Chapter 20
Chapter 20
ALIYU GARKUWA* *Wannan page d'in naku ne DA BAZARMU WRITERS allah ya k'ara had'a kanmu cikin k'aunar juna* Mamaki fal a fuskar Aunty ta b'alle murfin motar suka fito Hibbah ta kalleta tace "Aunty kinsan gidan ne?" Aunty tana kallon gidan tace "gidan Alhaji Sani ne, shine babban yaron daddy," Hibbah ta kalleta Auntyn ta kawai bata ce komai ba, aunty ta cigaba "idan har Alhaji Sani shine mijin ummanki, to ta more don Alhaji sani mutum ne mai kirki shekarun baya matarsa ta rasu da d'ansa guda daya mallaka sanadiyyar accident da sukayi a hanyarsu ta dawowa kano daga Abuja, shi kuma a lokacin sunyi tafiya da Abba," Hibbah ta karyar da kai yanayin jin tausayi tace "allah yayi masu rahma." Suka nufi gidan, gida ne madaidaici, mai gadin ya gane sa'idu don haka ya barsu suka shiga dayake ma irin almajiran nan ne yara, direct parlor'n gidan sa'idu yayi dasu suka shiga da sallama Umma tana zaune tana kallon sunnah TV suka shigo. Umma ta kalli k'ofa da sauri ta mik'e tsaye tare da zaro ido waje tana nuna Hibbah tace "Hibbah? Kece ko mafarki nake," Hibbah tana murmushin farincikin hawaye nabin fuskarta ta k'araso kusa da Umma ta rumgume ta, sai kuma ta saki kuka Umma ma hawaye nabin fuskarta, bata tab'a tunanin zata had'u da Hibbah a nan kusa ba. Ta d'agota daga jikinta tana share mata hawaye tace "kiyi shiru Hibbah ki daina kuka kinji," ta d'ago ta kalli Umma sannan ta maida kallonta ga Aunty tace "Umma ga Auntyna ita ce ta gyara min *RAYUWA*, inna lami da inna delu sunso b'ata ni sai allah ya taimake ni kuma aunty da momy suka taimakeni," Umma tana murmushi ta k'arasa kusa da Hibbah tana cewa "Auntyn Hibbah kiyi hakuri ban tare ki ba koh? Wallahi murnar ganin Hibbah ne yasa," ta k'araso ta rik'o hannun Aunty suka shigo cikin parlor'n aunty tace "lahh babu komi Umma ai tsakanin d'a da haifi sai Allah," ta zauna a kusa da Hibbah tace "Hibbah na yau sai kwana tare da Umma ko," Hibbah ta rufe fuska tana gyad'a kai. Shi kuwa sa'idu dama suna shiga ya nemi wajen zama. Umma kuwa kitchen ta shiga ta d'ebo musu dangin su snacks da drinks ta cika musu gaba dashi, suka d'an ci suna ta hirar yaushe gamu, Hibbah ta Saki jiki sunata hira da umma ita kuwa aunty mamakin Hibbah take yadda ta Saki jiki tana ta zuba surutu tana bawa Umma labarin abinda ya faru tun bayan tafiyarta har taimakon dasu aunty sukayi mata. Aunty ta kasa jurewa tace "Hibbah wai dama haka kike da surutu?" Hibbah ta tad'an rufe fuska tace "Kai Aunty," aunty tace"eh mana gashinan sai hirarki kike da ummanki," Hibbah tayi murmush. Umma ta kalli aunty tace "mun gode Auntyn Hibbah allah ya saka da alkhari, gaskiya naji dad'in abinda kuka yiwa Hibbah bamu da bakin yi muku godiya Allah ya bar zumunci." Aunty tace "ameen Umma dama na kawota ne zatayi hutunta anan idan sun koma zan turo driver ya d'auketa," Umma tace "to shikenan nan auntyn Hibbah Allah ya kaimu," aunty ta mik'e tana d'aukar jakarta tace "Umma ni Zan tafi sai yazo d'aukar Nata" ta kalli Hibbah tace "Hibbah ni Zan huce sai Adamu yazo d'aukarki idan kuma na samu time zan zo" Hibbah ta mik'e tace "to aunty na gode allah ya saka," aunty ta d'an harareta. Umma tace "mun gode fa Aysha kiyiwa momyn naku godiya kafin muzo, ki gaida gida allah ya tsare" umma ta rakota har bakin k'ofar parlor tana ta yi mata godiya Aunty har ta Fara jin