Chapter 29
Chapter 29
tafiwajen daddy'n shi. Tayi masa godiya sukayi sallama ta shiga ciki, bata iske kowa a parlor'n ba ta shige d'akinta tare dayin 'yar ajiyar zuciya. Labarin zuciya a tambayi fuska tana tsoran Faheem in dai ya ganta da wani jikinta yakan bata wani abu Wanda ta kasa tantance komene shi, tana son ko sau d'ayane su gaisa da Jabeer don ya fahimci irin manufofinsa, don d'an mutunci ne aurene ya kawoshi ba wai wani shashanci ba. Ta yunk'ura ta bud'e ledar wani k'amshi ya daki hancinta mai dad'i, wani material ne marun mai shegen kyau da mayafinsa da takalmi sai turare da mayuka da kud'i dubu biyar, wani card mai hoton zuciya yafi tafiya da hankalinta, ta d'akko ta bud'e kalaman k'auna ne taci karo dasu Wanda suka sanyaya mata zuciya, karo na farko da taji ta gamsu ta amince da auran Jabeer, don miji ne na k'warai ta lumshe idanu, hak'ik'ashi d'in ne take gani Jabeer yana da kirki yana Mata so na tsakani da Allah. Faheem yana shiga d'aki yayi wurgi da jakar hannunsa ya d'ora kansa a pillow rikitaccen abun yana da rikirkita tunani da wahalar fahimta, zuciyarshi ta Gaza sarrafuwa yana da juriyar gaske akan duk abinda ya jarrabtu gareshi amma me yasa ya kasa daurewa? Allah mai iko ya dafe zuciyarsa abinda yake ji a cikinta bazai iya fad'a fatar baki ba, ya runtse idanunsa shi bai tab'a samun irin wannan matsalar Mai zafi a cikin zuciyarsa ba, ya lalubo wayarsa tare da earpiece yasa a kunnensa k'ira'ar sudais ne ke tashi harshensa nabin surar tiryan tiryan ya haddace ayoyin nutsuwa ya samu da yak'inin wani abu ba makawa zai iya kasancewa dashi. *** Su Hibbah suna ta kiciniyar fara exams (WAEC) ta maida hankali tuk'uru wajen karatunta dan ganin result d'inta yayi kyau, sabon malami aka kawo musu don yi musu lesson d'in waec, ranar wata laraba kamar yadda suka Saba ita da fauzy suna zaune a cikin ajinsu suna solving wani physics dayake babu malami a cikin ajin, wata yarinya ce ta shigo tare da neman excuse tace "wai Hibbah Mukhtar Muhammad tazo inji uncle Sadeeq," suka kalli juna ita da fauzy sannan ta kalli yarinyar "kice masa ganinan," ta fad'a tana mik'ewa, direct office d'inshi ta nufa da sallama ta shiga ya amsa ta gaisheshi, bai amsa ba sai nuna mata d'aya daga cikin kujerun office d'in. Ya dubeta yayi mata murmushi "barkanki da safiya 'yar kyakykyawa muryarki tana da d'an karan dad'i," ita dai Hibbah batace komai don a d'osane take akan kujerar, kanta a k'asa tana murza zoben hannunta shi kuwa ya zuba mata idanu ta tsargu da kallon da yake mata. Matashi ne dogo siriri fari idanunsa a tsatstsaye suke irin na mashahuran 'yan duniyar nan, inyana kallon mace dole gabanta ya fad'i gashi kamar maye idan ya k'ullawa mace. Uncle Sadeeq shu'aibu kenan tunda yazo ya k'ella ido akan Hibbah ya kasa nutsuwa duk da yaga yarinyar bata hannu bace, amma idan ya k'ullawa mace saiyasan yadda yabi ya yaudareta, balke mace irin Hibbah ina zai iya bari, ai kota wane hali sai ya bi harta sallama masa don yaga kamar tsoranshi take ji. Ya dubeta "Hibbah kenan gaskiya kina da baiwa dan nidai ban tab'a con karo da irinki ba gashi muryarki akwai sanya mutum kasala," yana wani murmushin k'eta irin nasu na salon yaudara, ya janyo take away d'insa dankali ne da k'wai sai k'atuwar kaza ya Fara ci, "bismillah, ko na baki ne a baki? Kinsan ke ta dabance" ta kalleshi mamaki yake bata sosai "na gode ni Zan koma class," "haba Hibbah me yasa? Ko kin gaji da hirar tawa? D'auko min maltina a fridge," haushi taji kawai tasan d'an iskane ba mutumin kirki bane ta mik'e ta nufi fridge din. Ya k'urawa bayanta ido dama hikimarsa kenan idan ta tashi ya k'are mata kallo duk da hijjab d'inta yayi masa garkuwa amma hakan bai hanasa bin k'wak'wk'wafi ba. Ta ajiye masa zata tafi yayi saurin cewa "no no baby zauna tukunna ban gama ba ai," ta kuma had'a rai don dai babu yadda zatayi ne da tuni ta ci masa mutunci. Yayi dariya "smile mana Hibbah akwai lefi don nace ina sonki kinyi min ne, naga har yanzu a tsorace kike Dani ki saki ranki, ina sone mu more *RAYUWA*rmu, abinda za'ayi yanzu zan baki address d'ina ko?" Waro ido waje tayi tace "uncle me kake fad'a haka gaskiya ni ba 'yar iska bace," ta kuma bata rai tayi tunananin zaiji haushi yace ta tafi sai ma taga yayi dariya "no problem mai sonka shi yake binka don haka ni idan abu yayi min bana damuwa kiyi min kwatancen gidanku ni zanzo," ta kuma zaro ido wai ita awa takai wannan gidan Faheem ai ta shiga uku, to tamayi me da d'an bariki, "akwai dokoki da yayana ya kafa a gidansa ni bana tsayawa da kowa," ya fashe da wata muguwar dariya, da sauri ta fita tana tunanin kodai tab'ab'b'ene, ya bubbuga table d'in dake gabansa yace "ta yaro kyau take bata k'arko idan kinsan wata ai bakinsan wata ba." A tsorace ta isa class d'in fauzy ta kalle "Hibbah lafiya na ganki duk a tsorace," murmushin k'arfin hali ta k'ak'aro "ba komai fauzy," "to me un Sadeeq d'in yace miki?" Hibbah ta d'auko physics textbook d'in tana cewa "kawai wani aiki ya sani," "uhhmm Hibbah kenan kina k'ok'arin b'oye min wani abu ne, amma ki sani Uncle Sadeeq ni ya fara kira akan batun yana sonki bai samu dama bane shine ya rabu Dani," Hibbah tai mata kallon mamaki "amma shine baki tab'a fad'a min ba" "to ai gani nayi ba wani abun bane tunda mun rabu da shi akan ya hakura, amma ke me yace miki?" Hibbah ta kwashe duk yadda sukayi ta fad'a mata, fauzy tace "dama fa malamai suna ta fad'a wai d'an iskane don school d'in daya baro an tab'a kamasa da wata d'alibarsa," Hibbah ta gingina kai "tab' ai kuwa nan bazai samu matsuguni ba," "ai kuwa dai kuma wallahi ya kuma kiranki sai mun had'ashi da principal" fauzy ta fad'a da masifa, haka sukayi ta tattauna maganar har aka tashe su. Da yamma Nawaz yana zaune wajen Isah mai gadi suna wasa don Isah akwai barkwanci, ya lek'o yace "soja" don haka yake kiran Nawaz don yaga Nawaz akwai son wasa da bindiga sai ya saita Isah yana cewa "fire". Isah yace "Nawaz jeka cewa Hibbah tayi bak'o na fad'a masa dokar Alhaji shiyasa bai shigo ba," da gudu ya shiga cikin gidan "Aunty Hibbah uncle Jabeer," bata yi mamaki ba don wasu lokutan akwai matsalar network sai kayi ta kira yaki shigowa. Wani leshinta ta d'auko purple ta sanya tayi kyau ta fito, tayi zaton sabuwar mota ya canza sai da tayi tozali dashi ta tub'une fuska kamar kashin shanu, tana tunanin ya akayi mutumin nan yasan gidan nan don bak'in naci. Wannan nataccen murmushin nashi yana kan fuskar shi, idanunsa k'uru k'uru a kanta ya lashi leb'ensa tare da had'iyar wani miyau k'ut, ashe hijjab d'in nan yana hanasa ganin kaya, shi duk abinda yake nema a wajen 'ya mace ya gano shi gun yarinyar nan. Ta k'araso gami da kawar da kanta gefe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63