Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Aunty shikenan ma kawai ba sainayi tambayar ba," harararta Aunty tayi tace "ai kuwa baki isaba saikin fad'amin, fad'i ina sauraronki," kallon aunty tayi taga ta b'ata rai sai taji bataji dad'i ba tayi k'asa da kanta tace "Aunty wai momy tana da abokiyar zama ne?" Aunty taji tambayar a wani iri ta kalli Hibbah sosai tace "me kika gani Hibbah?" Kuma sunkuyar da Kai Hibbah tayi tace "kiyi hakuri aunty idan maganata ta b'ata miki rai, naga gidan ku babba ne kuma b'angare uku ne a gidan." Dariya aunty ta d'anyi tace "baki b'ata min ba Hibbah, kuma bara na fahimtar dake, wannan b'angarorin da kika gani kowanne dame shi, kinga da bangaren mu dana Abba da kuma na hajiya kaka. Haka daddy yayi tsarin ginin, daya gama kuma hajiya kaka tace ita baza ta zauna ba shine ya bawa Ya Faheem part d'inta, shi kuma b'angaren Abba sai yazo kano yake zama a ciki da iyalansa a Abuja yake aiki," Hibbah ta girgiza Kai alamar gamsuwa, a ranta tace ko waye Abba d'in? Aunty ta kalleta tana dariya tace "bara ma fad'a miki waye Abba don nasan zaki iya tambaya, Abba abokin daddy ne sosai tare suka taso tun suna yara, iyayensu ma aminan junane hakan yasa wasu suke tunanin ko 'yan uwane, amincin dake tsakanin su ne yasa suka zama tamkar tagwaye, d'aya baya tab'ayin abu saida d'an uwansa, sannan matar Abba ma k'anwar daddyn mu, Kausar ma matar Ya Faheem ma 'yar Abba ce, Abba yana da yara biyar Ya Haisam shine babba sa'an ya Faheem ne, sai Kausar wadda sa'a tace, sai Usman, Mubarak sai autar su Janan, yanxu kin fahimta?" Hibba ta d'aga Kai. Da haka suka k'ara gida suna ta hirarsu kamar babu abinda ya Faru. Da daddare bayan su momy sun dawo lokacin ma har sun gabatar da dinner d'insu, momy ta Kira Aunty bedroom d'inta take tambayarta mene ya faru a gidan, aunty bata boye mata komai ba ta fad'a mata tun sanda Hibbah tazo gidan har kawo yanzu abinda ke faruwa tsakaninta da Faruq. Momy ta girgiza k'warai dajin k'udirin Faruq akan Hibbah, wayarta ta zaro ta shiga dialing number Faruq saida ta kusan katsewa ya d'auka yana karawa kunnansa yaji momy tace "kazo sama ina son ganika," ta kashe wayar. Yasan aunty ta fad'awa momy komai shiyasa ko d'ar baijiba. Saman ya hayo ya nufi bedroom d'in momy ya shiga da sallama ya samu waje ya zauna, momy cikin fad'a ta fara magana"yanxu Faruq abinda kayi ka kyauta kenan dama baka canza halinkaba?" Nan momy ta shiga yi masa fad'a sosai ta inda take shiga ba tanan take fita ba, sai da ta wanke shi tas sannan ta Fara yi masa nasiha mai ratsa jiki saida ta tabbar nasihar ta ratsasu sannan ta sallame shi, babu Wanda yayi tunanin Faruq zai kuma magana saboda yadda ya nutsu. Yana tashi yace "ai dama nasan gidan nan babu mai sona daddy ne kawai da Ya Faheem ke sona suma yanxu gashi basa nan, k'iris ake jira nayi laifi to gobema zan koma hutu kuma yasin na tafi sai kun ganni don bazan kuma dawowa ba saina gama," ya fita yana 'yar mita momy tace "allah ya shiry............ *# JUMMA'AT MUBARAK TO YOU ALL😍* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page2⃣4⃣ *NA* *Mamyn Najmah* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Gagara tarkon mahassada AYSHA ALI GARKUWA ki shige gaba muna binki abaya sawun giwa ya take na rak'umi farin gani farar aniya dashe daga rabba idan zaki yai kuka baza a tsaya ba, Allah ya barmu tare cikin so da k'aunar juna🀝😍* Washe gari da sassafe Faruq ya had'a kayansa ya huce Abuja gidan Abba wai acan zai k'arasa hutunsa, sai bayan ya sauka ya huta ma sannan wajen k'arfe d'aya na Rana ya Kira momy yake fad'a mata yana Abuja, daya fad'awa momy tad'anyi mamakin wannan tafiyar tashi babu sallama amma daga baya sai ta rakashi da addu'a da fatan samun nasara. Washe gari Hadiza ta kawowa momy sabbin 'yan aiki mata biyu, saidai su ba kwana zasu dinga yi ba suna gama aikinsu da dare yayi zasu tafi, momy taji dad'in zuwan 'yan aikin nan ba kamar ma aunty don ita bata so taga Hibbah na aikatau shiyasa tayi murna sosai da zuwan 'yan aikin. Kwanci tashi babu wuya a wajen ubangiji yau gashi har Hibbah tayi wata bakwai a gidan su Auntyn ta, wanda tayi *RAYUWA* a cikinsa mai tsafta da ganin gata tamkar itama 'yar gida ce, babu wanda zai kalli Hibbah yanzu yace itace Hibbah 'yar k'auye, don ta waye sosai jikinta yayi kyau fatarta ta kuma laushi sai sheki take, gashinta ya kuma samun gyara yayi kyau. Ita dai babu abinda zata cewa Auntyn ta da momy sai godiya da fatan alkhari dan duk sanadinsu ta samu wannan gatan, bata da wata matsala yanzu ta *RAYUWA* tasamu gatan da bata samu a wajen iyayenta ba ga ilimi na addini Dana zamani, bata tab'a tunanin zata samu wannan ilimin ba sai gashi ta sanadiyyar aikatau da aka kawota birni yanzu she can speak english for more than 5mnts. Yau ya kama ranar Monday kuma ayau ne d'alibai suka koma makaranta ciki kuwa har dasu Saudat bayan hutu da sukayi na k'arshen zangon karatu, yanzu sun shiga new session a ranar ne za'a kai Hibbah makaranta. Da wuri Hibbah ta shirya saboda tasan da yau za'a kaita makarantar boko shiyasa taketa zumud'i har Saudat na tsokanarta wai indai school d'insu ne da k'afarta zata gudu dan idan suka taxi tun safe baza su dawo ba sai shidana yamma", ita dai Hibbah saidai tayi murmushi a ranta tace kaida ka samu gata da dama har zakayi karatu ina kake da k'afar guduwa saidai kayi fatan allah ya shige maka gaba. Bayan su Saudat sun tafi aunty ta shirya da kanta zata rakata don ansai mata file anyi mata komi, dayake makarantar islamiyyarsu ce kuma basu da nisa a bakin layinsu take da k'afa ma suke tafiya. Bayan sunje makarantar Aunty suka gaisa da malaman direct office d'in principal suka huce bayan ta gaishe shi ta fad'a masa Hibbah itace sabuwar d'alibar dama da aka kawo, sannan ta buk'aci sannin class d'in daya bata, yace "ai bata da takardun primary bamuga sakamakonta ba, JS 1 kawai zamu kaita," nan aunty ta shiga Neman alfarma a kaita SS 1 ajinsu Safiyya, principal yak'i yarda, dake abune na kud'in tana cikashi da su dak'ar principal ya yarda za a kakta JS 3, nan akayi mata komi suka bata uniforms Kala Kala, aunty ta kalleta cikin kulawa tace "Hibbah nasan kinada k'ok'ari da hazak'a pls karki bani kunya, ki mai da hankali akan duk abinda ake koya miki babu ruwanki da k'awaye karatu kikazo yi kuma shi zakiyi, ki kula da kanki Hibbah makarantar nan makaranta ce da take cud'anya da maza kuma 'ya'yan masu kud'i zasu iya rud'arki da abubuwa da dama don haka ki kiyaye, duk da nasan Hibbah na bamai kwad'ayi bace tana jin magana," Hibbah taji dad'in kalaman aunty sosai tace "insha allah aunty zan kiyaye kuma bazan watsa miki k'asa a ido ba, zan maida hankali sosai

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});