Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ina k'iyayyar da ta huce wannan ina zata kai k'ararsa ne don a k'watar mata 'yancinta. Faruq ya shigo ya rufe k'ofar yana kallon ta, sai yaji wani haushin kansa kai zuciya bata yi ba, sai ta ingiza ka kayi abinda zaka zo kana shiga damuwa, sam baiji dad'in kalaman Hibbah ba duk ta rikitashi har yaji ya tsani kansa. "Hibbah" ya sunkuyo kanta, wani d'an tsaki yayi kukanta take yi, "oh my God! Wai Hibbah ya za muyi da juna?" Ya tsugunna nan ya d'ago kanta, fuskarta sharkaf da hawaye, ya maida kan nata kan filo tare da kifa nasa shima, "ni dai babu yadda zanyi da k'aunarki Hibbah tunda kince kin tsane ni to ko guba ce ki bani nasha na mutu na huta da wannan azabar sonki Hibbah, wallahi zan iya yi miki kuka a yau don ki tabbatar da ina k'aunarki ba tsanarki nayi ba, ki sani ni gwarzon namiji ne babu abinda zai iya sani kuka amma saboda ke nace zan iyayi haba masoyiyata Hibbah" zunbur ta matsa daga inda yake ta koma can k'ashen gadon "zo na rareasheki Hibbah baki san yadda nake ji a zuciyar nan tawa ba." "Allah yayi min tsari dakai shad'anin mutum irin ka, kai ba masoyina bane babban mak'iyi nane Wanda yak'i jini na, burinka nayi kuka raina ya b'aci na rasa kwanciyar hankali, shikenan farin cikinka me na tare maka?" Ya daki pillow'n da hannunsa yana huci idanunsa sun kad'a, cikin wata irin murya yace "ni ne shad'anin mutum zan tabbatar miki da hakan yanzu." Yayi wata zabura zai rik'ota ta tashi da gudu tayi hanyar fita yayi saurin cafkota, jikinta ya d'auki rawa badon ya rik'ota ba da tabbas zata iya fad'uwa saboda tsabar tsoro da fargabar mai zai faru, ya tsura mata idanu yadda yake ji a zuciyarsa yasan Hibbah ta kaishi k'arshe, so jarraba ne baya jin zai iya yi mata komai amma badon haka ba da yau saiya nuna mata shad'ancinsa. Yayi murmushi "Hibbah ina sonki da yawa furucinki ya fusata ni, fushina akwai wahala don bani da dad'i komai aka yi min saina rama, haka nake sai dai idan ni nayi niyyar yafiya ke kad'aice mace ta farko data sauya akalar ra'ayi na, kin ganni kamar tab'ab'b'e dubeni" saita bi umarninsa, don a cikin tsoro take, suka k'urawa juna ido. Sai yayi dariya ya ja hannunta suka koma parlor suka zauna ya shiga goge mata hawayenta "kin yave min? Wallahi nayi miki alkawarin bazan kuma b'ata miki rai ba, sai dai idan abisa kuskure na aikata, yanzu me kike son nayi miki?" Ta dube shi a nutse "Dan Allah karka sake kulani bare ka shiga harkata shikenan abinda nake son kayi min, kabar rayuwata ta huta abinda kayi min na yafe," "kina nufin baza ki aure ni ba?" Dam gabanta yayi wata mummunar fad'uwa zuciyarta ta shiga bugawa wai shi da gaske yake? "Aure fa kace Faruq kasan mene ma'anar aure? Taya aure zai k'ullu tsakanin mak'iya biyu? Ni fa abokiyar gaba ka d'auke ni, wace irin rayuwa zamuyi bayan nasan halayenka babu abinda ya sauya, ka kaga wuyanka sarka ce, kana nan akan batunka nason b'ata min *RAYUWA* saboda bani da galihu Allah ne gata ne." Ga mamakinta sark'ar ya tsinke ya jefar "wallahi tunda bakya so daga yau nayi miki alk'wari na daina sakawa, bazan iya daina sonki ba Hibbah sonki zai iya kashe ni, ni ban iya son abu ba idan ina son abu ina sonshi ne da dukkan gaskiya ta ko da zan rasa raina, Hibbah da kin aure ni