Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

miyau dakyar tace kana ta min magana a cukurkuďe a gurin wa zan samu jika, alhj basheer yace kina da wani dan da ya wuce Affan ne, oyizah ta saki baki tace ciki matarshi ke dashi, yace kwarai kuwa, kinga rabo ko, ranar da aka sa aurenta da jabeer a ranar aka daura auren da Affan kuma a ranar Rabo ya rantse kanshi, oyizah da zufa ke keto mata ta ko'ina tace umm hakane yanzu ta farfaďo kenan, alhj basheer yace garau ma tana can na barta a zaune, oyizah ta mike tace to bari a haďa mata abinci a kai mata ko, alhj basheer yace ya kamata kam, ki haďa mata duk wani abun da kika san me ciki na bukata in ma babu ayi min magana dan Allah, oyizah ta wuce tace to, Zama tayi a kasa a dakinta ta zuba uban tagumi tana tunanin yadda akayi ta samu failure a aikin jiya, da kuma yadda akayi har ciki ya shiga jikin yarinyar nan, inaaa bazai yiwu ba dole cikin nan ya fita, dole ne in kashe yarinyar nan dan wallahi bazan yarda ta sake dawowa gidan nan ba, mikewa tayi zubur ta wuce kitchen ta shiga shirya abinci daidai cin mutum daya, tana yi tana zancen zuci dan bata taba yin aiki irin haka ta samu failure ba.. Gab da la'asar kaka liman ya bayyana a asibitin, a zaune ya samesu hajja ta tasa mata abinci a gaba tana ci, fuskar hajja dauke da fara'a ta gaishe shi ya amsa yana kallon Afeeyah, Afeeyah ta sunkuyar da kanta ta gaishe shi ya amsa yana murmushi yace ya jikin kuma, Afeeyah tace da sauki, ya zauna a kan kujera yace to Allah ya karo sauki, suka ce ameen ita da hajja, saida suka dau kusan minti biyu shuru sannan ya kalli hajja yace dan Allah hajja in bazaki damu ba ko zaki dan bamu guri, Hajja ta mike tace haba babu komai wallhy ta fita daga dakin, Bayan fitar hajja da kamar minti uku kaka liman ya kalleta yace ya mai gidan naki, Afeeyah tace yana nan lafiya kaka, kaka liman yace lafiyar ciki ko ta waje, Afeeyah ta dago cikin rashin fahimta tace ban gane ba kaka, yace ina nufin wace irin lafy, lafiyar koshin lafiya ko kuma ta duka harda kwakwalwa, Afeeyah tace lafyr koshi kaka, sannan lafiyar kwakwalwarshi ma ina tantama akanta, wani lokacin in yayi abu kamar cikakken me lafy baya mintina kuma sai ya koma kamar da, kaka liman yace to yaya kika fahimci mutanen gidan, ina nufin a tunaninki wane irin zama sukeyi da yaron nan, kina ganin suna kaunarshi tsakan--- sammm ta katse kaka liman, tace muguwar tsana sukayi mishi wallhy, amma a gaban daddy sai su nuna basu da kamarshi, sannan kaka bata barinshi yayi sallah, duk wata ibada bata barinshi yayi, sannan kaka jiya da dadd--- yayi saurin katseta yace tambaya daya nayi miki, bari in yi miki cikakkun bayanai akan abubuwan da baki fahimta ba tukunna sai mu shiga wani, mijinki ba lafiyar koshi kadai gareshi ba harda ta kwakwalwa, tambayarki zanyi,? tsakaninki da Allah kinajin zaki iya yin duk abinda ya dace domin ki kubutar da mijinki daga wannan halin da yake ciki,? Afeeyah ta gyada kanta tace zanyi kaka,,, yace yauwa yar albarka, Ki sani mijinki ya samu saukin tabuwar da kwakwarshi tayi sai dai kuma azababben sihirin da ake mishi shi ke kara dagula kwakwalwar ya rasa fahimtarshi ya dinga yin abu kamar yaro, wani magani ake bashi wanda idan yayi awa shida bai sha ba zai iya dawowa mai lafiya amma ba sosai ba saboda