Chapter 44
Chapter 44
Amma ina Jan hankalinka ka nutsu ka gyara halayenka don shi aure nauyi ne da hak'k'insa zai d'oru a kanka ka gyara zuciyarka ka zama cikakken mutum ka duba misali akan d'an uwanka Faheem mana abin kwatancena da alfaharina a ko ina za'a girmamashi." Ya gyad'a kansa "insha Allah Daddy Allah ya k'ara girma" "ameen" Faruq ya mik'e shikam tafi nono fari don farin ciki ya cika zuciyarsa a yau. K'wak'walwa ta hargitse ya fad'a motarsa gwuiwoyi a sab'ule, kamar an doke idanunsa sun k'ank'ance kansa yayi nauyi ya rasa meke masa dad'i a duniya yau zuciyarsa ta tunzura ta ya mutse "Hibbah" ya furta cikin wata iriyar murya ikon Allah abu biyu ne rak a kowane jarrabi na *RAYUWA* samu ko kuma rashi, nasara ko rashinta, amma rashin cikar abinda kake so yafi tada maka hankali don zakaji kamar ka rasa wani sashe na ruhinka. Wace irin rashin sa'a Gare shi wane irin so yake yiwa Hibbah gashi kuma ya sameta ta zama mallakinsa amma zai salwantar da soyayyarta don faranta ran mahaifinsa da d'an uwansa. Anya ma zai iya tuk'in nan kuwa? Aunty ta bud'e motar ta zauna, waya fi jin bak'in ciki tsakanin ita da Faheem, sam bata ji dad'i ba Faruq yayi nasara, gabanta ya cigaba da harbawa ta had'iyi yawu dak'yar cikin damuwa, nazarinta da tunaninta baika ga fahimtar Faheem ba ganinta ta fishi bak'in cikinda shiga damuwa da tana da yadda zatayi to tabbas da saita hana wannan auren, kawai abinda ta d'auka Faheem baya jin dad'i ne. "Baka jin dad'i ne naga yanayinka gaba d'aya ya sauya? Naga yanzu muke tare lafiya lau, ni maganar shashashan yaron nan ta dame ni" yayi shiru, hakan ya dad'a bata tsoro "Yaya karka tada min hankali wani abin ke damunka?" Ya sunkui da kansa shi kad'ai yasan me yake ji a zuciyarsa. Ya cira idanu ya dubeta saida gabanta ya fad'i ragagas, cikin razana ta fiddo ido tana mamaki bata tab'a ganinsa cikin wannan halin ba. Ya dafa saman kujerar da take zaune " Aysha babu Wanda zai iyayi min maganin fitinar da nake ciki sai Allah na shiga mawuyacin hali Wanda ni da kaina tunanina da hangen nesa na bai tab'a hango min shiba, domin zuciya ta ta Gaza sarrafuwa naso dak'ile tasirin al'amarin amma baud'ad'd'ene a yanzu lokaci ya k'ure min, saidai ni da kaina ina tausayawa kaina zanyi k'ok'arin hakuri Allah ya bani jimiri." Ya dubeta cikin idanu "ina son Hibbah son da bazan iya misalta miki shi ba na fahimci na fahimci hakan saboda abubuwan da suke faruwa tsakaninta da Faruq shiyasa na kasa samun nutsuwa nasa Hibbah gaba na tambaye ta don ina son gano abinda ke tsakaninta da Faruq, amma bata nuna min akwai wata alak'a a tsakaninsu mai k'afi ba kamar yadda na sani dai shike zuwa wajenta, na sanya idanu da tsaro don sanin halin yaron nan bawai yana sonta tsakani da Allah bane, da ita yarinyar zatayi tunani bai kamata ta kuma sauraronsa ba ko don abinda yayi mata, tsoron kar wani abu ya faru na kasa b'oye abinda ke zuciyata da farko na gana da Ummanta d'ari bisa d'ari ta bani goyon baya kafin nace zan aureta, a lokacin tace na kirawo waliyina a d'aura mana aure saboda son da nake yiwa Hibbah ya rufe min idanu, ban kawo komai a raina ba na Kira Abba na fad'a mishi komai Allah ya taimake ni a lokacin yana gari, a ranar da yamma aka d'aura mana aure da Hibbah a masallacin unguwarsu. Bana son abinda zai b'ata ran daddy Aysha shiyasa na yanke shawarar