zan zubda duk wasu d'abi'u na da bakya so zan daina su" "to kai baka la'akari da matsayina ne da naka, ka manta ni 'yar aiki ce a gidan Ku, ka duba matsayinka na d'an masu kud'i ni kuma ba 'yar kowan kowa ba, ka shahara da farin jini a football ga farin jinin mata. Kaga wannan Jabeer d'in shine ya dace dani shine mai min soyayya tsakani da Allah, a gabandmsa ka tozartani da bayyana masa matsayina na 'yar aiki a gidanku, amma hakan bai hanashi k'aunata ba kuma idan Allah bai wulakanta ka ba babu mai tozartaka a duniya, a cewarsa koda yawo nake ina tsinyar abinda zanci, zai aure ni ballantana don ina aikatau a gidan ku ai ba sata nake ba ba maita ba, shine yasan darajata yake sona don Allah," idanunsa sun kusan rufewq saboda tsabar b'acin rai "kinsan yadda nake jin zafin maganganunki nan gara ki caka min wuka mai dafi, Hibbah ina ta fahimtar dake irin son da nake miki kin kasa fahimta ki daina tunanin matsayinki wai waye waye ni zan samu Ya Faheem na fad'a masa," ta waro ido waje "Daddy'n Nawaz ma fa yasan da batun Jabeer ya zanyi dashi kayi hakuri kawai," ya d'ora hannunta a kan k'irjinsa "Hibbah kiji yadda zuciyata bugawa idan kina min zancen wani zata iya bugawa ki kashe ni ki huta." Ta zame hannunta "ni dai ka daina tab'ani ban so" "saboda ni kuturu ne ko, idan ban tab'aki ba wa kike son na tab'a kawai ki yi hakuri da halina duk abinda kike tunani yanzu kin huce haka a wajena, idan kuma nayi niyyar kusantarki sau nawa ina ritsaki a d'aki, kawai ni so nake kafin na tafi Germany a d'aura auren mu," ta tsorata da kalamansa ita gani take kamar Faruq baya hayyacinsa, ta tashi ya rigata yana dariya "nasan kina sona gulmace irin taku ta mata kina so kina kaiwa kasuwa, da munyi aure zan bud'e miki idanu na koya miki yadda zaki soni har ma kiji idan baki ganni ba na d'an wani lokaci ki kasa sukuni, dama wand'annan idanun na kuka ne abu kada'an kiyi ta kuka." Tayi murmushi "kaji dashi dai ni aiki na zanje nayi," "muje na tayaki kinsan ni bana barin macen da nake so cikin damuwa ko yaya take shiyasa nake miki naci zaki ji dad'in rayuwarki dani" ta girgiza Kai "a'a na gode ka tafi kar Daddy'n Nawaz ya dawo" ya tab'e baki gami da yarfar da hannu "to meye a ciki, zan fad'a masa ma aurenki zanyi ai yasan komai tunda yana gani na tare da ke, kawai dai yana sharewa ne, ni bani number ki bazan iya barci ba sai naji muryarki" ta tsaya kawai tana kallonsa wai ita Faruq yake furtawa Kalmar so anya wannan ba salon yaudara bane, idan tayi la'akari da kalamansa na wannan jikin mallakinsa ne, jikinta kawai yake so ko da zai aureta daya gama cin muriyar jikinta zai yada ita ya koma har kokinsa da mata. "Magana nake miki kin wani tsare ni da wannan idanun naki masu saukarwa da mutum kasala, idan kina kallona tsumani kike yi ina ji ina k'ara sonki, idan kika cigaba da kallona kema kinsan abinda zai faru," tayi dariya "Kai fitina ne da kai na gaji da fad'a maka bazan iya ba" "gara ma tun wuri ki sama mana mafita don karshen watan nan nake so a d'aura aure idan ba haka ba za'a haifi d'an da ba ido" ta shige d'aki ya bita da kallo gaskiya yarinyar nan ta tafi dashi da yawa, ga manyan babies nan a gari amma duk basu burgeshi ba sai Hibbah. Ita kuwa

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});