Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yace "saki daya nayi mata" saki daya kuma malam fasika ce fa koka manta, kenan zaka dawo da ita nan bada dadewa ba." Lami ta tareshi da fadin haka. Malam yace "wa? Allah ya tsareni da kuma zama da ita, dama can saboda ban samu haihuwa bane yasa Na aureta yanxu kuwa allah ya azurtani. Ni ina ma shakku Anya wannan yarinyar jini nace kuwa?" Cikin tsananin kuka umma tace "wallahi 'yarkace malam jininka ce" ta juya ta kalli lami cikin kuka tace "Yaya kiji tsoron allah ki rinka tunawa da mutuwa da kwanciyar kabari, kinyi min sharri akan abinda ban aikata ba kisani sai allah ya bi min hakkina akan abinda kikayi min..........." Kukane yaci karfinta. Hibbah ce ta matso kusa da umma itama hawaye na bin fuskarta, ta shiga sharewa umma hawayenta, rumgume ta umma tayi tana cewa "ya allah ga amanar 'yata nan, Allah ka kareta daga dukkan sharri na mutum kona aljan Allah ka tsareta daga dukkan abinki kasa tafi karfin makiyanta" ta fada cikin kuka. Malam Mukhtar yace "ai da 'yarki zaki tafi baza ki barmin ita a nan ba" cikin sauri lami ta katse shi "a'a malam ka barta a nan kanaso tajene ta kwaso irin halayenta?" Malam yace "ai bana zaton 'yata ce shiyasa gara ta tafi da ita kawai" "a'a malam gara ka barta anan koba komai zaka tserar da ita daga halakar fadawa zina" Malam Habu ya kalli Umma da Hibbah yarda suka kuma kamkame juna suna kuka sai yaji sun bashi tausayi, yace "Aysha taso mu tafi gida kiyi hakuri kinji" cikin kuka mai ban tausayi ta kalleshi tace "Yaya tayi min sharri ta rabani da farincikina Hibbah, yanxu kowa a garin nan kallon fasika zai rika yimin alhalin ni ban taba zina ba......." Wani kukan ta kuma saki tana kuma rukunkume Hibbah. Hibbah kuwa hankalinta ne yayi mugun tashi ta shiga tunani _zina? Umman nawace ke aikata zina? Me yasa Inna lami bazata taba kaunar ummana ba? Me tayi mata a *RAYUWA* da har ta tsaneta haka_ Malam Habu ya katse mata tunani da cewa "kiyi hakuri Aysha ki saka aranki wannan itace kaddarar da allah ya aiko miki kiyi kokarin cinye wannan jarrabawar, *RAYUWA* ce wata rana sai labari kinji? Kuma maganar mutanan gari kuma dama ni na yanke shawarar zan tafi dake can bunkure ki zauna, yanxu idan mun shiga gida nayiwa su gwaggo bayani sai mu huce" Kai ta daga masa sannan ta mike tana kallon Hibbah. Murmushi ta kakalo tace "Hibbah zan tafi nasan zaiyi wuya na dawo nan kusa, Dan allah ina rokonki Hibbah ki kula da kanki ki zamo mai hakuri da juriyar duk abinda zaayi miki. Nasan zaman daza kiyi a gidannan sai yafi na baya kunci da wahala, nasan kina da hakuri to ki Kara akan wanda kike dashi kinji allah yayi miki albarka yasa kifi karfin makiyanki ya kareki daga dukkan mugun mutum." Rike hannunta Hibbah tayi cikin kuka tace "Umma Dan allah karki tafi ki barni wallahi idan kika tafi Inna kasheni zatayi don allah ki zauna" ta kuma fashewa da kuka. Umma cikin hawaye tace "kiyi hakuri Hibbah mahaifinki yana zargina da aikata zina, sanadiyyar haka ya sakeni kuma koda bai sakeni ba aure da zargi bazai yuyu ba. Ki hakuri Hibbah Zan tafi amma zan rinka zuwa dubaki." A hankali umma ta zare hannunta daga na Hibbah sannan tace "kirike addu'a itace makamin mumini, karki manta da azkar na safe da maraice sannan alwala kafin ki kwanta kamar yarda kika saba, da yardar allah saikinfi karfin duk wani mai nemanki da sharri." ahankali