Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shiga tayi wanka ta sauya kayanta tayi sallah ta nufi kitchen, tana cikin aiki Nawaz yace Daddy na kiranta. Ta iske shi zaune yana kallon MBC 2, taje ta durk'usa a gabansa yace ta kawo mishi ruwa, yaso su had'a ido amma kunyarta tayi yawan gaske, ta kawo masa ruwan a cup ya karb'a yasha. "Hibbah" ya furta, yau dai furucin nan yana tsumata, "d'auki wannan kayan naki ne" mamaki yasa ta kasa godiya d'auka tayi ta nufi d'aki. A kan gado ta zazzage, atamfofi ne guda uku da dogayen riguna biyu da hijjabai biyu sai riga da skirt kala biyu, masu daraja don duk 'yan waje ne, da mayuka da turarukan Mata, ta lumshe idanunta tunanin Faheem take da alkharinsa tun sanda suna mota take tuno irin k'amshinsa da kalamansa, Hibbah yadda yake furta sunan a tak'aice a harshensa, wani abu zuciyarta ke zargi don me Faheem yake yi mata wad'annan tambayoyin? Bata yi mamakin wad'annan kayayyakin ba, duk da bai tab'a yi mata kyautar kaya masu tsada kamar wad'annan ba amma dama ya saba yana yi mata kyauta. Ta d'auko takarda da biro, ta soma tunanin me zata rubuta,kawai sai ta fara rubutun. _Daddy_ _Bani da kalmomin godiya a gareka, na gode Allah ya k'ara girma da bud'i na alkhari ya barmu da Nawaz._ _Hibbah._ Ta kira Nawaz ta bashi ya kai masa, yana kwance a parlor ya haye kansa "Daddy gashi inji Aunty Hibbah" ya karb'a ya bud'e ya karanta, yayi nazarin kalamanta wani d'an murmushi yayu yarinyar ta shiga rayuwarsa, yayi ajiyar zuciya yau saboda da ita ne kawai yaji bai son fita ko ina yana hutawarsa. Allah yasa ta fahimci manufarsa, ko tama sanu take sharewa don yayi mata hannunka mai sanda oho, ai ita mai hankali ce zata gano shi a hankali matsalarta dai rashin son sakewa a gidan indai yana gidan, sai tayi ta nuk'u nuk'u bata son ko ganinta yayi har abin ya zame mata tsoro. Da yamma ya samu ya fita don anyi masa waya ana nemansa, yana fita Jabeer yayo mata waya yana waje, nan ta shirya ta ja hannun Nawaz suka fita. Bayan sun gaisa Jabeer yace "Hibbah banji inda shawarar ku ta tsaya ba akan sa ranar nan, sauraronki nake yi na samu Aunty Aysha naji bakinku yazo d'aya itama tace wai zata tattauna da Umma, abinda yasa na dame ki ni mutum ne mai d'aukar abinda nake so da mahimmanci ban son shiririta a al'amurana, idan kina ganin abin bazai yiwu ba ki fad'a min gaskiya kawai kar ki b'oye min" tayi d'an murmushi "kasan ba nike da kaina ba kuma nayi maka bayanin komai bani zan aurar da kaina ba, amma ka samu Alhaji Ku tattauna kaji ta bakinsa," "to naji dad'in hakan, kar kiga zak'ewata ina sonki da yawa shi yasa nake nuna miki damuwata kuma nasan kema kina sona, zan sameshi in Allah ya yarda." Faheem ya dawo ya huce su, Nawaz ya bishi don taryarshi, al'adarsa kenan komai yake yi da yaji motar Daddy'n shi ya dawo to saiya taro shi, Faheem ya saba mishi da hakan yakan ji dad'i aranshi sosai. Tayi ajiyar zuciya Faheem mai sata cikin rud'ani in dai ta ganshi sai komai ya sauya mata in a parlor take ta gudu d'aki, in tana tafiya ne taji kamar anyi mata dabaibayi dole take tsayawa sai ya huce sannan ta cigaba, ya katse mata tunani "ina son mu gaisa da yayan nan namu amma naga kamar bai da son mu'amala da mutane, a k'alla ya sha wucemu anan yasan kuma ina zuwa wajenki ne don