Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da dariya suka cigaba da hira har dare ya raba sannan sukayi bacci oyiza batai maganar sallar magrib da isha ba, wa ma yasani ko tayi na safe da rana ohooo...... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:33] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tun daga ranar suwaiba ta samu gurin zuwa su zauna suyita hira suna shewa suna kulle kullensu dan ta kuntatawa zeenatu, anan suwaiba ke yini In ba ranar girkinta bane, ko kallon zeenatu ta daina yi, saboda ita a ganinta tayi kawa wacce zata ci arziki da ita kamar yadda ma'u ke ci da zeenatu, (bata san bomb ta samu a madadin kawa ba).. Watansu uku da aure oyiza bata fara nuna komai na halin tsafinta ba, sai dai abinda ke bawa alhj basheer mamaki game da ita shine rashin sallarta, ko ya matsa mata tayi sallah to fa zata san yadda tayi ta zille dan baza tayi ba, gurin zeenatu kuwa mugun kyankyamin cin abincin oyiza takeyi saboda sam bata yarda da musuluncinta ba, ko sun haďu a dinning ana cin abinci sai tace ita yanxu abinci mai nauyi bata mata cikinta yakeyi,, a cikin wannan lokacin ne oyiza ta fara laulayi mai zafin gaske, komai bata iya ci, haka ta tsani kamshin gidan gaba ďaya, tunda alhj basheer yasan ciki ne makale jikin oyiza shikenan duk wani kula da soyayya ta duniya ya ďauka ya daura mata, babu dama zeenatu tayi abu in oyiza tace bata son kamshin shi to fa shikenan zai hauta da faďa sosai kamar tababbe, suwaiba ce ke shigowa ta kula da ita suyita yada habaici dan zeenatu taji haushi, duk da zeenatu na jin haushin abin amma sai ta danne ta dinga tambayar oyiza ko akwai abin da takeso, ko kallonta oyiza batayi bare ta bata amsa, abubuwa suka hadu sukayi ma zeenatu yawa, gashi sam mijinta ya juya akalarshi gurin kula da oyiza a cewarshi, gurin Ma'u da amaryar da Alhj bara'u yayi kadai zeenatu ke samun sauki, Kayan baby babu wanda alhj basheer bai siyo ba a nan nigeria da waje, kuma duk kayan maza ya siya dan a scaninng an tabbatar mishi namiji ne, itama chummy ta tabbatar mata namiji zata haifa, gaba daya oyiza ta gama wasa wukarta dan ta gama hada plan din yadda zata mallake gidan da duk wasu kadarori na alhj basheer, Cikin oyiza ya kusa wata tara alhj basheer ya ďauketa suka tafi india acewarshi zasu fi samun kula ita da babynshi, tafiyarsu ita tasa zeenatu tasamu sauki take bacci da adduointa cikin kwanciyar hankali, da rana su ma'u da Abida amaryar Alhj bara'u su shigo su ďebe mata kewa da bata shawarwari duk da Abida itama ba isashshen lafiya gareta ba saboda cikin dake makale jikinta na wata hudu, A daren ranar talata ta idar da sallar tana shirin kwanciya taji ringing din waya, daukar wayar tayi taga alhj basheer ta dauka cikin mamaki dan rabonshi da ya kirata har ta manta, sallama ta mishi ya amsa murya babu walwala tace ya mai jiki, yace da sauki ta sauka lafiya, zeenatu ta washe baki tace Allah ya raya ya kuma bata lafiya, me muka samu, kukan da oyiza ke yi ya hana shi bata amsa, kuka takeyi sosai tana fadin ya za'ayi ace ya' mace ta haifa, tsawa ya daka mata yace to ubanwa kike tunanin ya canza miki, ko wannan din ke kika bawa kanki, ki rufe min baki kar ranki ya baci, zeenatu ta kashe wayar da sauri ta hau gado ta dukunkune (nidai bansan me ke ranta ba a wannan lokacin, farin