Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shahada). Dr ya shigo tare da budurwar ya shiga duba shi lokaci daya ya gano cewar ya rasu ya lullub'a masa zanin dake jikinsa ya dubi su Daddy "Alhaji sai dai hakuri Allah yayi masa cikawa" su baba dama tuni suka gano hakan sai suka bishi da addu'ar samun rahma wajen ubangiji don ba'a shiga tsakanin Bawa da ubangijinsa. Haka suka d'auko gawar suka mata sutura aka kaishi gidansa na har abada, sannan aka nemi iyalinsa aka fad'a musu. An kashe kudi a bikin Hibbah da Faheem don ko wajen events d'in kawai da aka gabatar kawai kud'insa ya isa ballantana azo ga irin dukiyar da su Abba suka kashe mata a kayan d'akinta dana kitchen, gaskiya su Daddy sun sunyi rawar gani don kuwa Hibbah ta zama 'yar gata ta ko wane b'angare. Wani tank'ameman gida aka shigo da Hibbah ko a iya get d'in gidan kawai kasan gidan ya tsaro mamy data rik'o hannun Hibbah na dama yayin da aunty ta rik'o d'ayan hannun nata gaba d'aya Hibbah a rumgume take a jikinsu fuskarta a lullub'e tana ta kuka k'asa k'asa, mamy ta rad'a mata "my Hibbah nemi tsarin Allah ki yi add'u kafin ki shigo ki shigo da k'afar dama kiyiwa aurenku addu'a da sa masa albarkar ubangiji" duk da kuka take hakan bai hanata yin addu'a ba ta kuma shiga da k'afar dama. Haka su mamy suka shigo da ita cikin k'aton gidan nata dake ta zuba uban k'amshi mai dad'i direct bedroom d'inta suka huce da ita inda suka sauketa a kan gadonta, nan mamy ta kuma yi mata nasiha sosai a k'arshe ta rufe da kuma koya mata wasu dabarun zama da miji kafin kuma su tafi. Haka 'yankai Amarya suka tafi suna ta zuba santin gidan, aka bar Hibbah ita kad'ai sai Saudat Safiyya da fauzy da aka bar mata suma suna gama gyara inda 'yan kawo Amarya suka b'ata suka ce zasu tafi Saudat tace "Aunty Hibbah mu dai mun tafi kar ango yazo ya bubbugemu, ni dai da safe zanzo gashi" fauzy tace "lallai kam ni dai kazar za'a ajiye min" Safiyya tace "auntyna mudai mun tafi" suka fita suna dariya adamu driver ya kaisu gida. Haka suka bar Hibbah ita kad'ai duk tsoro ya cikata ga kuma kunya tana tunanin da wane ido zata kalli Faheem a matsayin mijinta? Tunaninta ne ya katse a lokacin da taji k'arar bud'e k'ofa da sauri ta kuma yin k'asa da kanta zuciyarta na harbawa da sauri sauri. Faheem ne ya shigo shi da Haisam dake rik'e da leda a hannunsa shima da k'yar Faheem ya yarda ya rakoshi wai ai ba auren fari bane kuma Dan d'an uwansa ne bashi da yarda zaiyi. Suka k'araso da sallama a zuciyarta ta amsa, suka k'araso suka zauna Haisam ya ajiye ledar dake hannunsa yana cewa "Amaryarmu k'anwarmu sannu ya gajiyar biki" Hibbah tayi shiru bata ce komai ba, Haisam yace "too k'anwata yau kuma rowar magana ake min? Ko da yake ba laifinki bane Amarya ce ke" ya fad'a yana murmushi "to tunda na rako miki angonki bara na tafi" sai kuma yau d'an fara yi musu nasiha kafin ya mik'e Faheem ya raka shi har bakin get sannan ya dawo. A inda ya barta anan ya dawo ya sameta, a hankali ya hayo kan gadon ya yaye mahafin dake lullub'e a fuskarta tare da shafo fuskarta ruwa yaji a hannunsa da sauri ya juyota suna fuskantar juna ya shiga goge mata hawayen ya d'anyi k'asa da murya "haba my hrt desire kuka kike yi gidana fa aka kawoki gidan yayanki