Chapter 12
Chapter 12
da aka nannad'e da k'yalle tace "me ya sameki a goshi?" Kallonta Hibbah tayi lokaci d'aya taji tana burgeta ganin yarda take ba girman kai, gata da saukin kai tace "yankewa nayi." Tace "ayya allah ya sauwak'e, bara na kira muku momy din." Ta fada tanayin hanyar hawa benan. Su kuwa 'yan matan suna ganin Aunty'n tasu tabar parlor'n d'aya daga cikinsu tace "Saudat kinga matsalar Aunty Aysha koh, ta maida 'yan aikin gidan nan kamar wasu 'yan uwanta." Wadda aka Kira da Saudat tace "ai kedai bari Safiyya ni kaina ina jin haushin wannan abun." A tare suka juya suka watsawa su delu wani mugun kallo suka ja mugun tsaki suka cigaba da kallon su. Karan saukowa sukaji Wanda ya basu tabbacin momy'n suce take saukowa, kyakykyawar macece Fara take saukowa cikin shiga ta alfarma ta k'aso cikin parlor suka gaisa da delu Hibbah ma ta gaisheta. Momy tace "ai da ji nake baza kizo ba har na bawa Hadiza cigiya ta samomin wata," delu cikin girmamawa tace "wallahi hajiya bansami yarinyar da wuri bane," hajiya ta kalli Hibbah tace "to Allah yasa ba irin halinsu d'aya da dije ba, dan banji dad'in aikin dije ba Sam." Delu ta kuma duk'ar da kai cikin girmamawa tace "ba halinsu d'aya bama insha Allah, kuma ita wannan na kawota ne zatayi zama dindindin anan, don ko ganin gida ma baza ta dinga zuwa ba." Da mamaki akan fuskar momy tace "to saboda me delu?" Delu ta k'ak'aro murmushi tace "ai haka iyayen nata suka ce," momy tace"to Allah ya taya mu rik'o kenan sai aurene zai rabamu da ita." Delu tana yak'e tace "ai kuwa." K'walawa Hadiza kira momy tayi, saiga wannan Matar data bud'e musu kofa nan ta shigo da hanzari ta durkusa a gaban momy tace "gani hajiya," momy ta kalli Hibbah tace "Hadiza gatanan ki kaita d'akin ku, sannan ki nunnuna mata aikinta."Hadiza cikin girmamawa tace "to hajiya" ta kalli Hibbah tace "taso muje" mikewa Hibbah tayi tabi bayanta. Wata 'yar hanya sukabi ta parlor'n suka b'ulla wani dan fili daga gefe kuma d'akine, Hadiza na gaba Hibbah na binta a baya suka shiga ta nuna mata inda zatasa kayanta, suka fito suka nufi kitchen dama Hadiza girki take nan Hibbah ta shiga taimaka mata da yanke yanke. Su delu kuwa sun dan taba hira kafin delu ta tashi zata tafi aka Kira Mata Hibbah sukayi sallama ta huce............ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πππππππππ *RAYUWA* page1β£9β£to2β£0β£ *NA* *MAMYN NAJMAH* πππππππππ *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Komawa kitchen d'in tayi suka k'arasa girkin, bayan sun gama Hadiza ta zuba a kula tace Hibbah ta d'auka sukai parlor. D'auka tayi suka shiga parlor'n lokacin ma babu kowa a parlor'n, tsayawa tayi Hadiza tayi gaba ita kuma tabita a baya dinning area suka nufa Hadiza ta jere kayan akai tacewa Hibbah"ki rik'a lura da abubuwan da nakeyi don wannan duk aikin kine," Hibbah ta d'aga kai tare da cewa to. Haka suka k'are jera abincin akan dinning suka koma kitchen suka d'auki nasu Wanda Hadiza ta ware musu, d'akin da hadiza tace nasune suka koma Hadiza ta zuba musu sukaci tare. Hibbah sai taji matar ta burgeta yarda take janta a jiki ba kyara bare hantara, Hibbah tayi shiru tana tunani da tana k'auyensu da yanzu ta dawo daga islamiyya inna ta d'ora mata tallah, sai kuma ta tuna ashefa ta bar gidansu tana gidan gwaggo. Tana can duniyar tunani ta tsinci muryar Hadiza cikin d'aga murya tana cewa "Hibbah! Wai me yake damunki ne? Tunanin me kikeyi?" Numfashi