akwai wasu tsibace tsibbacen da aka birne a cikin gidan wanda gano su sai ansha matukar wahala, duk ranar da aka hako wadannan asiran to wannan ruwan maganin ya daina tasiri a jikinshi domin duk wata tabuwar kwakwalwa zata barshi, karki ce sihirin wasa akayi mishi, wannan na gasken gaske ne wanda yake da matukar wahalar karyewa, kin fahimceni ko, Afeeyah ta gyaďa kanta tace ay kaka duk abinda aka ce min matar nan zatayi bazan musa ba saboda ni ganau ce ba jiyau ba,,, shigowa dakin sukaji anyi babu sallama, da sauri suka waigo dan ganin ko waye....... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah Oyizah suka gani tsaye idonta kyarr kan Afeeyah, gefenta kuma salma ce rike da basket din abinci, gaban Afeeyah sai faduwa yakeyi a zuciyarta tana adduar Allah yasa bata ji tautanawarsu ba, gyaran murya kaka liman yayi ya kalli oyizah yace an wuni lafiya, da sauri ta kauda kanta tace lafiya lau ta karaso gaban gadon Afeeyah jikinta a mace tace ya jikin, da sauki Afeeyah ta fadi ba tare da ta kalleta ba, salma kuwa ajiye basket din tayi ta koma gefe tana cika tana batsewa, mikewa kaka liman yayi ya kalli Afeeyah yace bari in koma, Kiyita "hasbunallahu wa ni'imal wakil" saboda maganin musibun duniya, Allah ya kara sauki ya kuma inganta abin dake cikin ki, Afeeyah tace ameen kaka nagode yaushe zaka dawo, yace too zan dai gani amma ay bazan koma ban sake dawowa ganin jikin naki ba, tace to sai ka dawo kaka, ya kalli oyizah da kanta ke kasa yace to hajiya sai anjima ko, tace to sai anjima, har ya fita ya kuma lekowa yana kallon kwandon abincin yace "ki danne kwadayinki, in har ya taso miki to ki tambayi goro a baki domin kwantar dashi kin gane ko" Afeeyah ta kalli kwandon nan take ta gane manufarshi tace to kaka nagode, Oyizah da ta tabbatar kaka ya tafi sai ta dago kanta ta zauna ta dafa Afeeyah tace sannu, amma jikin da sauki ko, umm kawai Afeeyah tace, oyizah tace kin ci abinci kuwa, Afeeyah ta yatsina fuska tace bana iya cin abinci amai yake sani, oyizah tayi murmushin mugunta tace shiyasa na dafo miki abincin da nasan masu ciki naso, salma ďan zubo mata, Afeeyah tayi saurin cewa a'a ta barshi doctor yace a daina bani abinci saboda aman na wahalar dani, oyizah tace doctors din nan sun cika iyayi manta dasu kici babu aman da zakiyi, Afeeyah tace saidai ko zuwa anjima dan yanzu bacci nake ji, oyizah zata kara magana cikin bacin rai salma ta katseta tace haba mummy dole ne, ji yadda kike wani pettn dinta tunda tace baza taci ba ba sai ki kyaleta ba, cikinta,,,, oyizah ta harari salma tace baki san me lalurar ciki sai an matsa mishi yake cin abinci ba, ko so kikeyi in bari ta wahalar min da jika, Afeeyah ta kwanta tace uhmm, oyizah tace rabu da salma kinji bata san lalurar ciki ba shiyasa, salma tayi tsaki ta tashi ta fita daga dakin tana mamakin yadda mummy ke lallaba wannan yar iskar yarinyar, babu yadda oyizah batayi ba akan Afeeyah taci abincin da ta kawo amma firr taki, har hajja ta shigo tasa baki Afeeyah tace ita sam yunwa ne bataji kuma tana ci zatayi amai, oyizah ta boye bacin ranta tace to hajja anjima ki tabbatar taci saboda bai kamata mai karamin ciki ta dinga zama da yunwa ba, hajja tace karki damu in shaa Allahu zata ci, oyizah ta dan

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});