kuma mijinki mai k'aunarki to mene naki na kuka kuma Uhumm?" Ita dai Hibbah bata ce komai ba tayi k'asa da kanta saboda tsananin kunyar Faheem. Faheem yayi murmushi ganin yadda ta wani yi k'asa da kai "nifa gaskiya wannan kunyar yau a ajiyeta a gefe don baza ta k'ware ni ba" ina ai Hibbah ji tayi kamar k'asa ta tsage ta shige ciki. Hannunsa ya d'ora a kan cikinta yana d'an dannawa "my hrt desire hidima ta hanaki cin abinci koh? Gashinan cikin ya kuma matsewa taso muje na baki" ai hankali kanta a k'asa tace "naci abinci na k'oshi" "a'a banyarda ba tashi maxa muje muyi sallah mu godewa Allah sai na baki wannan d'an cikin ne yaci abinci" ya fad'a yana jan hannunta suka sauko daga kani gadon ya zaunar da ita a kan carpet, ya fita kitchen ya d'augo plate da cup ya ajiye lokacin ita har tamayo alwala, shima ya shiga yayo kafin ya fito ta d'auko hijab d'inta yana zuwa yaja su sallah, nan suka gabatar da sallar bayan sun idar ya shiga kwararo addu'o'i kafin ya dafa kanta yayi mata addu'a, bayan ya gama ya shiga yi mata tambayoyi a take duk ta bashi amsoshinsa wanda dama yasan za'a rina. Ya janyo place d'in da cup ya juye kazar a plate d'in ya tsiyaya mata madarar a cup sannan ya zauna tare da janyota jikinsa ya gutsuro ya kaishi dai dai bakinta a hankali ta bud'e bakin cike da kunya ta amsa tana taunawa kamar bata so. Ya d'auko madara yasa mata a baki ta kurb'i kad'an ta kawar da kai, ya kuma gutsurowa zai sa mata ta kawar da kai "daddy na koshi fa" ya d'an had'a rai "wannan cikin naki yana bukatar abinci kuma kina cemin wani kin k'oshi ki amsa ko kuma na miki d'ura" haka badon taso ba ta bud'e bakin ya saka Mata, haka yayi ta bata har sai da ya tabbatar ta k'oshi sannan ya daina bata shi kuma ya shiga ci. Shima saida ya k'oshi sannan ya d'auke gayan daga wajen ya gyara, ya dubeta gyangyad'i ma ita take yi ya d'auketa cak ya d'ora bisa gado. Firgit ta tashi ya dubeta yana murmushi "bacci ko my hrt desire?" Ta d'aga masa kai yace "to ina zuwa" ya mik'e ya fita. Ta ganin ya fita itama ta tashi ta cire kayan dake jikinta ta d'aura towel ta Shiga wanka da alwala. Ta fito ta mulke jikinta da wani mai da Aunty ta bata mai tsananin k'amshi ga kuma turarukan da Aunty da mamy suka ce idan zata kwanta ta shafa sai kuma Wanda gwaggo ta bata, haka ta d'auko duk tayi amfani dasu sai k'amshin ya had'e ya bada daddad'an k'amshi. Ta d'auko wata rigar baccinta iyaka gwaiwa samanta net ne daga wajen k'irjinta sai kuma k'asan yadi mai taushi da silb'ine hannun kuwa na bra ne ta saka sannan ta kashe fiyila ta koma kan gadon ta karanto suratul mulk da iklas, falaq, nas sai ayatul kursiyyu ta tofa a tafin hannunta ta shafe jikinta sannan ta kwanta a b'arin hannunta na dama ta karanta بسم كاللهم اموت و احيا sannan ta kwanta zuciyarta cike da tsoro. Ta Fara bacci kenan taji mutum a kusa da ita yana shafa jikinta a hankali tayi firgit ta tashi ta juyo Faheem ta gani a cikin bargon shi ko a jikinsa yana cigaba da shafata, ta dubeshi a marairaice "Daddy bacci nake ji" wannan daddy da take kiransa dashi yana b'ata masa rai a zuciyarsa yace yau zan bambance miki tsakaninki da Nawaz don ya kirani Daddy kema saiki ki fad'amin hka.

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});