Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Hibbah tana shiga d'aki ta shiga tunani tabbas Faruq jikinta kawai yake so ba wai yana sonta tsakani da Allah bane, da sunyi auren yana samun abinda yake so shikenan zai koma duk wasu d'abi'unsa, gara tun da wuri karta sake ta yarda ayi wannan auren, to amma mene mafita? **** Faheem kuwa cikin dare ya kasa bacci, da k'yar ya kalli agogo dare yayi sosai tsit kakeji sai haushin karnuka daga cen nesa isaka ke kad'owa. Kamar yasha abin maye, jirim jirim yake jin kansa tunani yayi masa yawa zuciyarsa ba dad'i yayi wani d'an tsaki me yake kawo masa ciwon Kai ne, ya juyo ya dubi Kausar barcinta take hankali kwance irin mai dad'in nan don ta kwaso gajiya, babu ruwanta da irin damuwar da yake ciki Anya wannan macen ita ta dace da ya zauna da ita, sam bata damu dashi ba bare ta san damuwarsa har ta kwantar masa da hankali. Ya shafa kanta yana son Kausar saidai rashin kulawar da bata yi masa ya dakusar da son da yake mata, a ganinsa duk mace burinta ta tarairayi mijinta ta kula dashi donta mallakeshi amma ita banda ita aikinta yafi masa mahimmanci. A hankali ya shiga kiranta a cikin kunnenta "Kausar" saida ya tashe ta ta karanto damuwa tsantsa a cikin idanunsa, babu abinda yake buk'ata a yanzu kamar ta sanyaya mishi zuciyarsa har ta huce ta daina yi masa wannan rad'ad'in da yake ji. Ita kanta ma ta damu da kewarsa tasan tayi missing mijinta tasan dole ya damu bata tsinana mishi komai tana dawowa datayi sallah taci abinci sai barcin gajiya, da safe kuma kafin ya fita ma ta fice, lallai ta jinjina hakurin Faheem wasu lokutan yakanyi fad'ansa da mitarsa ya hakura, ita kanta tasan ya fita gaskiya amma saita take don ita aikin nan jinsa take a jininta. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣8⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Haka Kausar tayi k'ok'arin faranta masa a wannan daren fiye da yadda yayi tsammani har ya ma manta da wata matsala da take damunsa, sai yaji ina ma haka Kausar zata d'ore, mace mai neman albarka ita ke faranta ran mijinta a duk sanda ta ganshi cikin damuwa sai tayi k'ok'arin kawar masa da wannan damuwar. Bayan komai ya lafa yaji wannan abun dake tsaya masa a zuciya ya dawo, ikon Allah wato wannan abun bazai k'aye sa ba kenan. Washe gari ya kama juma'a yayi wankan juma'a cikin wata rantsatstsiyar shadda mai mugun kyau, yayi kyau da sosai ya fito tamkar saurayi baza ka tab'a cewa Faheem yana da aure ba, Faheem akwai iya kwalliya da k'yale k'yale kamar mace. Ya fito da alama masallaci zashi, "Daddy" ya juyo don sautin yad'an tab'oshi, ta cigaba "dama Aunty tayi min waya wai zanje nayi mata kwana biyu don bata jin dad'i" d'if yayi abinda yasa ta dubanshi kenan ashe shima itan yake kallo, ya dawo ruwa tsundum wai shifa ya yanke shawarar zai dake bazai k'ara bari wannan abun ya dawo masa ba, yana k'ok'arin dak'ile shi k'arfi da yaji to amma bayin kansa bane abin yana fitowa ne a duk sanda zai d'aga idanunsa ya kalli Hibbah ko kuma ya ganta da wani tana mu'amala dashi, ko kuma idan bai ganta ba yana jin shi kamar ya rasa wani abu muhimmi ne a rayuwarsa, tun jiya har yanzu wannan abun yana jinsa a zuciyarsa gashi ita kuma yanzu Aysha na k'ok'arin nisanta shi da ita, anya kuwa zai iya jure rashin Hibbah a kusa da shi? Da k'yar ya nemo abinda zai