Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO:+2349030159301 [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM* *INA GODIYA GA ALLAH SWA DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFIN. SALATI DA AMINCI SU KARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD SAW, ALLAH YA KARA MANA SON SA AMEEN.* *NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN DUNGURUNGUM GAREKI MASOYUYATA AYSHA ALIYU GARKUWA. ALLAH YA KARA BASIRA DA DAUKAKA, ALLAH YA RABAKI DA SARRIN MAI SARRI YA TSAREKI DAGA DUKKAN MAKIYANKI. YA ALLAH INA ROKANKA KA DAUKAKA AYSHA ALIYU GARKUWA KASA TAFI KARFIN DUK WANI MAKIYINTA AMEEN* *INA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFINKI BANDIRAWO DA KIKAYI ALLAH YA SANYA ALKHARI YA KARA BASIRA DA BAIWA MAI TARIN YAWA AMEEN.* Kauyan *katsalle*wani karamin kauye ne dake cikin kauyen *bunkure* dake jahar *kano*. Malam Mukhtar da iyalinsa na daya daga cikin mazauna cikin kauyen. Matan malam Mukhtar biyu lami itace uwargida sannan Aysha amarya. Tun auran malam Mukhtar da lami shekara goma allah bai basu haihuwa ba hasalima ko bari lami bata taba yi ba. Malam Mukhtar ya damu kwarai da rashin haihuwa da bai samu ba, wannan dalilin yasa shi Karo aure. Allah ya hadashi da Aysha yar mokocinsu ya aureta, bakaramin tashin hankali lami ta shiga ba jin wai mijinta zai Karo aure sannan kuma yarinya karama zai aura wadda bata fi yar cikinta ba, wannnan dalilin yasa lami shiga ta fita na ganin ta hana wannan auran amma sam abu yaci tura duk wajen malamin da taje magana iri daya suke fada mata dole ne sai yayi wannan auren, Wannan dalilin yasa ta hakura da bin malaman ta daura damarar yiwa malam Mukhtar da Aysha tijara da rashin mutunci Sam ta hanasu sukuni da kwanciyar hankali kullum cikin neman masifa take. Wata tara da auran Aysha da malam Mukhtar allah ya a zurtasu da 'ya mace kyakykyawa sak ta dauko kamannin Aysha, kasancewar ita Aysha kyakykyawace tamkar balarabiya. Haihuwar da Aysha tayi ya kuma daga hankalin lami, ranar da akayi haihuwar ta wanke kafarta ta tafi gidan aminiyarta delo ta fada mata abinda ke zuciyarta ba bata lokaci delo ta zari mayafi suka kama hanyar gidan bokansu. Suna zuwa suka fada masa bukatarsu nan ya bata kullika da wanda zatayi turare dana tsarki da wanda zata zubawa malam Mukhtar a abinci ya tsani Aysha da 'yar ta ta. Bayan ya gama yi musu bayanin kumi lami ta kunce gefen zaninta ta kunto kudi ta zubewa boka sukayi godiya suka tawo cikinsu fal murna. Tun daga wannan ranar malam Mukhtar ya juyawa Aysha baya, baya shiga dakinta ko magana ma bayi mata yakeyi ba saidai idan lami ta zugoshi yazo ya balbaleta da fada, KO sunan jaririyar ma ita ta sama mata *HIBBATULLAH* _gift of Allah_. Haka rayuwa ta juyawa Aysha da 'yarta cikin lokaci kankani, shekarar Hibbah daya allah ya bawa lami 'ya mace so kuga rawar kai wajen malam Mukhtar da lami, tunda lami ta haihu Aysha takoma tamkar yar aiki komi ita takeyi wankin kashi kirki komai ita keyi. Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar lami wato Rahmatu, akasha shagalin suna duk da kauyene amma malam Mukhtar ya kashe kudi. Rahmatu ta taso cikin sangarta da shagwaba sabanin Hibbah data taso cikin tsangwama da kyara da tsanar da mahaifinta yake nuna mata. _wannan kenan_ "Ke Hibbah! Hibbah ina kike ne? kina jina ina kiranki ayeh?" Lami dake zaune a tsakar gida ta fada tana karasa jera abincin siyarwarta a faranti, Rahmatu na taya ta. "Na'am Inna gani nan zuwa" Hibbah ta fada tana fitowa daga wani dan karamin daki rike da hijjab dinta a hannu tana kokarin sakawa. A hankali ta karaso ta tsugunna a gaban Inna lami tare da cewa "gani Inna". Murfin dake hannun innan ta kwada mata aka tana cewa "ubanki kikeyi a dakin kina jina inata a kwada miki Kira amma kikari burus kika k'i amsawa koh? Saboda kin rainani koh?" Cikin tsantsar masifa da daga murya take magana. Da sanyin murya tace "Dan allah Inna kiyi hakuri wallahi hadda nakeyi,gobe malam zai ansa hadda kuma duka zaiyi idan ban iya ba...........". "Ni zaki fadawa karatu don ubanki ko don ba waccan tambadaddiyar uwar taki bace take kiranki, ayeh?" Cikin masifa da bala'i ta katseta. Kasa Hibbah tayi da kanta ta kuma cewa "kiyi hakuri inna" "Bazanyi hakurin ba shegiya munafuka sai anyi magana kice ayi hakuri da hakurin ta mutu sadakar nawa kika bada? Nace sadakar nawa kika bada? Kuma wallahi wannan makarantar gaf kike da daina zuwanta don bazai yuyu ba ki dinga yimin cikas acikin Sana'a taba tashi ki dauka ki fitar min dashi kuma saura ki dawo min da saura kiga yarda zanyi lasalasa dake a gidan nan". Magana takeyi ko numfashi bata saukewa. Matsawa tayi kusa da farantin ta dauka ta Dora a kanta data Fara tafiya taji Rahmatu Na cewa "wallahi Inna bakin cikin Hibbah take miki, kullum sai sale driver yace takai masa amma taki ta Kai masa, tun rannan dayace zai siye duka shine tace bazata saida masa ba." Rike baki Inna tayi tanajin Rahmatu sannan cikin tsantsar masifa tace "ke Hibbah zonan yar bakin ciki" jikinta ne ya fara kyarma ta juyo cike da tsoro ta tsugunna a gabanta. Wata maka Inna ta kaimata a fuska tace "bakin ciki kike yimin kar a siye kwantai kike so nayi? To wallahi kika dawo min da kwano data wallahi sai naga mai kwatarki a gidan man shegiya Mai zubin aljannu, tashi ki bar min gaba." Tashi tayi hawaye nabin gefen fuskarta tayi hanyar zaure da niyyar fita ji tayi an dafa kafadarta ta San ko wane hakan yasa cikin sauri ta goge hawayenta, sannan ta kakaro murmushi ta juyo Umma ce a gabanta wadda a gabanta akayi komai, dauke da murmushi a fuskarta tace "kiyi hakuri hibbatullah wata Rana sai labari kiyi ta hakuri *RAYUWA* mai canji ce wata Rana ma bama duniyar baki daya." Murmushi tayi tace "wallahi Umma babu komai a raina nasan haka allah ya kaddara min tawa *RATUWAR*" Umma ta shafa gefen fuskarta tace "yauwa Hibbah allah yayi miki albarka". "Ameen "Hibbah ta fada tana kokarin fita daga gidan. "Hibbah" Umma ta fada tana karasowa kusa da ita. Juyowa tayi tare da cewa "na'am Umma" kuma dafa ka fadarta tayi tace "don allah Hibbah....." Katseta... *Idan kuna bukatar Na cigaba sai naga comments naku ta wannan number 07088301840* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* 2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Masoyana na samu sakonnin ku kuma in allah ya yarda zan cigaba da wannan littafin na gode da kauna da kulawa da kuka nunamin.* Katseta Hibbah tayi da cewa "na kula da kaina karna kula kwayan banza, karna biyewa wani namiji muyi hira kuma na zama mai kamun kai da nutsuwa a wajen sana'ata na girmama mutane, duk wanda ya zomin da wata magana dabai dace ba karna kulashi ko ba haka ba Umma?" Hibbah ta jero mata wadannan kalaman. Umma kuwa tsayawa tayi tana mamakin yarda d'iyar tata tasan abinda take son fada mata. Cikin mamaki

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});