Hibbah ta sauke tace "ba komai baba," Hadiza ta kalleta tace "a'a Hibbah da akwai wani abu, kinga fa abincin da kike ci kin dena, kin tafi tunani fa kuma hawaye a fuskarki ko dai kewa gida kike yi?" Da sauri Hibbah ta d'aga kai, Hadiza tace "ai sai hakuri a hankali ma zakiga kin saba da nan d'in musamman ma kika rik'e dokokin hajiya zaki zauna da ita lafiya don hajiya bata da wata matsala, sai dai yaranta wannan 'yammatan su biyu sune masu matsala, suma idan kika bi duk abinda suka ce miki suma baki da matsala dasu." Hibbah ta girgiza kai cike da gamsuwa tace "to baba na gode, amma menene dokokin hajiya da 'ya'yan nata?" Hadiza tace "gaskiya hajiya macece mai son tsafta bata son k'azanta ko kadan, sannan tana son mutum mai gaskiya da rik'on amana, tak'i jinin rashin kunya tana son taga kana mutuntata da yaranta, idan kikayi haka sai kiga hajiya na sonki wata k'ilama tasa ki a makaranta kamar yadda tayiwa dije gata tasa ta a makaranta ta d'auketa tamkar 'yar cikinta daga baya dije tazo tana yi Mata d'auke d'auke, har yakaita da d'aukar sarkar hajiya ta gold." Zaro ido waje Hibbah tayi tace "sata?" Hadiza tace "wallahi kuwa, shiyasa ma hajiya ta koreta," Hibbah ta girgiza kai tana mamakin wannan lamari can tace "insha allah zanbi duk dokokin hajiya kuma Zan kula da dukkan ayyukana." Hadiza tace "Allah yasa," "ameen" Hibbah ta fad'a tana mikewa ta d'auke plate d'in dasukaci abinci takai kitchen tare da wanko hannunta, Tana shigowa d'akin Hadiza tace "kizo kiyi wanka ki canza wad'an nan kayan, sannan wannan kanma ki wankeshi kizo nayi miki kitso na gaya miki hajiya fa bata son k'azanta," Hibbah tace "to" a zuciyarta kuwa cewa tayi baba Hadiza bakisan *RAYUWA*r danayi bane shiyasa kike ganin k'azantata, towel Hadiza ta d'auko mata sabo tace "ga wannan dashi zaki rika wanka" Hibbah ta amsa tare daa godiya. Kayanta ta shiga cirewa ta d'aura towel d'in da Hadiza ta bata ta shiga band'akin, tsayawa tayi kallon band'akin ya tsaru kamar ka kwanta, ta gama k'arewa toilet d'in kallo itadai bata ga ta inda ruwa zai fito ba sai wata 'yar tukunya data gani Fara da ruwa a kwance a wajen kuma wannan bata ga ta inda mutun zai tari ruwa ba. Hakan yasa kawai ta juya ta fita daga toilet d'in, ta nufi kitchen ta Kira Hadiza ta nuna mata yadda zata yi. Hanyar kitchen d'in ta nufa cikibis sukayi da Faruq ta sunkuyar da kanta tare da matsa masa ya huce ji tayu shiru mutum bai huce ba hakan yasa ta d'ago kanta don ganin me ya tsayayi. Gani tayi ya sha'afa yana kallon ta, kallon idanun sa tayi sannan ta kalli jikinta gani tayi Ashe kirjinta ya k'urawa ido yana kallo. Sai a lokacin ta tuna ashefa towel ne a jikinta kuma shima tsayinsa bai huce iya gwaiwarta ba da sauri ta juya zata koma d'akinsu, shima Faruq cikin sauri ya janyo hannunta ta fad'a jikinsa wata gigitacciyar k'ara ta saki wanda hakan yayi sanadiyyar fitowar Hadiza da sauri daga kitchen tayo dakin nasu inda anan ne taji k'arar. Aunty Aysha ma da take parlor a zaune tajiyo k'arar itama cikin sauri tayo wajen. Tsayawa Aunty Aysha da Hadiza kukayi suna mamakin yadda Faruq ya rukunkume Hibbah suna kokawa, yana kokarin zare towel d'in dake jikinta. Kasa jurewa Aunty Aysha tayi ta buga masa wata muguwar tsawa, da sauri Faruq ya cika Hibbah, Hibbah wadda hawaye kebin fuskarta da sauri tayi d'akinsu. Aunty Aysha ta karasa kusa dashi ta yarfa masa Mari tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63