nauyi ma. Har wajen mota Hibbah ta rako Aunty, sannan sukayi sallama cike da kewar juna. Hibbah ta koma suka cigaba da hira shima sa'idu yace zai tafi, umma ta Bashi kud'in mota ya tafi. Da umma zatayi girki ma tare sukayi da Hibbah, umma tayi mamaki Gannin yarda Hibbah ta iya girki haka. Lokacin da mijin umma ya dawo Alhaji Sani ya taya umma murnar ganin Hibbah kuma yace zai d'auketa ya rik'eta tamkar 'yar da ya Haifa. Haka Hibbah ta cigaba da zama wajen ummanta, kullum cikin bawa ummanta labarin gidansu aunty take, har umma taji bazata iya karb'ar Hibbah a hannunsu ba, dan sunyi shawara da Alhaji akan zasu karb'eta yace zai rik'eta, a haka har hutun Hibbah ya k'are aunty tazo ta d'auki Hibbah tare sukaje da umma tayiwa momy godiya. ***** *RAYUWA*r Hibbah ta canza daga k'unci ta koma farinciki, Hibbah ta kuma gogewa ta waye, ta kuma zama budurwa idan kaga Hibbah sai ka rantse tafi shekaru sha bakwai, ta kuma cika ta ko ina ta zama cikakkiyar budurwa. Yanxu suna shirin shiga SS 2, Hibbah ta kuma maida hankali akan karatunta don tana cikin d'aliban da malamai keji dasu a makarantar. lokacinne kuma aunty ta kammala makarantar ta *BAYERO UNIVERSITY KANO*, zata tafi service d'inta, da farko Enugu state aka turata, sai da Abba ya shiga ya fita suka dawo da ita arewa inda aka tura Aunty Abuja, taji dad'in turata Abuja da akayi don a gidan Abba zata zauna. Matsalarta d'aya Hibbah bata so tabar Hibbah a gidan saboda tasan any time Faruq zai iya dawowa kuma tasan k'udirinsa akan Hibbah, idan kuma tace zata tafi da ita Abuja momy bazata ji dad'i ba ga kuma karatunta zata fara lalata mata shi. Haka Aunty Aysha tayi ta tunanin mafita daga baya ta yanke shawarar kaita gidan ummanta, ta fad'awa momy shawarar data yanke kuma momy tayi na'am da hakan, Ana gobe zatakai Hibbah, Hibbah ta tattara kayanta suka tafi gidan umman nata, aunty ta yiwa umma bayanin komai sannan ta tafi suka rabu cike da kewar juna. Kafin aunty ta tafi saida ta bawa Hibbah waya wai su dinga gaisawa. Haka Hibbah ta cigaba da zama a wajen ummanta cikim kula irin ta uwa tare da taimakon mijin nata Alhaji Sani, umma ta samo mata mai adaidaita da yake kaita makaranta yana dawo da ita, da haka har aunty ta dawo daga service d'inta lokacin da ta dawo ana hutun makarantu shiyasa bata je d'auko Hibbah ba kuma bata fad'a mata ta dawo ba. Sai Ana saura one week su koma school da yamma aunty taje ta d'aukota, tun a bakin gate Hibbah ta fara ganin taron Jama'a amma mafi yawansu mata ne, ta kalli Auntyn ta tace "Aunty me akeyi a gidan naga taron mutane," aunty tayi murmushi tare da cewa babu komai Hibbah," ita dai Hibbah bata yarda ba duba da k'unshin dake hannun Auntyn, driver ya shiga cikin gidan tare da yin parking, suka fito duk harabar gidan 'yan mata ne 'yan gayu masu ji da Kansu gefe guda kuma ga manyan mata a zazzaune akan fararan kujeru. Suna doso cikin gidan 'yammatan suka shiga ihun Amarya Amarya, kan Hibbah ya kuma d'aurewa ta kalli Auntyn ta sai taga ta kawar da kai tana murmushi taja hannunta suka shiga cikin gidan, a parlor ta kuma ganin tawagar wasu matan ta kuma gani nan ma suna shiga suka shiga yi mata ihun Amarya, daga can gefe ta hango Saudat, Safiyya da wata da bata Santa ba sai wani yaro da bazai huce shekaru uku ba d'an kyakykyawa yana ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63