Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana rawa tace "daddy kayi hakuri bazan k'ara ba, Allah ya huci zuciyarki Umma," ta fad'a tana share hawaye. Tausayinta yaji sosai ko da yake yaji dad'i umman ta burgeshi don shi mutum ne Mai son a bashi girma da girmama na gaba dashi don haka bai son reni ko kad'an shi yasa Hibbah ta shiga ransa don tana da biyayya da ladabi Sam bata kiransa da Yaya kamar yarda k'annansa suke kiransa saidai tace masa Daddy kamar yadda taji Nawaz yana fad'a. Ta tashi ta d'auko Jakarta, ya ajiyewa Umma kud'i ba yadda batayi ba ya d'auke abinsa amma yak'i yaji dad'in karramawar da akayi masa da sanin ya kamata irin na iyayen k'warai, suka yiwa Umma sallama suka fito. Ya bud'e mata gaban motar don yasan halinta sai ta zauna a baya, ta kalleshi gani tayi ya had'a rai babu alamar wasa a tattare dashi shiyasa ba musu ta shiga. Ya dad'e bai ji annashuwa ba kamar a yanayin nan ya kunna wakar Celine Dion yana sauraron baitukan wak'ar, yana tuk'i cikin nutsuwa, Hibbah ko numfashi bata yi k'wak'wk'wara ji take yi tamkar ta nutse, kunya ce nauyi ne rashin sabo ne, duk sunyi Mata dabaibayi don basu tab'a had'uwa haka gata gashi ba. Ya dubeta a nutse domin duk damiwarsa babu ita ashe Hibbah ce ta hana zuciyarshi nutsuwa, "Hibbah ta Nawaz ya kikayi shiru ne na takuraki ko? Banji dad'i bane akan abinda ya faru ashe fushi ne dake haka, ki sani nayi miki fad'ane don kawai na damu dake ina kishinki tamkar k'annena su Safiyya ya d'auke ki badon haka ba babu ruwana da ra'ayin wani, ina data dai kin huce ko?" Bata ce komai ba, ya dubeta idanunta sunsha kuka kuwa, zata kuma iya ci gaba da yinsa idan har ya takurata sai yaji maganarta don a takure take ya Sani, shi kuwa so yake ta saki jiki dashi ta daina jin tsoranshi haka don haka ya rabu da ita, da haka har suka k'arasa asibitin. Yana gaba tana binsa a baya, sama suka hau basuyi wata tafiya ba suka isa d'akin, suka shiga ta gaishe dasu momy lokacin Nawaz yana barci momy ta mik'e zata tafi wai dama shi take jira ya dawo yamma tayi sukayi sallama tayi masa fatan samun sauk'i suka tafi. Jimawa kad'an Nawaz ya tashi yana ganinta ya mak'aleta yana k'yalk'yala dariya kamar zata sake gudu ta barshi, ta shafa kansa tana dubansa yayi 'yar rama ta share k'wallar data taru a idanunta. Nawaz ya rik'e hannayenta "aunty Hibbah shine kika gudu wajen Ummanki kika barni kinga inda doctor yayi min allura," ta tab'a wajen "sannu Nawaz Allah ya baka lafiya," "Aunty Hibbah nima zan biki wajen Umma." Ta gyad'a Kai "to naji amma sai ka ji sauk'i zamuje," ta ja hannunsa suka fice barandar suna kallon titi dayaga abinda ya bashi sha'awa sai ya dinga nuna mata suna dariya, yana ta bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta. Yana tsaye ya hard'e hannayensa a k'irjinsa yana kallonsu sun burgeshi da Bashi tausayi "Hibbah" ya ambata a zuciyarsa sunan mai dad'i, ga mamakinsa ashe maganar ta fito fili har tabi iska ta isa kunnenta kawai gani yayi tad'an juyo ta kalleshi, suka had'a idanu cikin wani yanayi a hankali ta d'auke kanta, wani sanyi take gani cikin idanunsa sai taji abin yana mata yawo a k'wak'walwarta. "Hey! My boy," duk suka dubeshu, yayi zanzaro da hula Hana sallah a kansa, da siririyar sark'a tana k'yalli a wuyansa har taso ta shak'e sa, "Yaya ya jikin boy d'in?" "Alhamdulillah yaji sauk'i sosai," hankalinsa yana kan Hibbah bai ko damu da ganin Faheem ba, ya d'auki Nawaz ya rumgume shi tare da yi masa kiss a kumatunsa, shi kuwa ya mak'ale hannayensa a wuyansa tare da zagaye k'afafunsa a jikinsa, Faruq kenan yana k'aunar Nawaz shiyasa shima Nawaz yake k'aunar uncle d'in nasa. Hibbah kuwa kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanata don har yanzu tsoransa take ji............