Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kan abinda ya kawoni, ke uwa ce a gurina ya zamemin dole nayi miki biyayya," Aunty ma furucin Hibbah yasata farinciki, ta janyo Hibbah ta rumgume ta da d'an wani lokaci kafin suyi sallama aunty ta tafi don itama tana d lectures. Principal da kanshi ya kai Hibbah class lokacin da suka je da malami acikin class d'in dan saida malamin ya dakata principal ya gabatarwa da students ita as a new comer, ya mik'a amanarta a hannun class rep mace kuma yayi mata mazauni a kusa da class rep din. Ta maida hankalinta ga malamin suka cika cigaba da d'aukar darasi, sai bayan ya fita class rep d'in ta mik'awa Hibbah hannu cikin harshen turanci tace "barkanki da zuwa bak'uwar mu ni sunana Fauziyya Usman Aliyu zaki iya kirana da fauzy," ita ma Hibbah ta mik'a mata hunn cikin harshen turanci tace "naji dad'in had'uwa dake ni kuma sunana Hibbah Mukhtar Muhammad, fatan zaki rik'e ni amana kamar yadda nima Zan rik'e ki" fauzy ta girgiza kai tace "sunanki na da dad'i kuma zan rik'e amana insha allah," Hibbah tace "na gode kema sunanki yayi dad'i," da haka sukayi ta hira sauran students suka zo suna yi Mata sannu da zuwa da haka wani malamin ya shigo. Haka Hibbah ta cigaba da zuwa makaranta tana fahimtar abubuwan da ake koya mata, Wanda ya shige mata duhu bata fahimta ba takan tambayi malamai ko fauzy, idan a gida ne kuma sai ta tambayi Auntyn ta idan bata nan ta tambayi Saudat bata tambayar Safiyya saboda babu fuskar tambayar. A haka har su Hibbah suka k'are zango karatu na farko tare da fito da result d'in data bawa kowa mamaki, ta d'auki 5th position a class. Aunty tayi murna sosai da result d'in hakan ya kuma bawa Hibbah k'arfin gwaiwa tare da d'aura d'amarar cigaba da farantawa Auntyn tata, satinsu d'aya dayin hutu Abba ya turo a ka d'auki su Safiyya, gidan sai ya koma shiru gashi Hadiza itama ta tafi ganin gida, sai gidan ya zama daga Hibbah sai momy sai kuma 'yan aiki shiyasa Sam Hibbah bata jin dad'in gidan sai dai idan aunty ta dawo. Ganin yarda Hibbah take takura yasa Aunty ta nemi shawarar momy akan sukai Hibbah gidan kawunta inda ummanta take tayi hutu a can. Ranar asabar da daddare Aunty suna zaune da Hibbah a d'akinta, dayake Hibbah ta koma d'akin Auntyn tun sanda Hadiza ta tafi ganin gida, aunty ta kalli Hibbah tace "Hibbah ni kuwa akwai wata shawara da muka yanke ni da momy ban Sani ba ko zaki bamu had'in Kai," Hibbah da take duba wani littafin makarantarta ta kalli Aunty tace " Aunty bani da bakin yin jayayya daku duk abinda kukayi a kaina dai dai ne, nasan bazaku tab'ayin abinda zai cuceni ba," aunty taji dad'in furucin Hibbah tace "Hibbah kalamanki da sanin ya kamatanki sune suke kuma dasa k'aunarki a zuciya ta, dama shawarar da muka yanke da momy cewa mukayi tunda gidan nan ya zama ba kowa sai ke kad'ai kuma kema bajin dad'in zaman kike yi ba, shine nace ko zamu kaiki gidan kawunki can wajen ummanki ki k'arasa hutun a can." Da sauri Hibbah ta d'ago kanta tana kallon Aunty sai kuma ga hawaye tace "aunty ina tsoron zuwa wallahi nasan halin inna lami zata iya kasheni, dan allah ki barni a nan d'in," Aunty ta janyota jikinta tace "ki kwantar da hankalinki Hibbah ai Umma da inna lami kince min ba k'auyensu d'aya ba kuma mu iya kacinmu k'auyen da Umma take kawai zamuje," Hibbah ta