinya sai rainin tsiya don kinga Ana miki wasa ko" Safiyya ta DA dariya "to tsakanin mu shekara nawa ne d'aya ne fa kuma shima akasi aka samu da baza ki girmemin ba, kuma dandali ne baza'a ba" "eh naji na dai baki shekarar ai ko 1 minute na baki na dai girmeki

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});