Chapter 11
Chapter 11
jin mota ta fara tafiya Hibbah gabonta ya tsananta fad'uwa kuka ya kuma taso mata kanta ta tusa a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka marar sauti, batasan sanda barci ya kwashe ta ba............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πππππππππ *RAYUWA* page1β£7β£to1β£8β£ *NA* *MAMYN NAJMAH* πππππππππ *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Sun iso garin kano ta dabo tunbin giwa koda me kazo anfika. A tashar unguwa uku motarsu ta yada zango, mutanan motar suna ta fitowa, delu dake kusa da Hibbah ta kalleta a wulakance cikin daga murya tace "ke! Tashi mu tafi!" Allah sarki Hibbah tana can duniyar bacci bata Masan tana yi ba, ita kuma delu ji take duk salon barin gidan datayi ne yasata yin banza da ita. Cije lebe tayi tare da Sakin wani murmushin mugunta, mayafinta ta yaye ta daidaici tsakiyar bayanta ta buga mata gwaiwar hannunta. Kamar a mafarki taji saukar wannan dukan tasaki wata gigitacciyar k'ara a firgice ta d'ago kanta har hawayen azaba ya fara bin fuskarta, gefenta ta kalla inda delu take tana kallon ta. Ruwan pure water mai sanyi dake hannun delu ta fetsa Mata a fuska tace "dallah malama tashi mu tafi kin wani zauna kina yiwa mutane bacci a waje," delu ta fad'a tana bin Hibbah da mugun kallo. Hibbah bata da bakin magana sai hawayenta data goge tabi bayan delu suka sauka daga motar. Fita sukayi daga tasha suka nufi bakin titi, Hibbah sai kalle kalle take yi garin ya burgeta sosai wani titi data gani a sama motoci nabin takai ne yafi tafiya da hankalinta. Delu ta tarar musu adaidaita ta fada masa ya kaisu unguwar Rijiyar zaki,yace to suka shiga gani tayi sun nufi wannan gadar saman ihu tasa tace "malam Dan allah karka bi damu tanan mutuwa zamuyi." Me a daidaita da dariya ta taso masa yace "yarinya ki kwantar da hankalinki ba mutuwa zakiyi ba yanxu zakiga mun sauka ai hakan ma wani cigaba ne," delu tace " ke ki nutsu kina cikamin kunne, Dan allah kaima malam rabu da wannan yarinyar bata da hankali kasan Dan kauyen mutum", ita Hibbah bata Masan sunayi ba don gaba daya ta gama tsorata ta k'ankame jikinta sosai ta rufe idanunta k'am jikinta sai rawa yake. Mai adaidaitan ne ya juyo ya kalleta yaga yarda ta takure, sai hakan ya kuma Bashi dariya cikin dariyar yace "y'ammata ki Saki jikinki mun huce wajen," ko kulashi batayi ba saima kuma k'ankame jikinta datayi. A kofar wani madaidaicin gida adaidaitan yayi parking jin da tayi adaidaitan ya tsaya shine ta samu damar bud'e idanunta ta fito daga ciki ta tsaya tana ta kallon unguwar, kud'in me adaidaita delu ta bashi sannan tayi gaba Hibbah nabinta a baya. K'ofar gidan suka k'arasa delu tar k'wank'wasa, wani dattijo ne ya lek'o yadan washe baki tare da bud'ewa yace "a'a delu kece tafe da rana haka?" Delu tadan yi murmushi tace "nice wallahi kasan karshen wata yayi," ta kalli Hibbah, Hibbah tace "ina yini?" shima yana 'yar dariya yacer "lafuya lau, eh fa kin kawo wata ba'kuwar kenan?" "Eh wallahi allah yasa hajiyar na nan," delu ta tambaya. "Eh to wacce daga ciki?" "Hajiya Zainab mana" " tana ciki" delu tace "bara mu karasa ciki." Ta fada tana shiga cikin gidan, binta Hibbah tayi tamkar wata jela tana kuma kallon cikin gidan tana mamakin wannan gidan. Fili ne fatal sai wani bangare da aka ware don Adana motoci saida sukayi yar tafiya sannan suka kuma shiga wata k'ofar nan ma da 'yar tazara