Chapter 30
Chapter 30
shi kansa yasan bai samu masuk'i ba a wajen ta, ko kad'an baiji ba shi sai burge shi ma da take yi, "Hibbah baby bana son ki shan kunu da cin magani, sonki ne ya ingizo k'eyata tiryan tiryan na biyo ki har gidan ku, banga lefin mai gadinku ba don a kan aikinsa yake shi yasa na tsaya anan to amma mu shiga mota don ina buk'atar yin sirri da ke kin gane?" Ta tsuke baki "ina baka hakuri, saboda na fad'a maka yayana bai barina na fito don inada mijin aure," yayi dariya "na fahimce ki babyna bani da damuwa da mijin da zaki aura, ai nima ina da aure kawai dai inason mu k'ulla k'awance ne cikin sirri, babu wanda zai sani idan kina so ma sai mu dingaa fita Abuja ko Lagos mu killace acen ba mai sanya mana idanu muyi soyayyarmu a cikin weekend, idan kina so ma a jirgi zan dinga killace ki don bansan kisha wahalar mota," wani taikici ya tokareta a wuya "wannan ba harkata bace ni 'yar mutunci ce kamar yarda ka gani a siffance sai kaje ka nemi dai dai dakai k'warya tabi k'warya," "haba baby sone yake d'awainiya dani in banda haka da tuni nabar wajen nan" ta kalleshi "to ka bari mana ni na rik'e maka k'afa ne?" Da gudu motar Faheem ta huce su, uncle Sadeeq nata yi mata surutu kamar aku, Sam bata fahimtar abinda yake fad'a hankali ta nakan Faheem. Faheem ya k'urawa inda suke ido a hargitse zuciyarsa ta tunzura zafi take yi masa, shi kanshi mamakin kansa yake yaushe ya samu wannan zafin ran? Wannan abida yake yi harara cikin duhu ne iskace take wahakar da mai kayan kara don yarinyar bata ma san yanayi ba ga kwashe kwashe data tsira suyk tacin karansu babu babbaka, to mema ya kawo Sadeeq Shu'aibu nan wajen? Ya sanshi cikakken sani don tare sukayi secondary school, amma irin abotar nan da batayi nisaba, irin alak'ar makaranta ce da angama kowa ya kama gabansa sai dai idan wani dalili ya had'asu a gaisa da juna. Amma hakan bai hanasa sanin halayyar Sadeeq ba don yanajin labaran a wajen abokansu na neman mata, shiyasa Faheem bai fiya son mu'amala dashi donshi duk abinda zai zubar masa da mutunci da k'imarsa a wajen Jama'a bai sonshi, shiyasa duk macen daka ganta da Sadeeq dole ka zargi wani abu a tsakaninsu. Da k'yar ya shiga gidan ya kasa zama a parlor kamar yaje ya gargad'I Sadeeq kar ya sake ganinsa da Hibbah, to amma in b'era da sata daddawa ma da wari, ita ta bashi daman zuwa yasan tun sanda suke tare? Ko sallama basuyi ba ta kamo hanyar gida, tana shigowa tayi tozali da wani kallon tuhuma da yayi mata wani burki taja tayi tuntub'e da fushinsa dan ta gani yau a fuskarsa ta nuna. Jikinta sai rawa yake hantar cikinta ta yamutsa yau karon ba dad'i, saboda zabar b'acin rai har fuskarsa ta canza kamar fuskar Faruq idon zaici zalinta. Cikin sand'a sad'af sad'af zata wuce, yace "zo nan...............," *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Sautin muryar data ji yasa cikinta wani irin hautsinawa, ta durk'usa kanta k'asa tana sauraron hukuncinta may be taji saukar mari ko kuwa rufeta zaiyi da duka. "Don me kike kawo min irin wad'annan 'yan iskan gidana an fad'a miki dandalin bariki ne? Tun yaushe ma kike mu'amala da shi?" Ta kasa cewa komai sai k'asa da ta kuma yi da kai, "to bazan amince da wannan iskancin da rashin mutuncin ba da kin jawo Faruq yau