Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har kuka inganta mata musamman ma Aysha yadda kike kula da Hibbah babu Wanda zaice ba 'yar uwarki bace ita ashe k'anwarki ce jinin Ku d'aya" Daddy ya d'ora da cewa "bayan batun Hibbah akwai wani dalili mai k'arfi da ya samu zuwa gidan nan" ya mik'a mata hotunan da Abba ya d'auko nata da su Alhajinsu, ta amsa tana gani cike da tsantsar mamaki tabbas wannan suna Kama da ita lokacin tana yarinta don baza tace Hibbah bace don dad'ewar hoton amma kuma ita tunda take bata tab'a sa irin wad'annan kayanba. Ta dubi Daddy cikin nutsuwa tace "Alhaji gaskiya wannan bani bace don banma tab'a saka irin wad'annan kayan ba da na tab'a saka su to babu tantama nice" Daddy yayi murmushi "tabbas kece a jikin hoton nan Aysha" nan Abba ya bata labarin duk abinda ya faru. Umma ta sunkui da kai tana tunani ita dai tasan tabbas a k'auyen katselle aka haifeta, ta yaya zasu zo su bata wani labari daban bayan kuma ga mahaifanta nan a raye baba da gwaggo. Ta dubi su Daddy "kuyi hakuri gaskiya wannan labarin ma ba ni bace a cikinsa don ni iyayena suna nan a raye basu mutu ba" Daddy ya kuma murmushi "Umman Hibbah kina nunawa kamar baki yarda da mu ba ko? To idan ba damuwa ki shirya yanzu muje wajen su iyayen naki na k'auye mu tambayesu zasu fad'a miki gaskiyar abinda yake faruwa, mun tambayi Alhaji ya amince mu tafi tare yanzu kawai shiryawa zakiyi mu tafi." Umma tayi shiru tak'i tashi daga wajen balle taje ta kintsa, Hibbah ce ta matso kusa da Umma ta rik'o hannayenta "Umma don Allah ki tashi muje don tabbatar da abinda su Abba suke zargi, Umma Abba yana son 'yar uwarsa yana sonki a kusa dashi ki taimaka masa don Allah" Umma ta kalli 'yarta ta "naji na amince zan biku" "yauwa Umma mun gode" Umma ta mik'e ta shiga d'aki ta d'auko duk wani abu dazata buk'ata ta fito suka nufi k'auyen katselle. Motarsu tayi parking a k'ofar gidan su Hibbah don Daddy ne ya rok'i alfarma su fara tsayawa k'ofar gidan d'an uwansa don yana son ya fara ganinsa. Yara suka zo suka baibaye motocin, suka fito daga ciki suna kallon yanayin k'auyen Daddy ya kalli Hibbah "Hibbah shiga ciki kiyi mana iso" ta dubi Daddy duk yanayinta ya koma na tsoro sai k'ifta idanu take "Daddy tsoro nake ji inajin tsoron Inna lami wallahi" Aunty ta dafa kafad'arta "tawo muje babu abinda ta iya tayi miki" Hibbah ta gyad'a kai Saudat tace "nima zani" Safiyya da Kausar har suna had'a baki "ku tsaya ni" suka tsaya suka k'araso suka shiga gidan hannun Hibbah yana cikin na Nawaz. Sukayi sallama Rahmatu ce ta amsa musu tana zaune a tsakar gida tasa turtsetsan cikinta a gaba, ta nuna musu tabarma suka zauna ta gaishesu ita sam bata gane Hibbah ba tace "kuyi hakuri yanzu innar zata dawo ta fita ne" Hibbah tace "ba komai ai zamu jirata sai dai bamu kad'ai bane akwai iyayenmu mata da maza a waje suna son ganin baba, ya dawo ne?" Rahmatu ta tsaya tana kallon Hibbah tana son gano wani abu tattare da ita, bata gane fuskarta ba amma muryar tana ta tunanin ko Hibbah ce amma kuma tana mamaki anya Hibbah ce. Hibbah ta katseta "wai Rahmatu aure kika yi ne na ganki da ciki?" Rahmatu ta zaro ido "Hibbah kece kinga yadda kika koma kuwa, Hibbah ki yafe min kinga yadda *RAYUWA* ta mai dani ko hausawa sunce idan zaka