Chapter 26
Chapter 26
dukanta," "na daketa d'in, ta maka waye ni a wajenta ta fad'a maka matsayinta," ya kalli Hibbah dake rik'e dakuncinta yace "ke ki fad'a masa matsayinki a gidan mu," Hibbah tayi shiru wasu zafafan hawaye nabin fuskarta "tunda ke baxaki fad'a ba ni bara na fad'a, Hibbah ba kowa bace a gidan mu face 'yar aiki kuma baiwa!!!" Kalmar tayiwa Hibbah zafi da gudu tayi cikin gida tana kuka. Jabeer ya cilla masa wani mugun kallo "ba baiwa ma ko wace Hibbah ina sonta ina kuma k'aunarta a hakan Zan aureta," yana gama fad'in haka ya shige motarshi ranshi a b'ace ya figi motar. Faruq kuwa ya kasa nutsuwa yana tunanin koya bita cikin gidan sai kuma ga koma motarsa ya had'a kansa da sitiyarin motar. Yana mamkin meya kawo ta gidan ya Faheem. Hibbah kuwa tana shiga gida d'akinta ta nufa ta zube a kan gado ta shiga rera kuka, tana mai jin zafin abinda Faruq yayi mata ace a gaban saurayinka yayi maka wannan rashin mutuncin wannan wace irin *RAYUWA*ce? Ta kuma rushewa da kuka tana kuma tunano *RAYUWARTA* ta baya. Nawaz ne ya shigo rik'e da chocolate a hannunsa yana sha ya mik'o mata "Aunty kinga uncle ya bani chocolate," da sauri ta goge hawayen ta tana murmushi tace "to jeka sha Nawaz nima bara na shiga kitchen," ta mik'e ta nufi kitchen ta had'a musu dinner ta gyara kitchen d'in, tana gamawa taji ana kiraye kirayen sallah tayo alwala tazo ta gabatar da sallar, ta d'ebo abinci ta zauna suna ci ita da Nawaz sai shirme yake mata ita kuwa duk abin da Faruq yayi mata ne yake damunta har ta kwanta tana tunanin abin. Washe gari Monday ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan da taci jiya da dadaddare, ta tashi tayiwa Nawaz wanka ta shirya shi school bus na zuwa ya tafi, ita kuwa bata da niyyar zuwa saboda ciwon kan dake damunta don tana gama shiryashi ta koma ta kwanta sai wajen sha d'aya ta tashi tayi duk ayyukanta tana cikin yin mopping taji motsin mutum a bayanta tana waigawa taga Ashe Faheem ne tace "barka da safiya daddy" bai ma jita ba dun ya sha'afa wajen kallonta tunda suke zaune da ita sai yaune ya tab'a k'are mata kallo lokaci d'aya yaji wani abu a zuciyarshi, hazak'ar Hibbah da ayyukanta suna burgeshi sam bata nuna gajiyawarta akan duk abinda Kausar zata sata ga d'awainiyar da take yi masa da yaro. Ta kuma cewa "daddy barka da safiya," ya d'anyi firgit ya kalleta "lafiya" ya huce d'akinsa ya shiga ya d'auko takardun daya manta ya huceta, ita kuwa ko a jikinta ta k'arasa aikinta tayi wanka ta shirya tsam kamar mai fita wajen party ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci yana yi ta juye ta jere a dinning ta koma d'aki ta d'an kwanta a hankali bacci yayi awon gaba da ita. Cikin barci kamar a mafarki taji ana shafata taji kamar an danneta a hankali ta bud'e idanunta wa zata gani Faruq ne a kanta wani wawan ihu ta saki tare da tattaro k'arfinta ta tunkud'eshi ya fad'i k'asa da gudu ta ta fito parlor kicib'is sukayi da Faheem daya dawo hannunsa rik'e dana Nawaz da gudu ya rumgume ta, ita ma ta rik'eshi sai zare ido take yi. Faruq ya fito yana binta da mugun kallo, Nawaz ya k'arasa kusa dashi "uncle yaushe kazo?" "D'azu nazo Nawaz," ya kallo d'aya yayiwa Faheem ya fice abinsa. Faheem Wanda ke tsaye yana kallonsu kamshi ya d'aure me ya kawo Faruq gidanshi yanxu