goge hawayenta "aunty na gode allah ya k'ara d'aukaka, ni dama inna lami nake jin tsoro amma nima inason naga ummana," aunty tayi dariya tace "Hibbah na kin cika tsoro da yawa, ki shirya gobe da safe zamuje don bani da lectures goben," Hibbah ta kuma ruk'unk'ume Auntyn tace "na gode Auntyna allah ya k'ara d'aukaka ya barki da Uncle d'ina," ta fad'a tana tusa kanta jikin Auntyn nata wai kunya taji. Auntyn tayi murmushi tace "ameen Hibbah, tashi mu had'a kayan tafiya." Mik'ewa sukayi suka shiga had'a kayan. Washe gari k'arfe tara na safe suka d'auki hanyar Bunkure cike da tsaraba, Hibbah tana nunnunawa driver hanya har suka isa gidan, driver yayi parking a k'ofar gidan suka fito. Da sallama suka shiga inna (babar Abu) tana iza wuta a bakin murhu ta k'araso kusa dasu tana yi musu sannun, ta shinfid'a musu tabarma suka zauna ta d'ebo musu ruwa Aunty tana gaisheta ita sam bata gane Hibbah ba saida ta gaida ta da taji muryarta sannan ta ganeta ido ta zuba mata tare da rik'e hab'a cikin mamaki tace "Hibbah kece haka? Ai ni Sam bangane ki ba lallai birni ta karb'eki kinga yarda kika koma tubarakallah kinyi kyau," Hibbah ta rufe fuskarta da mayafinta, ita kuwa Aunty murmushi tayi, inna ta d'ora da cewa "ai a wajen malam (mahaifin Abu) nake jin wai lami ta turaki birni aikatau kuma ta horeki karki kuskura kizo ganin gida, bayan sharrin da tayiwa Aysha kema tayi miko saida ta rabaki da 'yan uwanki, Kai wannan Mata allah ya rabamu da sharrinta." Aunty tace "Amen, inna dama munzo wajen ummanta ne na kawota zatayi hutu anan, tunda can an hanata zuwa." Inna tayi murmushi tace "allah sarki Hibbah kinyi dacen iyayen gida, amma fa saidai kunyi rashin sa'a don ummanta tana gama allah ya kawo mata wani Alhaji a birni, ubangidan malam yace yana sonta aka d'aura musu aure bayan bincike da malam yayi ya tafi da ita birni," Hibbah ta d'ago da sauri ta kalli inna ta kalli aunty. Aunty ta d'an gyara zama tana kallon inna tace "inna a birni wane gari suke?" "Ai a nan garin kano suke da zama," inna ta bawa Aunty amsa, aunty tace "wace unguwa a birnin," inna ta d'anyi shiru kamar mai tunani can tace "wallahi 'yar nan na manta sunan unguwar amma da sa'idu zaizo daya fad'a muku sunan unguwar don jiya ma yaje ya kai mata sak'o," Hibbah tace "inna zai jima ne bai dawo ba?" Girgiza kai inna tayi tace "a'a don naga bai d'auki kayan aikinsa ba, yanxu zaki Ganshi ya shigo, bara na k'arasa iza wutar can," ta fad'a tana tashi, shiru sukayi can saiga sallamar sa'idu kallon su Hibbah yayi alamar rashin sani ta gaida Aunty, Hibbah ta gaishe shi itama saida tayi magana ya ganeta nan, inna ta k'araso tana cewa "yauwa sa'idu dama Hibbah ce tazo take son ka rakata gidan ummanta idan baka komai," sa'idu yace "ba matsala dama baba ya aikeni kasuwar su muje kawai," aunty tace "a wace unguwa take a kano d'in?" Sa'idu yace "a wai goran dutse," "ok" aunty ta fad'a tare da mik'ewa Hibbah ma ta mik'e, nan dai suka yiwa inna sallama aunty ta zube mata kud'i tayi ta godiya suka tafi. Garin kano suka koma, unguwar goran dutse suka nufa sa'idu yana yiwa driver kwance har suka isa gidan, kallon gidan Aunty tayi da mamaki ta kalli driver tace "Adamu wannan ba gidan Alhaji Sani bane?" Adamu driver yace "eh shine hajiya.............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});