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.A.W *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Ya kalli inda Faheem yake a tsaye bashi ba dalilinsa, ya matso kusa da ita abinda bata so kenan, shi a wajensa ba wani abu bane don ji yake kamar ya rumgume ta, wutar k'aunarta yana faman huruwa a zuciyarsa duk sanda ya d'ora idanunsa a kan idanunta baya iya sarrafa kansa, ya matso sosai kusa da ita, bata da niyyar kulasa, "Hibbah kinsan kuwa irin sonda nake miki? Kada ki maida hannun agogo baya bana so ki dinga tuna baya ban tab'a tsintar kaina a irin wannan love d'in ba Hibbah." Ya dafa kafad'arta, a taorace ta kalleshi suka k'urawa juna kallo na d'an wani lokaci abinda ta gani a idanunsa tad'an tsorata don tabbas binda ke zuciyarsa ya fad'a, ta ture hannunsa. Yayi murmushi "wannan gangar jikin mallakina ce sai nayi yadda nake so da ita in munyi aure, don haka ki dena guduna , ni d'in nan zan baki mamakin yadda zaki yi dadi indan na zama mijinki," murmushi tayi don ita a ganinta wauta kawai yake tace "abinda kamar wuya, naji zancen kamar almara ta Yaya zaka aure ni? Ka tuna fa kaso k'unsa min b'ak'in cikin da har na mutu bazan manta shi ba, kuma badon komai ba kawai don zalinci da son Kai, karma ka Fara yaudarar kanka don yarda ba yadda za'ayi dakai wai kai masoyina ne, don Allah na rok'eka saboda girmanasa ka k'yale ni ka k'yale min rayuwa haka." Ya kad'a kanshi "duk abinda kika fad'a gaskiya ne ni kaina ina cikin mamaki da tuhumar kaina Yaya akayi na samu kaina cikin sark'ak'iya har na fad'a tarkon sonki, banji haushi ba ai na fad'a miki kyauta kika sadaukar min da kanki wallahi zuciyata bazata iya daure wani abu dake ba matuk'ar ba aure mukayi ba," "ni kana bani mamaki to wai taya zamuyi aure? Wannan shirmen tunani ne abinda bazai yiwu ba." Yaji zafin maganarta ya take k'afafunta da takalmin k'afarsa, ta runtse ido saboda zafi, Faruq mugune yasan takan mugunta. Ya tallafo tallafo hab'arta yana wannan murmushin nasa na k'eta "dube ni sai na aure idan yaso in na aure ki ki hak'a rami ki binne ni da raina ko kuma kii gunduwa gunduwa da nama na saboda tsabar k'iyayyar da kike min," ya k'ura mata idanu tak'i bud'e idanunta, ji yayu tamkar ya lashi kumatunta, ya hurawa idanun iskar bakinsa duk da a rufe suke. Ta bud'e idon tana dubansa shed'anin mutum kenan gani take kamar baya hankalinshi, Anya ma Faruq baya shan k'waya don abubuwan da yake yi kamar bashi da tunani a k'wak'walsa, duk inda ake neman namiji mai kyau Faruq ya kai sai bashi da hali. Ya lakuce mata hanci, ya matso da kansa kusa da ita sosai ya sassauta murya "ke d'innan yadda kika shiga raina, ni sonki nake Hibbah kamar nayi hauka don Allah me kika yi min ne?" Ta juyar da kanta gefe, ya sa dariya "kin mai dani dodo ko Hibbah?" Yayi k'wafa "wata rana sai kin rumgume ne kinmin kiss, ni kuma shagwaba zan tayi miki," ya d'an ja da baya "ki samu cikin addu'a Allah yasa

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});