Chapter 55
Chapter 55
Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```wattpad@mamyn_najmah2222``` "Ranar wata juma'a da yamma na dawo daga gona na hango ki kinata gudu kina kuka abin tausayi na tsayar dake da k'yar kika tsaya kinata kuka kamar zaki shine, na tambaye ki meye saki kuka? Cikin shashshek'ar kuka kina magana da k'yar kika ce min 'yan fashi ne suka harbi iyayenki suna can a bakin titi. Naji tsoro sosai shine naja hannunki cikin zulumi da tsoro muka tafi bakin titin amma abin mamaki babu kowa akan titin saidai jini dake ta gudana ta wajen. Na tambaye ki ina suke kikace kema anan kika barsu sai na shiga tunanin ko wasu mutanan ne suka zo wuce suka d'auke su, banyi k'asa a gwaiwa ba naja hannunki muka je wajen mai gari na shaida masa komai, shi da kansa yasa a cigirta ko za'a ga iyayenki na barki a hannunsa n dawo gida inna bawa zulai labarin abinda ya faru ta tausaya miki sosai. Zawon sati guda ana cigiyar iyayenki ba'a samu ba, da mai gari ya ce a kaiki cikin birni wajen 'yan sanda ko zasu ga danginki ni na bashi shawarar ya barki kawai a wajensa duk lokacin da 'yan uwanki suka natsu suka dawo hayyacinsu zasu buk'ace ki, mai gari yace nayi hakuri bazai iya rik'e ki ba amma ni idan naga zan iya k'ofa a bud'e take sai na d'auke ki. Nace masa to amma bara naje nayi shawara da iyalina, na dawo gida na shaidawa zulai komai mutuniyar kirki sam bata nuna komai ba a ranta sai ma murna da tayi ita da d'anta Habu. Na koma wajen mai gari ya bani ke amana muka tawo tun daga ranar na rik'eki tamkar d'ana Habu sam bansan naga hawayen ki ko kad'an saboda amana ce ke a wajena." Malam ya d'anyi shiru "Aysha tunda yanzu ga danginki sunzo nemanki to ya kamata ki koma garesu musamman ma shi da yake son rayuwa dake" Umma wadda hawaye ya gama wankewa fuska ta d'ago tana kallon malam "baba dama ashe da gaske ne maganar da yake fad'a? Don Allah baba kace min ba haka bane kace min kaika haifeni ba wasu daban ba" "haba Aysha keda ya dace kiyi farin ciki da murna kinga danginki sai kuma ki rik'a wasu maganganu daban?" Gwaggo ta tareta da fad'in haka. "Gwaggo ba farin ciki ne banyi ba tabbas nayi farin ciki amma bansan a ce baku ne iyayena ba" Abba shima da hawaye suna zuba a idanunsa yasa tissue ya goge yace "Aysha k'anwata hak'ik'a yau ranar farin ciki ce a gare mu ranar mai cike da alkharai ranar da Allah ya bayyana mana fuskokin mu, ki kwantar da hankalinki domin kuwa har yanzu su malam suna nan a matsayin iyaye a gareki" Gwaggo tace "alhamdulillah naji dad'in zuwan wannan rana naji dad'i da Allah bai karb'i rayukan mu ba har ya bamu aron wannan Rana da zamu damka ki a hannun d'an uwanki," "tabbas zulai haka ne, yau zamu maida amanar da aka bamu sai dai kash mai gari da ya bamu ke Allah ya amsa abunsa, duk da haka yau zan Bawa yayanki amarki." Ya kalli su Daddy "ga amanar 'yar uwarku nan da aka bamu yau na dawo muku da ita" Daddy cikin jin dad'in lafazin tsohon yace "mun gode daamanar daka rik'e mana bamu da abinda zamu saka maka dashi anan duniya, Allah ya saka muku da alkhari" suka amsa da amin kowa murna yake. Daga haka suka shiga hira sosai sai can Daddy yace "don Allah malam ina rok'on alfarma a wajenku don Allah Ku yarda