Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

to wata muguntar ta had'a. A hankali ta k'arasa cikin gidan da sallama babu Wanda ya amsa mata saima mugun kallon da innar ta bita dashi tare da cewa "kefa a taki k'aramar k'wak'walwar kinyi tunanin na dawo dake gidan nan ne KO?"ta Saki wata dariya suka tafa da delu ta cigaba"ni Neman kud'i zanyi dake don haka ki tashi kije ki had'o tsummokaranki kizo zaku tafi da delu." Da sauri Hibbah ta d'ago kanta tace "ina inna?" "Gidan ubanki nace gidan ubanki kujimin yarinya da rashin kunya dole sakinji KO ina ne, ki tashi ki hada kayanki nace, kuma wallahi saura idan ankaiki kice zaki zo ganin gida wallahi saina kasheki kinsan halina sarai Zan iya kasheki." Jikin Hibbah na rawa ta tashi ta shiga d'akinsu kayanta tashiga had'awa hawaye na sintiri a fuskarta cikin ranta take tunanin wannan *RAYUWA* tata a raba ka da mafiyarka da mahaifinka yanxu kuma zaa rabaka da danginka da kowa naka akaika can wani waje kayi *RAYUWA* ba tare da kasan kowaba acan. Wani hawayen ya kuma gangaro mata Ta share da bayan hannunta ta karasa had'a kayan nata da basu fi kala biyar ba duk dun kod'e ta k'ulle a d'an kwali ta fito, taje gaban inna ta tsugunna tace "inna na had'a kayan." Inna ta watsa mata harara "kindai ji abinda nace kika kuskura kika dawo k'auyen nan saina kashe ki wallahi tashi ku tafi," hawaye ne yake gangarowa daga idonta tasa hannu tana sharewa amma duk da haka bai daina zuba ba. Rank'washi inna ta Kai mata aka tace "kujimin da munafukar yarinya annamimiya uwarki nayi miki daza ki Sani a gaba kina yimin kuka? Uban me nayi miki? Daza ki daina arhar hawayenki ma daya fi miki don wallahi, kinji na rantse babu Wanda ya isa ya hanani kaiki aikatau birni, shegiya mai bak'in hali." Ta fad'a tana kuma kwad'eta. Kuka ta kuma Saki harda magina ta kalli inna delu wadda sai murmushi take kana gani kasan na mugunta ne tace "meye kike kallona da wad'annan mayun idanun naki mayya kawai, ni tashi dallah mu tafi kina b'ata min lokaci ina da wajen zuwa da yawa." Cikin shashshek'ar kuka Hibbah ta kallesu tace "inna dan Allah kuyi min hakuri ku barni a cikin 'yan uwana da dangina, karku rabani da mahaifata don Allah wallahi bana so.........." Wani wawan mari inna t Kai mata "don ubanki har kina da bakin magana, ki kalli tsabar idona kice wai na barki cikin danginki? Ina kike da dangin? Shegiyar yarinya zatayi min bak'in ciki tun wuri gara ki fidda ran zaki kuma *RAYUWA* cikin danginki har abada!" Sun kuyar dakai Hibbah tayi tana kuka sosai. Inna delu ta mike tace "keh! Tashi mu tafi," ta kalli aminiyar tata tace "to lami zamu huce sai kuma na kawo miki albashin nata kuma duk wani alheri da aka bata a gidan naki ne." Cikin happy lami take washe baki tace "to shikenan sai na jiki allah ya kiyaye hanya, ke kuma" ta nuna Hibbah "kindai ji abinda na fada miki kika kuskura kika dawo k'auyen nan kinji dai furucina tam," mikewa Hibbah tayi tana share hawayen dayake tayi Mata sintiri ta kalli katangar su Abu ta tuno nan ne kad'ai yanxu ya ragemata kuma gashi suma an rabata dasu, Dama a dangin babanta bata san kowa. Abu ta hango tana lek'o gidan, kallonta ta tsayayi kafin ta d'auki k'ullin kayanta tabi bayan inna delu. Har bakin zaure inna lami ta rako su suna shirin fita daga gidan saiga su Abu da gwaggo sun shigo. Gwaggo ta kalli Hibbah tace "ina kuma zaki da kaya haka?" Daga gefe inna lami tace "aikatau zan kaita birni