Chapter 25
Chapter 25
ya isheta tasan halin Faheem sarai yanxu zai dizgata a gaban yarinyar nan, ta suri jakarta tana ta mita ta shiga ciki. Faheem ko kallonta baiyi ba ya cigaba da kallon news, Nawaz ya kalli daddyn shi yace "daddy ni yau a wajen aunty zan kwana," Faheem ya kalleshi "a'a Nawaz zakaje ka takurawa Hibbah ne da surutu ne kawai," "daddy bazan yi mata surutu ba," "to shikenan kaje ka canza kayan naka sai kaje Ku kwanta," Nawaz ya tashi yana murna yaje ya canza kayanshi ya tafi d'akin Hibbah, ya shiga da sallama waya yaga tanayi tace "aunty kiyi hakuri zanzo amma ba yanzu ba, saina daina xuwa islamiyya tukunna," daga can aunty tace "yaushe ne zakuyi walimar ne Hibbah?" "Next week Sunday," Hibbah ta hawa aunty amsa, "to Allah ya kaimu," "ameen Aunty," Nawaz ya matso kusa da ita "aunty bani mu gaisa da momy Aysha,," Hibbah ta mik'a masa wayar suka gaisa da aunty sannan sukayi sallama ta kashe wayar. Ta kalli Nawaz tace "Nawaz daddy ne yake Kira na?" Ya girgiza kai "a'a aunty nazo mu kwana tare ne," "ok to zo muyi alwala sai mu kwanta," suka mik'e suka d'auro alwala suka yi addu'a tare da kwanciya. Da safe Hibbah ta tashi tayi duk wani aikin gidan sannan tayi wanka tayiwa Nawaz ta shiryashi sukayi breakfast ta wanke cups d'in, da rana ma haka tayi musu girki hakama da dare. Haka Hibbah ta cigaba da yi musu bauta a gidan amma Kausar bata tab'a yi mata koda kallon aizik'i ba balle ta samu godiya daga wajenta. Da haka har ranar walimar su Hibbah tazo, aunty da umma sunyi bajinta kwarai don duk wani abu da akewa 'yar gata da walimarta haka sukayi wa Hibbah ta fito kamar ba ita ba, haka taro ya tashi aka sallami 'yan sauka aka basu allon su tare da kyaututtuka. *** Watan Hibbah d'aya agidan har ta Saba sosai kullum sai tayi komai na gidan take tafiya school, daddy kuwa Nawaz yake aikowa ya kai mata kud'in motarta. Ranar lahadi Faheem yana gida da wuri Hibbah ta gama komai ta kira Nawaz tace "Nawaz jeka fad'awa daddy zamuje gidan Aunty," Nawaz yace "nima zani gidan momy Aysha," tace "to jeka fad'awa daddy kazo mu tafi," ya juya cikin happy ya tafi wajen daddyn nashi dake harabar gidan yaje yace "daddy wai inji Aunty Hibbah zamuje gidan momy Aysha," Faheem yaji dad'in yarda Hibbah ta bashi girmansa ya zaro kud'i a aljihunsa ya mik'awa Nawaz "ka kaimata Ku hau mota kuce ina gaishe da Aysha," Nawaz ya amsa ya kawo wa Hibbah kud'in. Hibbah ta shirya cikin wata atampa yellow da ratsin royal blue tayi kyau sosai ta shirya Nawaz suka fito titi Neman adaidaita. Da k'yar suka samu suka nufi gidan Aunty. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHS ALIYU GARKUWA* Sun isa gidan aunty inda ta tarbe su cikin farin ciki suka rumgume juna suka zube kan kujera suna gaisawa, Aunty ta cika musu gaba da abinci kala kala sunaci suna ta hira har lokacin sallah yayi suka tashi suka gabatar da sallar. Ba wani aiki auntyn take yi ba a gidan daga gyaran d'akin mijinta sai girki don haka suka kuma zama a parlor suna ta hira, sallamar su sagir ce ta katsesu suka amsa musu, Hibbah ta gaishe da sagir dana bayan shi dan bata ga fuskarsa ba. Jabeer ya saki sassanyar ajiyar zuciya tare da amsawa muryarshi data jini ne ta gane wanene ta d'ago kanta duka kalli juna, Jabeer ya sakar mata wani murmushi mai cike