Chapter 40
Chapter 40
canzawa kuma shiriya ta Allah ce, amma komai yanada sanadi kuma zanso ace kece kika ja ra'ayina zuwa halaye masu kyau, Hibbah na k'agu muyi aure" ta numfasa "ni har yanzu zuciya ta bata yarda da mutum irinka ba, ban yarda wai k'aunata kake tsakani da Allah ba shiyasa nake ganin bamu dace da juna ba, kuma bazan b'oye maka ba Jabeer yayi magana da Aunty Aysha akan sanya ranar auren mu kaga bai kamata mu dinga yin abinda bazai yuwu ba." Fuskarshi ta canza ta soma jaja jaja, sauke Nawaz dake goye a bayansa ya rik'o hannunta da kyau, ta shiga kiciniyar k'wacewa. Ya zaro idanunsa waje "Hibbah saboda ina sonki shine kike yi min wannan wulakanci kin sani Allah ne kawai yayi min wannan jarrabin amma matsayina ya wuce ajinki bawai ina lallaminki bane ni mace bata juyani ko tirsasani akan abinda baya cikin ra'ayina, sai na aureki zaki gwammace kid'a da karatu sai kinyi nadamar abinda kikayi min zaki san kin auri d'an bariki!" K'wallar data taru a idanunta ta d'igo a kumatunta don ganin Faheem ya dawo ya fito daga motarsa, yayi shigewarsa ko kallonsu baiyi ba yayi wucewarsa. Faruq yana ta sambatun surutunsa don a cikin zafi yake baima damu da ganin Faheem ba. Hibbah duk hankalin ya tashi bata so ko kad'an Faheem ya ganta da wani bama Faruq kawai ba. Faheem yana shiga parlor ya dafe kansa dake sara masa jagab ya zauna akan kujera ya rufe idanunsa zuciyarsa tana bugawa, anya wannan abin nashi zai d'ore kuwa anya bazai je doctor ya duba lafiyarsa ba kuwa don yanaji kamar akwai wani abu dake damunsa. Ta shigo idanunta cike da hawaye kamar kullum Faruq ya saba sata kuka, ranta a b'ace yake don baram baram suka rabu da shi, taya ma zasuyi shiri da Faruq harma suyi wai aure, bayan kullum cikin fad'a suke. Tayi turus kamar tayi tuntub'e sai kace sai kace wadda aka yiwa dabaibayi ta dad'a shiga rud'ani ya dubeta cikin idanu wani abu data gani ya kuma sata rud'ani wani yanayi taji kamar ta fad'i a wajen, abin ya cigaba da zagayeta sai kace sihiri, a hankali taja k'afarta da tayi nauyi ta wuce d'aki ta rufo k'ofar gami da jingina a bayanta a jikin k'ofar, ta goge hawayenta cikin wani rashin jin dad'i da rud'ani meke damunta ne Faruq ya b'ata mata rai, tare da tasirin wani abu dake faruwa da ita. To amma Faheem fa me yake damunsa kamar ba shi ba, wai meke damunsa a yadda ta gansa kace kace cikin damuwa, duk sai take jin kanta ba dad'i sam ta kasa sukuni, to wai mene nata da shiga damuwa don Faheem yana cikin damuwa ita da ba matarsa ba. Faruq yana fita daga gidan Faheem cike da b'acin rai ya nufi gidan Aunty Aysha, bayan yayi parking ya nufi cikin gidan yayi knocking mai aikinta ta bud'e ya shigo ya zauna a kan kujerun d'akin. Ta shigo "barka da zuwa yau kaine a gida na?" Yayi murmushi "to ya zanyi dake nayi fushina na gala ba zan iya gaba da ke ba, d'an uwa baya fushi da d'an uwansa" tayi dariya "Umar Faruq kenan yaya halinka? Ka canza ko har yanzu kana nan dashi?" "Ki bari dai kawai Aunty yanzu ma tawa ce ta kawo ni domin kece jagoraba don nasan zaki sharemin hawaye na," ya sassauta murya "Aunty aure nake son yi a cikin wannan lokacin kafin na tafi Germany, ki bani shawara kisa albarka kuma kiyi addu'a" tayi shiru tana nazarin maganar Faruq lallai Faruq yayi hankali ya nutsu