Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

miki rahma" Baba kuwa ya kasa magana su momy kuwa al'ajabin abin ya hanasu magana sai fatan allah ya bata lafiya suke. Haka dai suka d'auko hanyar garin kano bayan an kai delu gidanta na gaskiya, inna lami kuwa acen suka barta a gidan cikin hauka don baba cewa yayi baza su tafi da ita ba da Abba ya buk'aci su tawo da ita saisu kaita gidan mahaukata amma fafur baba yace aa a barta abinda ta shuka take girba. Sun dai tawo da Rahmatu da take ta kuka tana yiwa mahaifiyarta fatan samun lafiya don hannunka baya rub'ewa ka yanke ka yar. Haka suka iso garin kano direct gidan Daddy dake rijiyar zaki suka huce anan suka yada zango, bayan sunyi wanka suka ci abinci aka zauna zaman hutu. Ba jimawa Umma tace ita zata huce gidan mijinta, baba yayi mamaki don shi a tunaninsa Umma bata yi aure ba yana shirin mai data d'akinta sai kuma yaji ashe tana da aure, sai kawai ya kawar da tunanin yana addu'ar Allah ya zab'a masa wadda tafi alkhari. Daddare duk suka watse Aunty ta koma gidan mijinta da tace da Hibbah zata tafi momy tace a'a ta barta anan tayi zamanta. Kausar ma Faheem d'aukarta yayi suka huce yaso ya d'auki Amaryarsa Hibbah amma Daddy ya hana haka badon yaso ba suka tafi shi da Kausar suka bar mata Nawaz a wajenta don cewa yayi shi a wajen Aunty Hibbah zai zauna. Rahmatu kuwa da gwaggo sunsha gata da tarairaya gata iri iri. A daren Rahmatu ta haifi 'yarta mace amma 'yar bata zo da rai ba. Tun dawowar su daga k'auye aka shiga shirye shiryen bikin *Hibbah* da *Faheem* sosau su momy suka shiga kintsa Hibbah da sabulai maya mayai na gyaran jiki Dana sa laushin fata ga turaruka kamar Ana b'arin turare a jikinta ko hucewa tayi ta kusa da kai sai k'amshin ya jima bai baje ba, ga wasu had'i da ake bata kamar me har su Saudat ma sha suke yi don suma an tsaida maganar aurensu, Saudat kuwa sun daidaita da Usman d'an Abba ita kuwa Safiyya wani saurayinta ne Yusif. Faheem kuwa duk ya k'osa a kawo masa matarsa baya iya jure rashin ganinta a kusa dashi shiyasa kullum yana hanyar zuwa gidansu don ganin abar k'aunarsa. Momy da mamy har gwaggo sun gane take takensa shiyasa suka kuma d'aura d'amarar gyara Hibbah. Su Aunty ma sun fito da anko kala biyar wai bikin 'yar gata za'a yiwa Hibbah, mamy ce ta had'o mata lefe na gani na fad'a........ *#Juma'at mufeedah to you all my fans😍❀🀝* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page 5⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```wattpad@mamyn_najmah2222``` *wannan page d'in d'ungurin gum na sadaukar dashi gareku masoyan littafin RAYUWA ina son Ku ina jinku a zuciya ta, Kuyi hakuri bakwa jina kwana biyu wallahi bana samun time ne.* Daddy ya baiwa baba duk wata dukiyarsa da take wajensa da da farko baba yak'i karb'a yace ya barsu ya cigaba da juyawa amma daddy yace ina kawai ya amsa, haka badon baba yaso ba ya amsa. Part d'in da Faheem ya zauna nan daddy ya mayar na baba. Kwanansu uku da dawowa daga k'auye, suna zaune kamar kullum don tunda suka dawo kullum da yamma zasu zauna a parlor ko a garden suyi ta hira, mai gadi ne ya shigo da hanzari yayi musu sallama suka amsa yace "Alhaji dama wani ne ya bada sako a kawo maka" ya mikawa daddy takardar dake hannunsa yace "kuma yace don Allah idan yanzu kana gida idan ka karanta sakon dake ciki ka hanzarta zuwa