zan barwa Faruq Hibbah ni zan hakura!" Ya had'iye bushshshen yawu "Aysha ki kaini asibiti wani abu yana tab'o min zuciya" ta runtse ido ga mamakinta hawaye ya zubo mata saboda tausayin d'an uwan nata. "Haba Yaya wane irin hukunci ne wannnan ka yanke ma kanka, kai ne kawai is dace da aurenta domin kai mutum ne dana tabbatar baza ka tab'a wulakanta mace ba har *Abadan*, duk wani jin k'ai da tallafi zaka yiwa Hibbah a matsayin matarka saboda kyawawan halayebka haka matsalolin gidanka sun dakushe, amma Hibbah tasab komai kuma zata magance su da tafiyar da al'amuran iyalanka. Ta saba da Nawaz ta jashi a jiki tana tarairayarsa me yafi wannan kwanciyar hankali, gata mai ladabi kuma tana baka girmanka dayi maka biyayya bata tab'a tsallake maganarka, wallahi na tabbatar Hibbah xata amince da auren nan ko musu baza tayi ba, ko da ace bata ra'ayin aurenka maganar gaskiya kawai idan su dadday sukaje sukaji tana da aure sai mu fad'a musu kaine mijin, amma zancen sadaukarda soyayya ma bai taso ba." Ya numfasa "Aysha kinfi kowa sanin halayena bana son naga ko kad'an na b'atawa su daddy rai, kinsan yadda yake ji da Faruq kina ganin dai maganganun daya fad'a miki don kawai kince bazai aureta ba, to ina kuma ni Dana aureta gaba d'aya? Gobe idan sunji tana da aure a goben zan bar masa ita insha Allah, Aysha karki manta komai nufin Allah ne ki rik'e min wannan banason kowa ya sani sai gobe zan fad'a musu da kaina, Faruq d'an uwana ne banason hanashi auren Hibbah ina k'ausa sosai zan iya sadaukar mishi da komai." Ta goge hawayenta tana girgiza kai "Yaya wata kusan tafi wata bazan iya had'a 'yan uwantaka ta dakai da shi ba, bazan iya jayayya da kai da mahaifinmu ba inda wani bare ne da saina hana yuwuwar abin amma tunda Kai ka yanke hukunci da kanka, Allah ya tabbatar mana da alkhari, muje na kaika kaga doctor." Ya yamutsa fuskq "ba komai kawai ki rakani gida bazan iya tafiya ni kad'ai bane, kinsan tuk'i saida nutsuw................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* "Uncle" ya d'ane jikinsa, d'agashi yayi cak yana juya shi suna dariya, tana tsaye kallonsu kawai tayi saita koma kitchen ta cigaba da aikinta. Ya sauke Nawaz ya bi bayanta kitchen d'in, ya tsunkule ta a gefen cikinta tayi zillo gefe fuskarta a d'aure "bana son abinda kake min bai kamata ba wannan ai wulakanci ne" idanunta suka ciko da k'walla ya ritsata yana yi Mata murmushi, idan da abinda ta a duniya to isgilancin da Faruq yake yi mata a duk sanda yazo gidan sai yaga hawayenta hankalinsa yake kwanciya, ya lakuce hancinta ta juya kai gefe "albishin na kawo miki Hibbah, wannan duk gangar jikin nawane nan da sati biyu za'a d'aura mana aure, iyaye sunyi magana kinga na zama naki kin zama tawa har *Abadan* maganar da akayi jiya kenan, Yaya mutum ne mai zurfin ciki na sani bazai fad'a miki ba ko da yake ke ba abokiyar hirarsa bace, nasan bakwa wata mu'amala idan banda ta gaisuwa tunda shi ba shiga harkar mutane yake yi ba, ni shiyasa ma zuciya ta tak'i yarda dashi har na d'ora wani zargi a akansa to amma na kasa gano gaskiya." A razane take kallonsa "Faruq idan mafarki kake to ka farka don wannan maganar shirmene irin naka, ta yaya ma ni zan aureka? Wani irin zama zamuyi dakai? Nasha fad'a maka iyayena Jabeer suka sani baza kuma su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63