Umma ta rinka ja da baya tana tafiya, da gudu Hibbah tazo ta rumgume ta tana rokonta karta tafi. "Kiyi ki barmin gida kafin nadawo", malam Mukhtar ya fada yana fita a gidan. Ita kuwa lami guda ta Saki tace "saika tattara kanwarka Ku kara gaba ai dama duk wacce tayi gigin hada miji dani sai taga abinda yafi haka", ta fada tana kuma shekewa da dariya. Mamaki da al'ajabin abin ne ya hana malam habu magana ya kalli Umma yace "kiyi hakuri mu tafi yamma nayi." Haka suka rabu su biyun duka suna kuka. Bayan fitar su umma haka Hibbah ta zauna tanata rusa kuka mai ban tausayi, lami ce ta kalleta ta tabe baki tace "ni bani kudin sana'ata, gara ma ki daina yi mata kuka don kema kin kusa barin gidannan." Mika mata kudin tayi, fizgewa lami tayi tai gaba. Ita KO Hibbah saboda tashin hankali tama manta bata fada mata akwai canjin sale ba............. *by* *MAMYN NAJMAH* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page 8⃣to9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *ina neman afuwarku na kuskuren danayi a last page na, fatan za'a yimin uxuri* *Ina mika sakon barka da sallah ga dukkan masoyan aunty na _AYSHA ALIYU GARKUWA_. Ina kuma baku hakuri na jina kwana biyu da banyi typing ba, abubuwa ne sukayi yawa don ko na happy sallah bansamu damar yi muku ba. Masha Allah yanzu komai yayi normal kuma insha allah zaku cigaba da jina. ~Aci gaba da gashi~.* Tun karota yayi gadan gadan ya hayo gadon tare da fizgota ta fada cijikinsa, ya shiga shashshafata. Jikin ta ne ya dauki rawa tamkar mazari saboda taji bokon abu, kokarin kwace kanta ta shiga yi duk da bata da wani karfi saboda zazzafan zazzabin da take fama dashi. Cikin kwarewa yake bin gabbanta yana shafawa hannunsa ya dora kan dukiyar fulaninta, jin hannunsa a kan kirjinta tayi cikin zafin nama ta hankadashi ya fado kasa da sauri ta duro daga gadon ta nufi hanyar fita. Fizgota yayi tare da cewa "ke kin isa na shigo dakin nan ba tare dana biya bukata ta ba, wallahi tunda na bawa waccen matar kudina kema saina fanshe a kanki." Ya fada yana janyota jikinsa tare da shafa fuskarta yace "kina da kyau baby, me yasa baza ki yarda dani ba? Uhum? Kibani hadin kai mana." Banza tayi dashi tana cigaba da kiciniyar kwacewa. Ganin zata bata masa time yasa ya ja wuyan rigarta tare da ketawa, take rigar ta yage dukiyar fulaninta ya bayyana. Rikicewa yayi ganin yarda suke a tsaye gwanin sha'awa, hannunshi yake kokarin dorawa tasa bakinta ta kafa masa wani mugun cizo. Da sauri ya saketa yana yarfe hannu, ita kuwa mikewa tayi zata bar dakin yasa kafa ya tade kafarta kamar an wurgata ta bugi kofar dakin akwai wata b'ula a jikin kofar, ta saitinta ta fada karfen jiki ya yanketa a goshinta ta zube a kasa jini yana kwararowa taa fuskarta. Rarrafowa yayi ya karaso inda take yana dariyar keta, Hibbah kuwa bayan ta fadi karfen da suke tare kofa take laluba da hunnunta, cikin sa'a kuwa tajishi. Janyoshi ta rikayi a hankali, shi kuwa sale tuni yayi mata rumfa yana sumbatarta ta ko ina. Janyo karfen tayi tare da dagoshi ta kwada mai a keyarsa. Dagata yai yayi gefe yana layi ya fada gasa yana ta juyi. Ita kuwa jin ya dagata ta samu da kyar ta mike tana dafa bango ta bude kofar tare da fita itama cikin layi ta fito daga dakin KO gabanta bata gani ji tayi ta bugi mutum, jirin da yake dibanta yasa tayin

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});