asibitin" daddy ya kad'a kai "to shikenan zaka iya tafiya" mai gadin ya juya ya koma bakin aikinsa. Daddy yana rike da takarda yana zulumin abinda zai gani a cikinta yana tunanin to daga k'ark'ashinwa wannan takardar tazo sannan waye a asibiti? Su Abba da sauran mutanen dake zaune kuwa kowa da abinda ke cikin ransa tunda sukaji an ambaci asibiti. Da k'yar daddy ya iya bud'e takardar ya karanta sak'on da ya gani ya d'aga masa hankali ya d'ago ya dubi su baba da duk shi suke kallo yana furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un yace "Ku tashi mu tafi asibitin murtala" a gigice suke kallonsa waye ba lafiya baba yace "waye bashi da lafiya" Daddy da har ya kai kofar fita yace "kuyi hakuri ba lokacin bayani Ku tawo kawai mu tafi" haka su momy suka d'augo hijjabansu suka fito, motoci suka shiga kai tsaye asibitin murtala Muhammad suka nufa, bayan sun gama parking suka nufi cikin asibitin d'akin da aka yiwa Daddy kwatance suka nufa Daddy ne yake jagorantarsu har suka isa d'akin. Da sallama suka shiga yarinyar da take jinyar tashi ta amsa masa, Wanda baba ya gani yana jinyar ne ya sashi karasawa kusa dashi cikin hanzari "Ibrahim Ibrahim me ya sameka garin ya wannan Abu ya faru?" Baba duk ya rude sai tambayoyi yake masa. Su momy kuwa sai sannu suke masa, Alhaji Ibrahim dake kwance a gadon na asibiti ya rame yayi bak'i kasusuwansa duk sun bayyana kamar mai cutar Ebola ga hannunsa d'aya babu k'afa ma babu guda d'aya bakinsa kuma ya karkace ya rik'o hannun baba "Mukhtar ka yafe min kaji k'aina nayi nadamar yadda na rusa amincin mu ta hanyar cin amanarka, wallahi nayi dana sanin san duniya irin nawa" ya ja numfashi da k'yar baba ya kuma k'amk'ame hannun nasa "Mukhtar kaga k'arshena ko? Kaga k'arshen zab'ar duniya akan lahira da nayi ko? Kaga illar cin amana ko? Sannan ga uwa uba shirka da nayi da ubangijinmu, Mukhtar duk wani hali da ka shiga a baya wallahi nine sila ni nayi maka sammun da aka zautar maka da tunani ni nasa a lalata maka k'wak'walwa, kaga k'arshena ko Mukhtar kowa ya gujeni hatta 'ya'ya sun gujeni matata ma haka wannan yarinyar nurse ce ita kad'ai ce take jinyata don Allah ka yafe min wallahi nayi nadama....." Ya karasa maganar hawaye na bin fuskarsa sannan ya soma wani irin tari kamar zai amayar da hanjinsa. Allah sarki baba shi duk tausayinsa yake ji sashen zuciyarsa kuwa na mamaki irin wannan san zuciya na mutane ashe har Ibrahim zai iya yi masa wannan rashin imanin? Da sauri ya girgiza kai nima ina da lefi da ina bawa kaina kariya da Neman tsari wajen ubagiji da bazaiyi tasiri a kaina ba, baba ya kuma rik'e hannun Ibrahim yace "na yafe maka Ibrahim Allah ya yafe mana" murmushin k'arfin halin Ibrahim d'in yayi bayan ya tsagaita tarin ya dubi su Abba dasu momy da su Hibbah masu arhar hawaye har amfara ambaliyarsa yace "don Allah Ku yafe min" daddy ya dube shi "ba komai ni na yafe maka Ibrahim Allah yana son masu yafiya" suma su momy su Aunty duk sukace sun yafe masa. Sai kuma ya dinga wani tari sosai ba k'ak'k'autawa har numfashinsa na d'aukewa, yarinyar dake jinyarsa ta fita da sauri don kira doctor shi kuwa baba dake kusa dashi sai maimaita masa Kalmar shahada yake amma ina ya kasa kamawa a haka har numfashinsa ya d'auke gaba d'aya (to dama Wanda yayi shirka ina zai cika da Kalmar

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});