sai kuma taga k'ofofi guda uku. Ta bangaren daman taga delu ta k'wank'wasa, wata matace ta fito ta bude musu wacce bazata huce sa'ar delunba itama da fara'a tace "delu kece tafe?" Delu tai yake tace "eh wallahi hajiyar dai na nan koh?" Delu ta tambaya, da sauri Hibbah ta ce "ina yini?" Matar ta kalleta tace"lafiya lau," ta kalli delu "Eh tana ciki, amma dai wannan ce wadda kika kawo mata a madadin dije koh? Don jiya ma saida tace na duba Mata anan wajen mu wai tajiki shiru, ashema kina tafe, yarinyar kuwa mai hankali," delu tace "eh wallahi bara mu shiga," Ciki suka shiga nan fa Hibbah ta kuma baza ido tana kalle kalle, parlor ne babba an tsarashi da kujeru na zamani, babu wani tarkace a parlor'n, kayan kallone na zamani sai center carpet din dake shinfid'e a tsakiyar parlor'n da wani table da aka d'ora a kanshi, sai daining area. K'ofofi biyu ne a parlor'n wata 'yar hanya sai kuma bene dake can gefe. Hibbah ta shagala da kallon tsarin gidan sai ji tayi ta yi tuntub'e ta tafi kamar zata hantsila tai saurin ja baya, da rawar jiki ta shiga bashi. Shi kuwa janye kafarsa yayi yana murmushi baice komi ba ya maida hankalinsa ga TV da suke kallo. Mugun kallo delu ta bita dashi tana zama a k'asa tace "wai ke baki da hankali ne? Ace mutun don ya rayu a k'auye sai ya zama marar hankali? Dan allah Faruq kayi hakuri" wanda aka kira da faruq din yace "babu komai baba, dole ai ta nuna bak'unta." Ita dai Hibbah batace komi ba sai sunkuyar dakai da take yi ta zauna itama a rakub'e, sauran yaran dake parlor'n suka gaishe da delu a dak'ile, 'yammata ne su biyu wanda baza su huce sa'annin Hibbah ba sai kuma wani k'aramin yaro dabazai huce shekaru shida ba. Kan Hibbah na k'asa ta shiga gaishe su, 'yammatan suka amsa a dak'ile Faruq ya amsa yana kallonta kafin ya mike yabar parlor'n Wanda yayi daidai da saukowar wata budurwa daga benan parlor'n kana ganinta kasan 'yar uwar Faruq ce da sauran yaran don suna tsananin kama, amma kana ganinta kasan ta girme musu. Wayarta data bari a parlor'n ta d'auka tare da komawa zata hau benan Faruq yace "Aunty Aysha pls dan kira musu momy sun dan jima da zuwa suna jiranta," wadda aka Kira da Aunty Aysha tace "suwa fa?" Don ita batama Lura da su delu ba. Faruq yace "wannan wadda take kawo mata 'yan aiki ce, gata nan a zaune," kallon inda ya nuna mata Aunty Aysha tayi tace "lah baba delu ina yini Ashe zakizo har momy ta fidda rai da zuwanki," ta fad'a tana k'arasowa kusa da su delu, delu tai murmushi tace "lafiya lau Aysha wallahi ina tafe ina momyn taku?" Aunty Aysha tace "tana sama bara na kira miki ita," ta kalli Hibbah tace "wannan ce yarinyar? Kyakykyawa tubarkallah ga kuma hankali" Delu tace "hmm itace ina wani hankali anan daga zuwan mu har ta fara rashin hankali," Aunty Aysha tace "me tayi na ganta nutsatstsiya," "ina nutsuwa anan, daga shigowarmu ta taka Faruq dake zaune." Delu ta fada tana hararar Hibbah. Faruq har yakai k'ofar shiga d'akin su yaji delu na fad'ar ta taka shi, ya waigo yace "Aunty Aysha bata sani bafa," yana gama fad'in haka yayi shigewarsa. Kallon Hibbah aunty Aysha tayi wadda duk ta kuma takurewa tace "ya sunanki?" Hibbah cikin sanyin murya tace "Hibbah!" Aunty Aysha tace "wow nice name dama ana samun irin wannan sunayen a k'auye?" Delu ta tab'e baki tace "uhumm ita dai gashi nan" Aunty Aysha ta kalli goshinta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63