Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* A razane take kallonshi "me ya same shi? Tun yaushe ne bashi da lafiya?" Kausar ta lek'o fuskarta babu walwala "wato ke yanzu iskancin naku har sai kun shigo d'aki kun rufe kanku a ciki ko? To wallahi ba'a nan gidan ba don zan sanar da Faheem kwashe kwashen banzan da kike yi, dama tsintacciyar mage bata mage, kizo ki had'a min tea inason nasha kafin na koma asibitin" wasu hawaye suka zubo mata masu zafi tabbas dole ne kowaye ya d'aura zarginsa a kansu tunda suna d'aki ita dashi kuma su ba muharraman juna bane, amma wulakancin da Kausar take mata ya isheta haka itama yau basai gobe ba insha Allah zata bar musu gidansu zata kira Aunty t bata hakuri don gaskiya ta gaji da rashin mutuncin da Faruq da Kausar suke yi mata gara ta tattara ta bar musu gidan su........... "Dalla ki huce ki kawo min tea nace, ai abinda yafi kuka ma sai kinyi shi badai kwad'ayi kika zab'arwa rayuwarki aba" Hibbah t goge hawayenta ta jinjina kai tare dayin hanyar kitchen. Ta had'o mata tea d'in ta kawo mata ta karb'a tana yatsina fuska ba madalla bare na gode ta Saba da wannan wulakancin na Kausar don wai bata isa ba ma tayi mata godiya. Hibbah ta d'anyi k'asa da Kai "Aunty a wane asibiti Daddy'n Nawaz yake zanje nayi masa sannu?" Ta wurga mata harara tare da jan tsaki "b'ace min da gani bansani ba stupid kawai" tamkar an kwad'a mata gora a tsakar kanta, wannan wulakanci dame yayi kama? Koda mutunci ne kawai a tsakaninta da Faheem ace bashi da lafiya yana kwance a asibiti ai ya dace taje tamai sannu bare mutumin da ya zame Mata kamar uba ya rik'eta amana. A sanyaye ta wuce d'akinta Nawaz zai biyota Kausar ta buga masa tsawa ya koma ya zauna, ta shiga d'aki zuciyarta a dagule ta janyo wayarta tana tunanin ko ta Kira Aunty Aysha tana kuma tsoro karta kirata tak'i d'aukar wayar don tasan haushinta take ji, tana mason ta fad'a mata ma jiya ta gama exams d'inta amma tana jin tsoro, number Aunty ta shiga dialing zuciyarta cike da tsoro. Sai da ta kusan tsinkewa sannan ta d'auka "me kika kira kuma ki fad'a min?" Cikin sanyinta tace "Aunty da rana, kiyi hakuri ki saurare ni" "lafiya ai kema kinsan laifinki dole ne nayi fushi dake wato kin had'a kai da Faruq kin bashi goyan baya, Hibbah bazan b'oye miki ba ina tausaya miki Faruq ba cikakken mutum bane don baki fini saninshi ba, d'an uwana ne amma bashi da halin mai kyau kuma halin kirki shine cikar mutum, Hibbah idan har kika auri Faruq to baki yiwa kanki adalci ba ki duba irin rayuwar da kika taso a cikinta karki manta fa har yanzu bakiyi 'yancin kanki ba a k'ark'ashin wasu kike kina musu aiki, idan kika duba sam Faruq bai dace da rayuwarki ba, kamata yayi ki samu mijin da yasan daraja da k'imarku Wanda zai gyara rayuwarki ya ingantata, yanzu na gano nice kad'ai kishinki da tausayinki ke sam ba kya tausayin kanki, rashin zuciya ne irin nawa da nake ta k'orafi akan maganar" Hibbah ta fashe da wani irin kuka "Aunty yaya kike son nayi da raina kina d'ora min laifi babu abinda baki sani ba tsakani na da Faruq ke kika ceco rayuwata daga hannunsa, ni dai nasan wannan k'addara ce ta Allah amma babu sa hannuna akan duk abinda Faruq yake aikatawa tun farko na fad'a masa ni ina da wanda zan aura, kuma yace su Daddy yau