gina ramin mugunta ka Gina shi kajere wata Rana kai zaka fad'a, gashinan Inna taso lalata miki rayuwa Allah bai bata iko ba sai Allah ya dawo mata da abin kaina Hibbah ba aure nayi ba....." Sai ta saki kuka ta rik'o hannun Hibbah "Hibbah ki yafe min don Allah Inna ta b'ata min *RAYUWA* garin son kud'i Inna ta sani na koma karuwar k'arfi da yaji gashinan yanzu sun b'ata min rayuwa sun guje ni, cikin nan da yake ni kaina banson na waye ba a tsakanin sale direba ko kuma Musa d'an Inna delu. Hibbah kowa ya guje ni Inna kullum a cikin hantarata da kyarata take, duk son da baba yake yi min yanzu ya daina k'awaye na sun gujeni kowa a k'auyen nan k'yamata yake yi, Hibbah nayi nadama nayi Dana sanin biyewa Inna dana yi gashinan yanzu na lalata rayuwa ta" Hibbah ta shiga share mata hawaye itama hawayen na bin fuskarta "baki yi min komai ba Rahmatu na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana" "na gode 'yar uwata na gode, su waye wad'annan?" Hibbah ta dubi su Aunty "y'an uwan mu ne danginmu ne su bamu sani ba" "danginmu kuma kamar ya dama muna da 'yan uwa a birni?" Rahmatu ta tambaya cike da mamaki. "Eh Rahma kuna dasu mana muma bamu sani ba sai yau d'innan" Aunty ta bata amsa, Rahmatu sai taji sunan wani iri don ba haka ake kiranta da shiba, Aunty ta shiga bata labarin duk abinda ya faru. Rahmatu tayi mamaki sosai "Hibbah ashe rabon kije birni ki samo mana dangin mu ne yasa Inna ta turaki can ikon Allah, to ku shigo dasu ai ba'a barsu a waje ba ko?" Wayar Hibbah tayi k'ara ta duba bak'uwar number ta gani, da kamar bazata d'auka ba sai kuma ta d'aga "hello my heart desire ya ake ciki ne kun barmu a waje" ai Hibbah suman zaune tayi jin furucin Faheem ta kasa magana yace "hello kina jina?" "Ammm.....dama......dama yanzu zanzo na shigo daku" ta fad'a cike da in ina ta kashe wayar, Aunty tace "keda waye kike masa in ina?" "Ba kowa Aunty Daddy'n Nawaz ne yace sunji shiru" Saudat ta kwashe da dariya "to ai saiki tashi kije kar kisashi ya kuma ziyartar Dr" Hibbah ta kai mata duka suka sa dariya. Ta fita ta shigo dasu Rahmatu ta kuma shimfid'a musu wata tabarmar suka zauna ta gaishe su, Hibbah ta gabartar mata da kowa a cikinsu, Rahmatu ta nuna Umman Hibbah "Hibbah kardai kice min wannan Umma ce?" "Itace Rahmatu" Rahmatu ta zube a gaban Umma tana neman yafiyarta ta fad'a mata duk abinda ya daru da ita. Umma tace "babu komai Rahmatu ni baki yi min komai ba ina innan taki?" "Ta fita amma yanzu zata dawo...." Kafin ta rufe baki Inna lami ta shigo tana kallonsu da mamaki................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```Wattpad@mamyn_najmah2222``` Mamakin ta ita dai rasan bata da kowa a birni to me ya kawo 'yan birni gidan kuma ta gani har da manyan mutane bayan jerin motocin da ta gani a k'ofar gidan. Ta k'araso tana wangale musu baki "sannunku da zuwa" dukkan ninsu kallonta suke da mamaki yayin da Hibbah zuciyarta cike take fal da tsoran Inna, Daddy ne ya amsa mata da yauwa, ta gaishe su ka amsa ta dubi Rahmatu cikin fad'a kamar ba Rahmatu 'yar lelen Inna ba "ke Rahmatu kina gani anyi bak'i ba zaki kawo musu ruwa ba, kuma baza ki lek'a gidan delun ki kirani ba" Rahmatu tayi shiru tare da yin k'asa

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});