bayan yasan baya gidan, mene a tsakaninsa da Hibbah kodai itama tana biye masane? Da Sauri ya girgiza kai a'a Hibbah tana da halaye masu kyau, ya kalli Hibbah cikin b'acin rai yace "me kike aikata min a gida?" Da sauri ta girgiza Kai "a'a daddy wallahi bansan ya shigo ba ina kwance naji shi.......," nauyin k'arasawa tayi sai ta saki kuka. Tsayawa yayi kallon ta zuciyarshi ba dad'i sam baya son wannan kukan, ya d'aga mata hannu "tashi ki tafi bana son hayaniya," mik'ewa tayi ta nufi d'akinta tana kuka akan gado ta zube tana ta kuka yanzu shima zarginsa zai d'ora a kanta abinda ta tsana kenan Faheem yaga laifinta shiyasa take jure duk wani wulakanci da Kausar zata yi mata, tashi tayi ta d'auro alwala tayi sallar la'asar a wajen ta zauna tana addu'ar allah yasa Faheem kar ya zargi wani abu tsakaninta da Faruq, kuka ta cigaba dayi Nawaz ya shigo "aunty yunwa nake ji," ta mik'e ta nufi dinning ta zubo masa a plate ta kawo masa gabansa ta tura masa ta koma gefe tayi jugum tana tunani yace "aunty ke baza kici ba?" Ta k'ak'alo murmushi "nak'oshi Nawaz," "aunty dama kinci kafin na dawo ko?" "A'a Nawaz na k'oshi ne," bai kuma yi mata magana ba don shima wani lokacin kisan halinsu d'aya da daddy'nsa haka yaci abincinsa yana gamawa ya fice parlor. Faheem ya gani parlor ya k'arasa kusa dashi yace "daddy aunty Hibbah tak'icin abinci sai kuka take," Faheem ya kalleshi "kuka kuma Nawaz," "eh daddy tun d'azu take yi," ya mik'e ya nufi d'akinta yana zuwa ya tura k'ofar d'akin ganinta yayi a zaune akan sallaya ta kifa kanta. "Hibbah saboda me kika k'i cin abinci saboda abinda ya faru?" Da sauri ta girgiza kai, "to menene kisani ni bana zarginki akan komai, amma ki sani babu Wanda zai ganku a d'aki Ku biyu gida kuma ba kowa bai zargi wani abu ba, ki fita harkar Faruq fatan kin fahimce ni," ta gyad'a kai. "Shikenan ni bana son b'atawa mutum banson na ganki kina damuwa don haka ki samo abinci ki ci kinji ko?", ta kuma gyad'a kai to. Ya rufe k'ofar, sai ta samu kanta tana bin umarninsa, ta d'ebo abincin tana ci sai taji ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, Nawaz yasa ta a gaba Allah sarki shima ya damu yace "Aunty Hibbah daddy bai tab'a dukana ba kema bazai dake ki ba," tayi dariya yaro yaro ne, ahankali ta wantstsake har tayi musu girkin da dare. Washe gari da wuri ta tashi tayi komai don zata je skul. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Facebook groups ina ganin sak'on nin ku da k'arfin gwaiwr da kuke k'ara min ako da yaushe kuma ina godiya Allah ya saka da alkhari ina k'aunarku har cikin raina.* Yau da yamma ta gama komai da wuri tana zaune a d'aki taji wayar ta na ruri ta d'auko dan ganin wake kiranta bak'urar number ta gani da kamar karta d'auka sai kuma ta d'auka a tsorace "hello!" Ta furta a hankali. Daga d'ayan b'angaran taji yace "Hibbah bak'on ki ne gani nan k'ofar gida ina jiranki," ta dafe k'irgi "wai wa kenan ban gane mai maganar ba," yayi murmushi mai sauti "ai baza ki gane ba tunda ban tab'a kiranki ba, Jabeer ne wannan mutumin mai nacin nan, kiyi min hakuri Hibbah kar kice baza ki fito ba don Allah," Hibbah ta d'anyi shiru sai can tace "to ganin fitowa" ta kashe wayar. Ta sanya wata abaya bak'a mai mugun khair gami
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63