ciki ne ko kuma tausayin oyiza,, masu kishiya su bamu amsa plss..).. Satinsu biyu a india suka dawo gida cikin koshin lafiya,, tun acan ya raďa mata sunan mahaifiyar oyiza wato Salamatu (ummu Salma) tunda suka dawo makota ke shigowa yi mata barka, suwaiba sai tausarta takeyi akan gara ita tana haihuwa ba juya bace, wannan kalaman na suwaiba suna matukar sosa ran zeenatu su ke sata kuka a kullum dare da rana tana rokon Allah akan ya bata farin cikin rayuwa itama, dan haihuwa farin cikin rayuwa ne, in ka haihu ka wuce bakin cikin duniya da lahira, ya Allah ka azurta wadanda basu haihu ba da ya'ya masu albarka cikin gaggawarka bata shaidan ba, wadanda suke dashi kuma Allah ka shiryar mana kuma ka tayamu raino ameen thumma ameen..... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣2⃣ By Aysha Ya'u Kurah Shekarar ummu salma uku, in ka ganta sak uwarta gata katuwa kamar renon agric, tana matukar samun kulawa gurin mahaifinta dan ba kananan kudi yake kashe mata ba, a wadannan shekarun banda karfin imani da salatin annabi da tuni zuciyar zeenatu ta buga saboda ko kallo kwakwkwara tayi ma ummu salma to fah zata fashe da kuka ta dinga nunata, shi kuwa alhaji basheer babu bincike babu komai zai hauta masifa wani lokaci harda gorin haihuwa, zeenatu sam ta kasa gane kan mijinta saboda kullum alamuranshi kara tabarbarewa sukeyi sam babu sauki a tare dashi game da ita dan ko hanyar dakinta baya bi, ta ma manta rabon da su kebe tare a matsayin mata da miji, Oyiza kuwa yanzu burinta ta samu ciki amma kafin ta samu sai ta shirya tsaff saboda wannan karan bazata taba yin sakacin haihuwar ya mace ba, sai kace ita zata bawa kanta haihuwar,, ( kaii Rashin ilimin addini shine babbar cuta a rayuwar dan adam) A cikin kwanakin kullum dare suna gurin meeting duk dan saboda ta samu haihuwar ďa namiji, chummy ce ta kalleta bayan ta gama duk abinda zatayi na tsafi, tace oyee zaki haifi ďa namiji amma sai kin bamu jinin yaro karami namiji kar ya wuce 2yrs, oyiza ta dafe kanta tana tunanin inda zata samu ďa namiji, chummy tace ki kokarta oyee wannan bazai miki wahala ba in kikayi la'akari da yanzu iyaye na sakin yan 1 nd half year a titi da sunan wasa,, sweet kadai zaki bawa yaro shikenan,,, kije ki kawo zuwa jibi sai muyi aiki mu gama cikin satin nan.. Munafurci dodo ne tabbas mai shi ya kan ci,, Oyiza ce zaune a tsakar gida tana kallon salma na wasa cikin motarta da a kiyasi zata kai 350k dan har petur ana zuba mata ta fita yawo da ita cikin unguwa, suwaiba ce ta shigo rike da Abulbait tana ma ummu wasa, zama tayi a kasa kusa da kafar oyiza ta fara mata kirari, nan da nan oyiza ta saki fuska suna hira tana bin Abulbait da kallo, oyiza ta kalli suwaiba tace wai ni ko yanzu abul ya kai shekara uku, suwaiba tayi dariya tace wane uku, shekararshi 1 da wata takwas, oyiza ta haďiye miyau ta shafa kanshi tace naga yayi saurin girma ne, suwaiba cike da murnar an yabi ďanta tace a hakan, ay ko ni ganinshi nakeyi a motse kamar fara, oyiza tace aiko ya girma wallhy bari in bashi sweet kema akwai wata yar kyautar da zan miki, suwaiba cikin murna ta mike tana godiya ta bi bayan oyiza jiki na rawa, dubu ashirin oyiza ta bata tace ta kara jari sannan ta bare sweet ta bawa Abulbait tace shanye

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});