na aureki amma ko duban inda muke baya yi bare ko hannu ya d'aga min, ni kuma inason mu gaisa dashi ya sanni sosai don yasan shima yana da ruwa da tsaki a cikin maganar aurenki tunda a hannunsa kike zaune" "gaskiya ne kuma mutumin kirki ne, kawai dai allah ne bai nufa zaku gaisa d'in ba sannan na fahimci bai da wani ra'ayi akan shiga maganar aure na tunda bai tab'a yin magana akan hakan ba, amma nasan idan lokaci yayi zai yi." Ya gyada kansa "shikenan Allah ya tabbatar da alkhari na gode" ya bata wani k'unshi a rufe a takarda. "Kai baka gajiya yau da gobe sai Allah," "Ana gajiya da masoyi ne?" Mutuminta ne ya huce su a mota, Faruq d'an rikicin duniya da da inda zata je data gudu sai ya tafi saita dawo domin zai sa ta a gaba ne kawai sai ya sata kuka. Sukayi sallama ta shigo gida, ta huce shi a cikin motar kamar bata ganshi ba, ya dad'a k'uluwa kishi ke cinsa kamar masifa, wai wannan Jabeer da jaraba tsiya yake duk yadda ya tozarta Hibbah a gabansa bai hakuri ba. Ya fito yana take mata baya ya janyo mayafinta ba shiri ta yo baya kamar zata fad'i ranta a b'axe ta kalleshi zallar masifa ta gani a idanunsa yau ta tab'o Faruq, mai cin zalinta a bulus bare da dalili. Ya nannad'e mayafin a hannusa tana ja ta kasa k'wacewa, ya kuwa murd'e hannunta ta rintse idanunta ji tayi kamar zai b'allata tayi wata 'yar k'ara "wayyo Allah na!" Abinda ta tsana kenan wannan rashin mutuncin da Faruq yake yi mata tana d'aukarsa tsabar tsana ce da rashin galihu. "Zan nuna miki mahaukacin kishi na akanshi zan iya komai tunda kika jawo mutumin nan duk da irin tozarcin da nayi miki a gabansa ashe tsugunno bata k'are ba, matuk'ar na k'ara ganinki dashi sai na miki rashin mutuncin da baki tab'a zato ba, don ji nayi kamar nasa bindiga na harbi k'ok'on kansa." Faheem ne ya fito yaji kuma furucin Faru$q sarai amma yayi kamar bai san su ba yayi wucewarsa, wani bak'in ciki taji ya k'ulleta kamar ta fad'i ta mutu wajen. Babu mutumin da a duniya bata son mutuncinta ya zube a wajensa kamar Faheem tana ganin girmansa, gashi a yau yaji ya gani hujja ce da zai d'ora zarginsa akan gaskiya tana mu'amala da Faruq bawai iyakar soyayya ba, wani tunanin zai yi don Faruq dai bashi da halin k'warai akan 'ya mace, gashi ya rik'e hannunta gam bata da wani sauran mutunci a idanun Faheem, wannan wace irin *RAYUWA* ce............... *#JUMMA'AT MUBARAK TO YOU ALL😍😍🀝* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page3⃣7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Wani sambatun banza yake yi mata ta tureshi a fusace "Allah ya isa cin zalina da rashin mutuncin kake min, k'arewar tsana k'in jini ka kashe ni ka huta, babu mutumin da na tsana a duniya irin ka.........." Kuka ya shak'eta, maganar ta shige shi domin alwashin ya daina mata irin wannan abun amma why? Why yaji kishinta haka? Kishinta ne ya tursasashi don abinda yafi wannan ma zai iyayi sai dai duk abinda za'a yi masa ayi masa, ta shige gida, a cikin d'akin ta watsar da kayan ta kwanta kan gado gami da kifa kanta a kan pillow, ta gaji da wannan wulak'ancin da cin zarafin na Faruq wai me ta tsare masa ne a duniya? Burinsa ya sata kuka ya zubar mata da k'ima da daraja a idanun mutanen da suka d'auketa mai mutunci, to

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});