Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baya, cikin sauri Abu ta rikota tana tambayarta lafiya? Kokarin k'wace jikinta take yi tana nuna mata cikin dakin, kuma riketa Abu tayi tace "mene Hibbah? Kiyi min magana mene a dakin." Cikin rudu tace " na kashe shi yana ciki ya mutu." Sai kuma ta fashe da kuka ta rike hannun Abu sosai tana cigaba da kuka. Kallon goshinta Abu tayi inda ta yanke tadan waro ido tace "Hibbah meya sameki a goshi? Kuma waye ya mutu?" Bata amsa ba ta cigaba da kuka tana cewa "Abu ya mutu wallahi bada niyya na kashe shi ba." Abu ta kasa fahimtar waye ya mutu, kawai taja hannun Hibbah zuwa cikin dakin, K'ara Hibbah tasa tana cewa "wallahi idan naje dakin nan fyade zaiyi min, Abu kashe ni zaiyi ki kyale ni?." Ta kuma fashewa da kuka tana ciccijewa. Tsayawa Abu tayi da janta tace "ki nutsu Hibbah kiyi min bayanin komi," Abu ta fada cikin kwantar da murya. Shiru Hibbah tayi ta kasa magana, kallon ta Abu take yi tace "Hibbah ki fada min mana musan abinyi kafin Inna lami tazo." Jin an ambaci Inna lami yasa ta fara bawa Abu labarin abinda ya faru. Mamaki ne ya bayyana karara a fuskar Abu tace "fyade? Zai ai kata indai sale ne, Ai dama tun da naga yarda yake miki a kasuwa nasan akwai abinda yake nema" ta danyi shiru sannan taja hannun Hibbah tana cewa "ki nutsu Hibbah, mu shiga dakin muh gani idan yana motsi sai musan matakin dauka. Idan kuma ya mutu musan nayi," cikin tsoro Hibbah tabi bayanta suka shiga dakin. Sale suka gani a baje a dakin yana ta mutsu mutsu jini duk ya b'ata dakin. Kara sowa sukayi cikin dakin kallon shi Abu tayi taga yana motsi ta kalli Hibbah tace "ki kwantar da hankalinki Hibbah bai mutu ba yana motsi" Hibbah dai har yanxu hankalinta bai kwanta ba tace "to Abu kice ya fita daga dakin nan, kinsan idan Inna lami tasan yana dakin nan na shiga uku dukana.........." Katseta sale yayi cikin muryar data ji jiki yace "wallahi baxan fita ba idan har kinga na fita daga dakinnan to na samu abinda nazo nema." Ya mike zaune yana tallafe da keyarsa ya cigaba "Hibbah kisani bugamin karfen nan da kikayi shine *babban kuskuren da kika tafka* don kuwa kinsa naji dole na kusanceki kota halin k'ak'a." Dayake Hibbah tana daga bakin kofar dakin cikin tsiwa tace "aniyarka ta bika mugu kawai," murmushin yak'e sale yayi yace "wato kin samu bakin magana koh?" Murguda Mai baki tayi tare da jan tsaki tace "Abu yanxu mene abunyi kindai ji abinda ya fada koh?" Jan hannunta abu tayi suka fito daga dakin, bangaren su Inna lami suka nufa da sauri Hibbah ta kalli Abu tace "me kike shirin yine Abu?.'' Abu bata kalleta ba tace "ke dai ki biyo ni kiga me zanyi," "na biyoki Kamar ya? Ke kinsan halin Inna lami, babu yarda za'ayi mu fada mata wannan matsalar, memakon ta warware mana ita saidai ta kuma hargitsa abun." Tsayawa Hibbah tayi tana kallon Abu tace "allah Abu kije ke kadai nidai bazan jeba." Kallon ta Abu tayi tace "nifa ba fada mata zanyi ba kedai kizo muje" kuma gyara tsayuwa Hibbah tayi tace "wallahi kinji na rantse bazani ba". Jin ta rantse ya kuma tabbatarwa da Abu Hibbah bazata karasa inda take so suje ba. Shi kuwa sale ganin sun fita su biyun yadan ji tsoro karfa su Tara masa jama'a don yasan halin Abu tsaf zata aikata, cikin ransa yace _Anya kuwa bazan hakura da k'uduri na ba? Karfa nazo ayimin duka tunda kowa a kauyen nan yasan