Chapter 42
Chapter 42
cup d'in yak'i taruwa, ta dinga yi masa dariya ya shammaceta ya ture nata bokitin ruwan ya zube, sai ya hau shima yi mata dariya harda tsalle yana k'yak'yata mata dariya k'ya k'ya k'ya. Ta lura da motar Faheem don basu ji shigowarsa ba saboda ruwan da akeyi a tunaninta bazai fito ba saboda ruwa karya jik'asa, ga mamakinta fitowa yayi abinsa, Nawaz ya dinga d'aga masa hannu "Daddy Daddy ruwa zai dokeka ka gani ya jik'a ka" ya karb'e lemar daga hannunta yana kallonta, ta sunkui da kanta "Hibbah" wannan lafazin na Faheem sai taji.muryar tashi ta canza "baki kawo min lema ba kin Bari ruwa ya jik'a Daddy'n Nawaz." Ya ilahi, ita dai wani abu take ji tamkar zata fad'i k'afafunta suka d'auki rawa, ya zuba Mata idanu kawai yayi nisa ya tafi da yawa ikon Allah haka so yake Allah ya had'aka da Wanda baka tab'a tunani ba. Kamar bata motsi kunya da nauyinsa sun rutsa da ita. Shi da kansa ya samu damar da yake jira yasa Hibbah ta fad'a tarkonsa yau k'wauron baki ya k'are zai fasa k'wai. "Hibbah" da sauri ta juya da gudu cikin gida, yayi d'an murmushi yana Mai jinjina wannan irin kunyar ta Hibbah. D'akinta ta shiga ta d'ora kanta a bisa pillow zuciyarta kamar tana harbawa idanunta Faheem kad'ai take gani kamar cikin cikin film wannan abu yak'i goguwa nauyi ne tsoro ne ko kuma kunya me yasa haka? Faheem dodo ne? Tsabar cika ido da kwarjini ne ta bawa kanta amsa. "Hibbah" yadda yake futawa take tunawa a tausashe sai taji kamar yafi kowa iya furtawa. "Aunty Hibbah kizo inji Daddy" zumbur ta tashi zaune ta kad'a kanta "to ina zuwa" Ta jima tana sak'a da kwancewa me ya hanata fita kiran Faheem don fa ya rud'ata nauyinsa ya k'aro. Ya bud'e k'ofar ya shigo, ta dubeshi ya jingiba bayansa da k'ofar ta saci kallonshi wata k'atuwar rigar sanyi sanyi ya Santa mai taushi kamar gashin jikin mage, ya cire hular jikin rigar daga kansa gami da Santa hannayensa cikin aljihun rigar. "Hibbah" sai da ta kad'u sassanyan kiran ya ratsa zuciyarta "Hibbah ni gani nazo tunda na aiko ki zo kin k'i fitowa ni d'in............ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* "Hibbah ni gani nazo tunda na aiko ki so kink'i fitowa ni d'in abin tsoro ne? Ni fa mutum ne kamar ki idan kuma kunya ce gaskiya tayi yawa" tayi shiru ta kasa magana "ok to ki saurareni ina so ne muyi wata mahimmiyar magana, kinsan so wani abu ne dake faruwa da mutum ba tare da zato ko kuma tsammani ba, munyi amanna da fad'ar Allah ta'ala shike jefa so a tsakanin d'ayanmu, na tsinci kaina a cikin wani hali mai wuyar fad'uwa may be ma kin fahimce ni kika basar, na nuna miki alamomi da dama ke mai hankali ce kinsan me nake nufi. Ina nufin kalma guda aure, idan banda shi bani da wata manufa a gareki, ni zan aureki amma da sharad'in abu biyu kina sona kuma kina ra'ayina don wad'annan abubuwan suke Gina aure." Saura kad'an numfashinta ya d'auke wani abu taji ya harba a zuciyarta, duk lissafinta ya wargaje , wata sabuwa inji d'an caca ko da wasa bata tab'a tsammanin wannan furucin daga bakin Faheem ba, ikon Allah wai ita Hibbah 'yar aikin gudansa ba kazar kowa ba ita yake so? Ta yarda wani wajen Ana gudunka ana tsanarka wani wajen kuma sonka da k'aunarka ake yi, duk mutumin da ake yiwa hassada da