ku bimu birni mu zauna a can" malam yayi murmushi yana girgiza kai "a'a kuyi hakuri baza mu iya binku birni ba Ku barmu anan kawai" nan fa su Aunty suka shiga rok'on su da k'yar ya yarda zasu koma amma shi bazai zauna a can ba sai dai gwaggo ta zauna nan sukayi ta godiya daga nan suka shiga hira har akayi kiran sallar magrib mazan suka tafi masallaci su kuma matan suka a yi gida. Suna dawowa daga masallaci Daddy yace su taso suje gidan su Hibbah don sun ganshi yanzu ya shiga gidan. Haka suka d'un guma zuwa gidan su Hibbah. Kamar yadda suka shiga d'azu matan ne suka fara shiga suka tadda baba a k'ofar d'aki a zaune yayi shiru k'irjinsa sai bugawa yake yi dama yau tunda ya tashi yake jin k'irjinsa yana yi masa nauyi zuciyarsa tana harbawa gashi haka kawai sai ya dinga jin gabansa yana fad'uwa ko kuma ya zauna yayi shiru ya rasa me yake tunani yana son tuna wani abu amma saiya kasa tunawa. Su Saudat sukayi sallama suka shigo baba sai binsu d'aya bayan d'aya yake da kallo k'irjinsa na bugawa da yake akwai sauran hasken gari. Mamy ta k'ura masa ido cike da tausayin d'an uwan nata hawaye na shatata akan kumatunta tasa hannu ta share, baba yace "ku zauna ga waje" suka zauna suna gaishe shi ya amsa, Hibbah da Umma dai ba suyi magana ba. Bugun zuciyar baba ya tsananta a lokacin da sukayi ido hud'u da mamy da Sauri ya kawar da kansa gefe ya danne bugun da zuciyar tasa take yi yace "kune kuka zo nemana d'azu?" Momy cikin k'arfin hali da tausayin d'an uwan mijin nata kuma mijin k'anwarta tace "eh mune amma bamu kad'ai bane akwai mazajenmu da suke waje sune ma suke son su gana da kai" "ahh to ku shigo dasu mana ya zaku barsu a waje?" Aunty ta kalli Hibbah da tayi tsuru tsuru duk tsoro ya cikata tace "haba k'anwata ki nutsu mana ai komai yazo k'arshe da yardar Allah" Hibbah kawai kad'a kai tayi don gani take ko ya tayi magana Inna da baba zasu iya ganeta numfashinta ma a hankali take yi wai kar su ganeta. Aunty ta dubi Safiyya tace "Safiyya kije ki cewa su Abba su shigo"Safiyya tace "to" ta mik'e tai waje. Tana fita Inna na fitowa daga d'aki ta dubesu tana washe baki rik'e da fitila a hannunta "sannunku kun dawo?" Kausar ta yarfa mata harara Aunty tace "eh mun dawo" Hibbah ta kuma k'amk'ame Aunty ta fara kuka k'asa k'asa don a rud'e take sosai. Umma ta kalleta ta d'anyi k'asa da murya "Hibbah mene na kuka kuma babu abinda ta isa tayi mana Wanda Allah bai nufa zai same mu ba ki kwantar da hankalinki kinji?" Hibbah ta gyad'a kai Aunty ta janyota jikinta tana rarrashinta. Baba kuwa k'irjinshi da zuciyarshi ne suka tsananta bugawa gabansa ma ya shiga fad'uwa da sauri sauri. Ba jimawa su Abba suka shigo da sallama tabarmar da baba yake kai suka nufa zasu zauna, baba wanda tuni ya mik'e tsaye jin muryar da bazai tab'a mantawa ba ya shiga nuna Daddy yana girgiza kai yayin da kanshi yayi masa nauyi wani duhu ya halarci idanunsa tuni yayi taga taga zai fad'i da hanzari Daddy da Abba suka taro shi. Hibbah tana ganin baba ya fad'i ta k'walla k'ara tare da cewa "baba!" Ta dubi su Aunty suma duk sun rud'e tace "Aunty baba ya fad'i kar wani abu ya same shi" sai kuma tasa kuka. Gaban Inna ne ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63