kuma kin janyo wani har kin Bashi dama yazo min gida saboda nan ne matattarar 'yan bariki ko? Ki sani bana d'aukar nonsense na kuma fad'a ak'idata d'aya ce banazanjawa, na tsani munafinci gara ki nuna kanki kawai nasan inda kika dosa ba Wanda zaiyi tunanin idan an sa miki yatsa a baki zaki gatsa, kin bani mamaki kin bani kunya kisan yadda za kiyi da wannan kwashe kwashen banzan naki koki kama gaban ki!!" Wasu zafafan hawaye ne suke sauka a kuncinta, Kalmar k'arshe itace take dawo mata "koki kama gabanki!" Me wannan kalmar ke nufi kenan yana yi mata Kora da hali ne ko yaya? Garam! Ya buga k'ofar har tsakiyar kanta ta rintse idanunta da gudu ta shige d'akinta, wani abu yana mata yawo a cikin zuciyarta ta rasa gane menene wannan bak'in cikin zuwan uncle Sadeeq ne? Ko kuwa na mummunan zargin da Faheem ke mata ne, abin da take gudu shiya faru shikenan mutuncinta daya ke gani ya zube a idanunsa, dama shirun da yake yi mata tarata yakeyi yau ta cika masa ciki shiyasa yake mata kora da hali, ita duk cikin su Jabeer ne kad'ai take so, Jabeer mutumin kirkine yana da halaye masu kyau shiyasa ma tabar kyakykyawar alak'a ta shiga tsakaninsu, kuma shine dai yake zuwa da yardarta, amma Faruq ba ita ta kawoshi ba hasali ma baisan zai ganta a gidan ba, balle Wanda ya janyo fitinar uncle Sadeeq. Nawaz yazo ya kwanta akan cinyarta "aunty Hibbah kije kicewa daddy yayi hakuri naje yace baya son hayaniya," ta shafa kansa "to Nawaz ka bari ya huce ya daina fushin sai muje na bashi hakuri," ya gyad'a kansa kawai. Ranar har dare bata da wani sukuni maganganun Faheem ne kawai suke dawo mata, cikin tsakiyar dare ta kasa barci sai faman juyu take yi abin ya dami ranta bata son b'atawa mai kyautata, kallon mutuniyar banza Faheem ke mata baza ta iya goge wannan bak'in fentin ba, gashi yanzu yana yi mata hannunka mai sanda koda bazai kuma yi mata magana ba zaiyi ta tarata ne rana d'aya ya fad'a mata b'uru b'uru, da wad'annan maganganun ta kwana. Da safe gudanar da komai yadda ta saba saidai batayi sammakon fita ba yadda ta saba, bayan sun fits gaba d'ayansu ta d'auko Jakarta, yau ko school baza ta jeba don gidan su Umma kawai zata koma ta dubi hoton Nawaz dake bedside table yayi matuk'ar kyau tun ranar da tazo Nawaz ya bata shi, ta d'aukon ta rumgume wasu k'walla suka d'iso mata, baza ta iya kwatanta shak'uwarsu da Nawaz ba, ko ya zaiji idan ya dawo ya nemeta bai ganta ba, batason rabuwa da shi amma babu yadda zatayi. Ta mayar da hoton ma'ajiyarsa, bata da number Faheem data yi masa text message ta fad'a masa. Ta bud'e Jakarta a zaro paper da biro don rubuta sak'on da zata bar masa sai taji hannunta na rawa, a hankali ta fara rubuta masa sak'on _daddy ina neman afuwa, nayi abinda yake lefi ne a wajenka d'an Adam ajizi ne mai kuskure ne a koda yaushe, nasan akwai rashin fahimta da kayi min daddy bansan yadda Zan goge lefina a wajen ka ba, amma kayi hakuri Allah ya huci zuciyarka, mutunci madarane nasan nawa ya zube a idanunka kuma bazai tab'a kwasuwa ba to amma bincike da tuhuma wajibine akan mai lefi kafin a zartar masa da hukunci. Gaskiya d'aya ce daga k'inta sai bata nima ina da buk'atar ta inada dalilai daya sani tilas zanbar gidan nan,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63