tunda har ya yanke shawarar yayi aure, "to naji bayaninka kuma shi aure alkhari ne Allah yasa albarka yasa hanyar shiriyarka kenan ka dena wad'annan d'abi'un, nasan hali dai zanen dutse amma in da nauyin iyali a kan rusuna koma a daina gaba d'aya, yaushe ne za'a Fara shirye shirye, ka sanar da momy da Daddy da kuma Ya Faheem ya sani shima ko?" Ya sosa sumarshi "hmmm basu Sani ba tukuna, manta da Ya Faheem kinsan shi tsarine dashi zai iya kawo suka cikin lamarin don bana tunanin zai goyi baya" "to ai kuwa Ya Faheem shike da ruwa da tsaki a maganar aurenka shine yake wakiltar Daddy tunda ba zama yake yi a gari ba kuma kaga Abba ma bai fiya zama ba, kasan ance babban wa uba ne ko?" Ya yamutsa fuska "ai kin gane ni na fahimci baya son alak'ata da yarinyar, labarin zuciya a tambayi fuska, kawai dai bashi da yadda zaiyi ya rabani da abinda nake so" Aunty ta girgiza kai "a'a shi dai yana duba halayyarka ne saboda me zaik'i son abinda kake so shi zaifi kowa farin ciki da aurenka, a kullum burinsa Faruq ka shiryu ka bar kaza da kaza wannan abin da kake yana zubar maka da k'imane fa," "Nifa ina mamakin wannan wane irin hali ne nawa kuke ta aibatani, ni ba kisan kai nake ba, ba fashi da makami ba ba shan giya ba, ba kuma na ta'ammali da miyagun aiyukan ta'addanci, men's a cikin rayuwar dana keyi bai hanani bautawa mahaliccina ba, na lura gani kuke ki kamar na kafirce ko bansan Allah ba ko nauyi zunubi na yakai Allah bazai yafe min ba ku daina shiga tsakanin bawa da ubangijinsa domin shi gafuru rahim ne." "Gaskiya ne to amma babu Wanda ke son yaga nasa ya lalace in baka gyarashi ba duniya zata gyara maka shi, in baka fashi da shan giya amma kamannin mutum ake dubawa a gane yaya halayyarsa take care banzane kona kirki, kuma banji kayi lissafi da neman mata ba ko ita bata cikin manyan ayyuka zina fa, dole ne Faruq na fad'a maka gaskiya nasan da d'aci da ciwo amma ina tausayin wadda zata aureka, ina tunanin rayuwarta a hannunka domin idan neman mata ya damk'i mutum masifa ne, don barinsa ba k'aramin jihadi bane......" Ya d'aga mata hannu ransa a b'ace "kin gani ya isa kawai bana son wani k'wak'ule k'wak'ulen maganganu ina ruwanki da harkokina don sa ido irin naki ai kowa da tashensa lokaci ne idan ya wuce ai shikenan kuma aure ne sai nayi" tayi murmushi "Umar Faruq kenan to a ina yarinyar take nasanka da lek'e lek'e da gane gane, zanso ganin wannan yarimyar dole na kirata mai sa'a don ta ciri tuta tunda har zata auri k'anina" yayi dariyar jin dad'i "yauwa mutuniyata ai 'yar gidan ki ce ba wata bak'uwa ba, yarinyar nan ce Hibbah" ji tayi kamar gini ya ruso Mata rigigim! Ta zaro idanu "wace Hibbah? Badai tawa ba?" Ya gyad'a kansa "Hibbah dai da kika Sani.................." *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Aunty hankalinta yayi mummunan tashi "yaushe har ka yaudareta ka hure mata kunne kuka k'ulla soyayya tayi k'arfi haka?" "Ni ina sonta kuma itama tana sona duk da miyagun halayena, bata ganin aibuna kuma tace bazasu hanata aurena ba" cikin b'acin rai ta nunashi da yatsa "wannan shirin ka ne ni nasan k'aryane, yaudararta kayi don magana ce wannan da k'wak'walwata ta kasa d'aukata ba sonta kakeyi tsakani da Allah ba, ka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63