halin yarinyar nan_ mikewa yayi yana dafa bango. Su kuwa su Hibbah suna tsaye Abu sai magiya take mata amma ita tace tsoron abinda Inna lami zata mata take. Abu ganin Hibbah na bata musu time kar sale ya gudu yasa cikin ihu da daga murya yarda su Inna lami xasuji ta shiga cewa "wayyo allah kwarto jama'a kwarzo wayyo!" Saida ta fada sau uku ta tabbatar su Baba sunji sannan tayi hanyar waje tana ihun kwarto. Da gudu Hibbah tasha gabanta tana cewa "haba Abu wannan ai tonan asirine, kina so mutanen k'auyen nan Susan abinda ya faru Dani ne?" Kallon ta Abu tayi "to mene idan sun sani, naga dai kowa yasan halinki kuma kowa yasan waye sale, to don sun sani har wani abune?" Ta fada tana kaucewa daga inda Hibbah ta tsaya. Muryar Inna lami sukaji ta tawo da gudu rike da muciya tana cewa "ina kwarton yake?" Kallonta Abu tayi tad'dan nuna yanayin tsoro tare da nuna mata cikin dakin, da gudu Inna ta shiga dakin. Shi kuwa sale jin Abu na ihun kwarto yasa tsoro ya kuma dirar masa cikin tsoro ya xura kayansa ya nufi kofar fita cikin sauri. Kicib'is sukayi da Inna lami tana kokarin shigowa, baya yayi da sauri ya zaro ido waje ganinta da muciya. Murmushi tayi masa tace "ka kwantar da hankalinka na rik'e wannan muciyar ne kawai saboda tsaro, kaima kayi sakaci wai ya akai haka ta farune?" Kallon sale yake tsoro ya bayyana a fuskarsa b'uru b'uru yace "Zan miki bayani daga baya ni dai yanxu matsa na huce kinga yaran cen zasu tara min......." D'aga labulen da akayi ne ya katse masa magana, baba ne ya shigo yana kallonshi cikin tsana. Bayason baba yaga fuskarsa, Cikin zafin nama sale ya hankad'e Inna lami yabi ta gefen baba ya fita da gudu daga dakin, yana fita tsakar gida yaga su Abu da k'awayen su rik'e da sanduna, da wani mugun gudu ya gifta ta kusa dasu don karsu same shi amma duk da haka saida Abu da kharime suka kwad'a masa........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page1⃣2⃣to1⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *wannan page d'in naki ne ~sweety~ _SADNAF_ Allah ya kara basiraπŸ™* Cikin dare Hibbah ta farka saboda zazzabin dake nuk'urk'usarta ga kuma ciwon kai, tashi tayi daga kwanciyar datayi ta zauna tare da ruk'unk'ume jiki tana ta rawar dari hakk'oranta suna ta bugar juna. Kuka take yi a hankali Mara sauti. Cikin barci gwaggo taji gunjin kuka yana tashi a hankali, lalubar touch light dinta tayi ta kunna ta haska. Hango Hibbah tayi a zaune ta dukunkune tana kuka k'asa k'asa. Daga gadonta ta sauko ta k'araso kusa da Hibbah tace ''y'ar nan lafiya cikin tsakiyar dare ki tashi kina kuka?" Cikin muryar da bata fita sosai tace "gwaggo sanyi nake ji kaina kamar zai fashe, gwaggo sanyi sanyi nakeji," ta karasa maganar tana kuma k'amk'ame jikinta. Janyota jikinta gwaggo tayi taji yarda jikinta yayi zafi sosai tace "yi hakuri Hibbah bara na kawo miki ruwan raidore Dana tafasa dazu kisha insha allah zaki ji sauki kinji?" Kai kawai ta d'aga Mata. Zame jikinta gwaggo tayi daga na Hibbah a hankali ta tashi ta dauki touch light dinta ta fita tana haskawa, a bakin murhu ta bude wata tukunya ta tsiyayo ruwan a kwano ta rufe tukunyar ta dawo d'aki. Tana shiga d'akin ta k'arasa kusa da Hibbah D'agota tayi ta kafa mata a baki, bismillah ta fara sha, ba laifi tadan sha da yawa ta kauda kai. Gwaggo

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});