k'yashi sai hassadar ta zama kamar taki ake barbad'a masa Allah abin godiya wai ita ke da matsayin da Faheem yace yanaso tabbas idan Allah bai wulakanta ka ba babu mai wulakantaka a duk fad'in duniyar nan, Inna lami taso lalata rayuwarta amma da yake Allah gafuru rahim ne sai yayi hanyar zuwanta birni don wasu su gyara mata *RAYUWA* mai makon a lalata, Allah ne ya bata wannan baiwar bamai iya ja da ikon sa. "Ni zan aureki" kalmomin da suke mata yawo kenan, to me za tace abubuwa sun sark'e, "Hibbah" ya katse mata tunani, sai taji kamar ta fita da gudu don bayyana son nata gareshi zai dad'a nauyi da kunyarsa a tare da ita "Hibbah ya dai sai kin bani amsa ko muyi ta zama anan" Ya rud'a mata k'wak'walwa ta rasa Kalmar da zata d'orata a harshenta. Ya zauna gefen gadon nan fa taji daddad'an k'amshin dake manne a jikinshi ya kuma tsumata, a yanayin da take jin Faheem ranta shi d'inne tsagwaronsa kamar yadda take ji a yawan lokuta idan sun had'u abin na yi mata yawo, ko me kenan? Zata iya fassara shi da kalmar "so" to amma anya wannan so ne, idan sone me yasa bata jinsa ga Jabeer ko Faruq, tunda suma suna sonta kuma dasu ne ta Saba mu'amalar soyayya musamman ma Jabeer. Yau dai gata ga Faheem mutumin da take d'ari d'ari dashi, hanyar da yabi ma bata so ta bi don kar suyi arangama saboda mutuncinsa da k'imarsa da take gani fiye da kowane mutum a rayuwarta. "Haba Hibbah nifa bana son nayi ta magana a k'yale ni ni kad'ai bana jin dad''i, na jima a cikin k'alubalen sonki nayi k'ok'arin barin abin saboda wasu dalilai amma Hibbah na kasa jurewa, ba irin wannan son bane ake dak'ileshi yafin k'arfin hakan, na yarda da shi na kuma daina wani inkari cewa zan iya hakuri dashi domin ya wuce tunani na. Na sani kina ganin k'imata da girmana inason mu tafi a haka ki cigaba da ganin mutunci na, don ni hakan bazai hanani nuna miki k'auna ta zahiri ba tunda bawai wasa nake ba magana ce ta gaskiya ta aure, lokaci na k'urewa ko yaushe na k'ella ido na ganki sai abin ya tab'o min zuciya, bai kamata na b'oye miki ba don sai da amincewarki za muyi aure, kinga kuwa dole na nemi had'in kanki." Yayi murmushi gami da tsagaitawa ya maida numfashi "hmm Ana min rowar eyeball d'in nan har b'oyewa kikeyi don karna gani, Hibbah kinsan saboda ke nake dawowa gida da yamma, ko muryarki kawai naji sai hankali na ya kwanta, to ina zankai sonki bazai yuwu na iya daurewa ba ko kuma na cigaba da k'wauron baki ba, kinsan halayena nasan naki abinda na sani tuwo na maina za'ayi ki auri mai gidanki bana son tsaiko ki tare nan da sati biyu" ya dubeta "zuciyarki ta gamsu dani da shawarata?" Ta rufe idanunta da hannayenta magana dashi tana mata wahala. Hmm shidai ya sani akwai sanshi a tare da ita, sai dai ta kasa fahimtarsa ko ta san itama tana sonshi d'in domin kunyar da take mishi ai alamune na akwai wani abu a can k'asan zuciyarta dake tirsasa jin kunyar. "Hmm amma dai Hibbah nan zansha wahala dake wannan kunyar taki tayi yawa amma akwai lokacin da zan rad'a miki wani abu sai kin manta da komai banda ni d'in nan" ya mik'e "inason tuwon masara da k'ashin rago miyar kukan nan, ga wannan ki bawa Isah ya siyo miki abinda kike da buk'ata." Kud'i ne ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63