saboda ni na maidata tamkar jari ne, Neman kud'i zata je tayi a dinga aikomin kuma na fad'a mata karta kuskura ta waiwayi k'ayen nan koda wasa eyyeh." Kallonta gwaggo tayi cikin mamaki tace "tabbas Abu maganarki ta tabbata, yanxu lami bakya gudun yarinyar nan ta fad'a mugun hannu ko kuma su gidan a ka kaita su koreta ina zata dosa wata Sani acan? Da zakice karta kuskura ta waiwayi mahaifarta?" Inna lami cikin rashin kula tace "oho ita ta sani ni KO karuwanci zatayi taje tayi nidai kawai ta kawo min kud'i. Ai ita 'yar kishiya jarice baka saurin illata ta nima sai yanxu naga kuskurena na korarta danayi jiya shiyasa nace Rahmatu ta kirata." Harara Abu ta bugawa lami tace "to wallahi babu inda zata saboda ba 'yarki bace shine zakice zaki wani turata aikatau, ai kema kina da 'ya macen ki turata mana." Cikin masifa inna tace "keh Abu ki shiga hankalinki ko wannan kakar taki bata isa ta hanani Kai Hibbah aikatau ba balle wata ke 'yar ciki dallah kauce min da gani." Gwaggo tace "ke Abu babu ruwanki Karna k'ara jin bakiki," ta kalli inna "lami don allah badon ni ba kiyi hakuri karki tura yarinyarnan aikatau, kodan gudun b'acin tarbiyyarta........." "Wallahi Zulai babu Wanda ya isa ya hanani aikata birni," cikin tsantsar masifa lami ta katse gwaggo. Ba Hibbah da Abu ba harta gwaggo tayi mamakin yarda inna ta fadi sunanta kai tsaye batare data sakaya ba. Da mamaki gwaggo tace "lami zulai kai tsaye ba sakayawa?" Da masifa tace "to ba sunanki bane koba sunanki Zulai ba?" Girgiza kai gwaggo tayi tace "lallai lami," Hibbah ce ta k'araso kusa da gwaggo tace "gwaggo kiyi hakuri nasan ni haka tawa k'addarar *RAYUWA*r take na karb'eta hannu bibbiyu, Zan tafi aikatau birni na bar dangina, gwaggo ki kwantar da hankalinki nasan kina tsoron kar tarbiyata ta lalace ne. Insha Allah babu abinda zai canzani kedai kiyi tayi min addu'a nima inanan Zan cigaba dayi." Gwaggo taji dad'in kalaman Hibbah sosai cikin dauriya tace "to shikenan Hibbah allah ya miki albarka," Hibbah tana kallon Abu tace "ameen gwaggo," lami tace "mukuma allah ya tsine mana koh?" Babu Wanda ya kulata, Hibbah tace "Abu zan tafi nasan ni daku mun rabu har abada kiyafe min 'yar uwata kinji." Abu batasan danda hawaye ya zubo Mata ba tace "baki yimin komi ba Hibbah ni ya kamata na nemi yafiyar ki," cikin shashshekar kuka Hibbah tace "nima bakimin komi ba Abu." Suka had'a Kai suna kuka lamarin dayasa gwaggo itama hawaye. Kallonsu inna lami da delu sukayi suka tabe baki delu tace "gaskiya lami lokaci na tafiya fa." Da zafin nama ta fincike Hibbah daga jikin Abu tace"dallah ki huce ku tafi." Haka Hibbah tana ji tana gani suka rabata da y'an uwanta, haka suka rabu da Abu kowacce na zubda k'alla tare da d'agawa juna hannu har suka bacewa idanunsu. Tashar babura sukaje saida suka hau babur ya kaisu tashar *Bunkure* sannan suka nemi motar garin Kano, cikin sa'a kuwa suka samu motar data rage saura mutum uku ta cika. Kwandostan ya nuna musu motar, wajen motar suka k'ara delu ta kalli Hibbah tace "dallah ni shiga muje," Hibbah bata tab'a hawa mota ba shiyasa batasan yarda ake hawa ba. Tsayawa kallon delu tayi tace "aya zan hau?" Wani mugun kallo ta bita dashi tare da bangajeta ta shiga motar. Tsayawa tayi taga yarda ta shiga sannan itama ta shiga duk a tsorace take, wani mutum aka samu shine cikon na ukun. Yana shiga driver yaxo ya tashi motar

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});