zasu je wajen Alhaji zasuyi magana, yanzu nasan Alhaji bazai Hana su Daddy ni ba saboda ya d'auke ni kamar 'yarsa idan nace banaso zaiga kamar don bashi ya haifeni ba Aunty ni addu'arki kawai nake nema." "To ma fahimce ki Allah ya zab'a abinda yafi alkhari amma nidai auran Faruq bai kwanta min ba, yanzu ki shiryowa Yaya abinci kar kisa gishiri yana asibiti bashi da lafiya." Taji dad'in yadda Auntyn ta sauko "Aunty me yake damunsa ne haka?" "Ba komai sai dai kinzo d'in zakiyi mamaki idan na fad'a miki ciwon dake damunsa" ta rausayar kai "to Allah ya bashi lafiya yana wane asibiti?" "Nan dai asibitin da suke ganin likita" "to shikenan insha Allah ina tafe" sukayi sallama ta ajiye wayar tare da nufar kitchenta had'a masa abincin da marasa lafiya tayi wanma ta shirya ta nufi asibitin. A hankali ta shigo sanye take da bak'ar abaya tayi kyau sosai ya dubeta zuciyarsa ta harba, matuk'ar zai k'yalla idanu yaga Hibbah to dole saiyaji wani abu a zuciyarsa ko wanne abu Allah ne yake sashi amma akwai silarshi ko shakka bayayi itace silar wannan ciwon nasa. Bata yarda sun had'a idanu ba ta gaishesu da tambayar ya jikin nasa ta ajiye kayan abincin. Aunty Aysha tana kallonta da nazarin wani abu alamar tausayi "Hibbah ya shirye shirye banji kince komai ba ga Yaya ba lafiya" ta dubeta da mamaki me kuma ya kawo rashin lafiyar Daddy a ciki? "K'warai kuwa abinda kikaji na fad'a shi zaiyi ruwa yayi tsaki a d'aura auren nan don Daddy zaiyi tafiya, kuma nasan halin Faruq sarai bazai yadda a d'aga auren nan ba" ta had'iyi wani yawu ita kam ta shiga uku yanzu ba za'a fasa d'aurin auren nan ba. Faheem yana jinsu bai ce komai ba. Aunty ta kalleta duk tayi wani iri kamar ba ita ba tace "Hibbah ina sauraronki kinyi shiru bakice komai ba, alkawarin dana yi miki yana na nan bazan fasa ba zan bada gudumawata mai tsoka mu siyo abubuwa da ita." Maganganun Aunty sun sata rud'ani da rashin nutsuwa ta mik'e zata fita "Hibbah! Ya haka yaya muna magana zaki fita?" Ta tsaya Jim sai kuma had'a idanu dashi wasu hawaye suka zubo mata zuciyarta ta cushe da wani abu marar dad'i, kawai ta fice. Suka kalli juna da da wani yanayi mai ban mamaki, Aunty ta d'anyi murmushi tace "Yaya yarinyar nan ka yarda bata son auren nan da laifinta nake gani amma na gano wani abu k'ulli ne kawai Faruq yayi mata" ya yamutsa fuska "meye dalilinki na fad'ar haka? Kina da tabbacin abinda ke zuciyarta? Idan tana so zata yarda ta amince ne?" "Hmmm Yaya kenan har yanzu baka fahimci Hibbah ba, Hibbah yarinyace mai kawaici da alkunya tana da biyayya da zurfin ciki, nasan halayenta ni kaina sai tura takai bango nake sanin wani abu nata, matsin da Faruq yayi mata lokacin tana gida badan tana da hakuri ba da zata iya barin gidan don ba kowace macece za'ayi yunkurin rabata da kimarta ba kuma ta cigaba da zama a inda ake barazanar aikata mata wannan mugun abin, yanzu Yaya wanda yaso aikata wannan b'arnar ace yana son ta tsakani da Allah ni nasan k'arya ne yayi haka ne don comma wata manufa. Hibbah bata b'oye min sirrinta d'azu data kirani take fad'a min bata son Faruq lokacin idona ya rufe da fushi nak'i sauraronta daga baya nayi tunani mugunta ce kawai irinta Faruq don karya barta ta auri Wanda

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});