da ma'anoni. Ta kawar da kanta kefe suka cigaba da hira da aunty ita kuwa aunty ta fahimci abinda ke tsakaninsu, ta taya Hibbah murna sosai ta kuma yi farin ciki da hakan ta mik'e ta nufi d'akin mijinta ta had'a masa ruwan wanka tare da fito masa da kaya marar nauyi, shima sagir biyota yayi donya watsa ruwa. Parlor'n ya rage daga Jabeer sai Hibbah sai kuma Nawaz daya ke ta wasanshi jikinta, Jabeer ya kalleta yana murmushi "Hibbah ba magana," ta sunkui da kai "ai na gaishe da ku," "Hibbah gaisuwa daban maganar da bake so kiyimi da ban," ta d'ago tad'an kalleshi ta mayar da kanta k'asa don bata da amsar bashi, gani take yi kamar zai yaudareta tana yiwa maza kallon halinsu d'aya shima hankali zai buk'aci jikinta. Ta kuma yin k'asa da kanta yace "Hibbah ki yarda dani wallahi inna k'aunarki kuma ni auranki zanyi pls ki karb'i buk'atata," Hibbah dai bata ce komai ba sai wasa da take yi da zuben hannunta, Jabeer yayi suru kawai yana kallonta, ita kuwa Hibbah duk a takure take dan bata son yawan kallo yana takureta. Aunty ta dawo parlor'n tana dawowa Hibbah tace "aunty bara mu tafi yamma tayi," aunty ta harareta "me kike nufi? Wai yanxu zaki tafi?" Hibbah ta d'an karyar da kai "aunty daddy fa yana nan kinga bazai so kukai dare ba, ga girki ma da zanyi yanzu idan na koma," aunty tayi murmushi "to shikenan na karb'i uzurinki," Hibbah ta d'auki jakarta Nawaz ma ya mik'e "aunty zamu huce sai munyi waya," "to shikenan Hibbah na gode ki gaida min da Yaya," Jabeer yayi zaraf "Aysha mai zai hana na kaita tunda da mota a hannuna," da sauri Hibbah ta d'ago Kai ta kalleshi, aunty ta kalli yanayin Hibbah duk ta rud'e tace "ai kuwa da ka kyauta, kasan yanzu kafin ta samu mota ma aikine tunda yamma tayi," Hibbah ta kalle Aunty tayi narai narai da ido. Jabeer yaji dad'in furucin aunty jiki na rawa yafita, Aunty tayi murmushi tace "Hibbah Jabeer yana sonki so na hak'ik'a me yasa bazaki karb'i tayinsa? Kullum idan yazo gidannan Bashi da zance sai naki," Hibbah ta kalli Auntyn ta "aunty bana k'i karb'ar tayinsa bane kawai ni inajin tsoran maza ne," "a'a Hibbah ba duka aka taru aka zama d'aya ba, kinga yanzu yana jiranki a mota, kaso mai sonka kinga shi aurenki zaiyi da kin k'arasa school amma dai kiyi tunani." Hibbah tace "to shikenan aunty na gode," aunty ta bata wata leda bak'a cike da kayan kwalliya ta amsa tayi godiya. Aunty ta rakota har bakin motar ta bud'e mata kusa da Jabeer ta shiga suka tafi, a mota Jabeer sai janta yake da hira ita dai ba magana daga uhmm sai a'a, dayaga haka sai yayi ta jan Nawaz da hira har suka shigo unguwar nan ne ma dai tayi ta nuna masa hanya. A bakin gate d'in gidan yayi parking Hibbah kanta na k'asa tace "na gode," Nawaz ya bud'e motar ya fita da gudu ya shiga gida. Jabeer ya kalleta yace "Hibbah maganar mu fa?" "Sai na fad'awa aunty," ya kalleta "nasan Aysha zata bani da yardar Allah," "Allah yasa," ji sukayi an bud'e k'ofar ya janyoh hannun Hibbah tare da sinka mata mari "uban me kikeyi a motarsa?" Hibbah ta d'ago kai ta kalleshi, cikin tsoro ta furta " *Faruq* kaine yaushe ka dawo?" "Bansani ba, me kikeyi a motarsa nake tambayarki," Jabeer cikin zafin yace "kai dallah ya isheka kawai daga ganin yarinya muna tare sai ka shiga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63