fad'a mata don kada ta zargi wani abun "ki Bari ni zan same ta basai kinje ba" yana gama fad'in haka ya fita. Haushi ne ya kamata bata so ya hanata fita ba ita saidai ta zauna tana yi musu gadin gida kenan, ita kenan bata da 'yancin kanta gaskiya gara tayi aurenta ta huta da wannan mulkin mallakar. Bai nemi Aysha sunyi maganar ba donshi shaf ma ya manta sai da yamma ya fita ya tuna, ya sassauta gudun da yake yi ya nemi Aysha ta waya, bayan sun gaisa yace "me ya faru ne wai yarinyar nan zata zo me zata yi miki?" "Yaya bana jin dad'i ne shine nake so na karb'i ajiyata dana kawo" "hmmm amma dai kinsan idan ta tafi akwai matsala a gidana, ina mai miki aiki?" Tayi dariya "ba komai tana nan dama nafison ta dawo hannuna tunda maganar aurenta ta taso, ya kyautu itama da ta k'arasa jarrabawarta tayi aure tunda ta samu miji, Jabeer ya takura min da maganar Sanra rana shiyasa nake son ganinta, na yaba da hankalinsa kuma bata b'oye masa komai ba akan dangantakar dake tsakaninmu da ita, to shine nake son naji ta bakinta asa ranar yanzu ne ko kuwa a bari saita k'arasa kammala WAEC d'inta don muma musan irin gudunmawar da zamu bada ko?" Ya taka burki don hakan shine kawai zaifi samun nutsuwa don maganganunta sun Sanya shi cikin wani yanayi, kai shi dama baiyi mata wayar ba don kalamanta sun sanya shi cikin wani tunani. "Yaya kana jina kuwa naji kayi shiru" bai ce komai ba ya kashe wayar, gorar ruwan faro ya d'auko yana sha kad'an kad'an sanyin ya ratsashi har cikin zuciyarsa, yayi ajiyar zuciya yana ganin kiran Aysha ya k'yale don bazai iya cigaba da jin wad'annan maganganun nata ba zasu iya kaishi emergency yanzu, zurfaffan tunani ya tafi mai zai hana yayiwa kansa k'iyamul laili me yasa zai haramtawa kansa abinda ya yarda yana yiwa tsarkakakkyan so, gaskiya zai k'wari kansa wajen nuna kawaici da nuna nauyi baki anya zai iya cigaba da hakuri har ya sadaukar da irin wannan son, zai iya haifar masa da ciwon zuciya. Yaso yaji ta bakinta akan mu'amalarta da Faruq don baison alak'arta dashi amma tak'i fad'a masa da alama Faruq zai zame masa k'adangaren bakin tulu. "Uncle" d'ane bayansa yana k'yalk'yala dariya, yana son Nawaz don yashiga ranshi sosai, tayi murmushi Faruq, Faruq duk shigar da yayi tana yi masa kyau kamar Faheem, sun iya shiga mai tsari kodai a jinin su hakan yake kamar gaske wuyansa yau ba sark'a. Ya dubeta "masoyiyata kinyi min kyau yau fiye da kullum" ta dubi kanta material ne yellow anyi mishi d'inkin Riga da skirt yayi mata d'as a jikinta, ya matso yana k'ok'arin tab'ata taja da baya ta kawar da kanta gefe, "bana son abinda kake min donni a wajena hakan ba waye bace saboda irin tarbiyyar da aka koyar dani hakan bai dace ba" "to ya kike so nayi Hibbah, so ba abinda bai sawa kinsan yadda sonki yake a rayuwata kuwa kawai kiyi hakuri dani, bara kiji wallahi saboda ke na dad'e banyi mu'amala da mace ba na tada kaina harsai ranar auren mu" "Duk sanda zakayi abu kayi shi domin Allah, kajo tsoran Allah bawai saboda ni zaka daina mugayen ayyuka ba kabari domin Allah na sani shiriya ta Allah ce, don haka fad'in hakan bazai sani nayi wasarere da jikina ba domin mu ba muharramai bane, shed'an shine zai shiga tsakanin mu" "to amma ki sani so gundarinsa kansa mutum ya canza koda baison

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});