Chapter 11
Chapter 11
ta tabbata, Allah ka tabbatar da wannan maganar kasa Abida ta faďi a bakin mala'iku, Abida tace ameen zeenah, tashi zeenah tayi ta shige ďaki ta cire rigarta tana kallon kanta a mudubi, kirjinta ne kadai ya ciko amma mararta a shafe take, maida rigarta tayi tana adduar Allah ya tabbatar da wannan abun,, Washe gari tun asuba ta gama shiri dama bata rintsa ba tana ta addua, karfe takwass dai2 ta fito suka wuce dan mai gidan baya gari sunyi tafiya shi da oyiza mai laulayi wai batasan warin gidan da nigeriar gaba ďaya, (samun guri), AKTH suka nufa, basu wani sha wahala ba saboda akwai kawar Abida a asibitin, test din jini akayi mata aka tabbatar da tana da ciki, scanning ppr aka bata suka je tayi scanning inda ya nuna makalallen ciki na wata hudu, '"HAMDAN KASIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN FIHI,"" abinda zeenatu ke fadi kenan hade da kuka, saida suka gama komai a asibitin Abida ta maidata gida cike da murna ta tsaya tayi wa su Ma'u albishir sannan ta wuce aiki, Hajja da ma'u a lokacin suka shigo taya ta murna, har ta ďaga waya zata kira alhj basheer ta fada mishi sai wata zuciyar ta haneta, haka gida ma so takeyi ta musu surprise, Kula sosai take bawa cikinta da ya kai wata biyar har ta fara zuwa awo alhj basheer da oyiza basu dawo ba, gidan Abida take zama suyi hirarsu lokacin ta haifi ďanta namiji mai suna JABEER, Cikin zeenatu na wata bakwai su oyiza suka dawo itama da nata cikin watanshi bakwai, fitowa tayi cikin hijab tana musu sannu da zuwa, alhj basheer ne kadai ya amsa babu yabo babu fallasa, ta kalli salma tace ummu ya hanya, salma tayi banza da ita suka wuce daki ita da mamanta, saida alhj basheer yayi wanka ya huta sannan ya fito cin abinci, zeenatu ce tayi serving dinshi tana mishi hira yana amsawa jefi2, bayan ya gama cin abincin ne ta fara mishi magana cikin hikima, tace ranka ya dade kudi nakeso, ya yatsuna fuska yace me zakiyi da kudi, ta sunkuyar da kanta kasa tace siyayya nakeso inyi ma kyautar da Allah ya bani, cikin rashin fahimta yace ban gane ba, ta daga hijab din jikinta ta dauko hannunshi ta ďaura kan cikinta tace Allah ya azurtani da ciki har na tsawon wata bakwai, "karaf a kunnen oyiza da ta fito cin abinci," fuskar alhj basheer ta kasa boye farin cikin da yake ciki a wannan lokacin, janyota yayi ya zaunar da ita kan jikinshi sam bai kula da oyiza ba, ya kalleta yana shafa cikin da ya dan taso yace da gaske zeenah, ta gyada mishi kai, yayi murmushin jindadi ji yakeyi kamar wannan ce haihuwar da zaiyi ta fari, yace Allah ya fito min da abinda ke cikin nan kuma yasa namiji--- ta maza ta toshe mishi baki tace namiji da mace duk Allah ke hallitarsu, muyi fatan samun masu albarka shine kawai yallabai, yaji wani nutsuwa ta ratsashi yace hakane Allah ya bamu masu albarka, "mtswwwwwww" sukaji an ja tsaki mai karfi suka waiga suka ga oyiza tayi gaba tana huci kamar zakanya, kau da kanshi yayi ya cigaba da kallon cikin zeenatu yace gobe ta shirya suje siyayya da asibiti a kara duba lafiyarta, sun dade suna hira cikin jin dadi ya ma manta da wata oyiza a rayuwarshi... Oyiza kuwa tana shiga ďaki ta maida salma ďakinta, ta hau kan buzun tsafinta sai gata ta bayyana gaban "chummy" idonta jawur take fada ma chummy halin da take ciki, chummy tayi iya yinta da duk wasu siddabarun da zatayi tace oyee wannan cikin bazai zube ba, cikin jikinta na tare da kariyar adduoi sosai sai dai ki bari in ta haifeshi sai kisan abun yi, cikin tashin hankali tace "my lord" to idan ta haifi namiji fa, chummy tace sai kinso ya rayu in ya fito duniya, oyiza hankalinta ya ďan kwanta tayi sallama da chummy ta bace ta nufi gida.... Ciwo takeji sosai amma hakan bai hanata ci gaba da aikinta da tasbihi a bakinta ba, wani irin Murďawa mararta tayi ta tsuguna da sauri tana faďin "YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKHA ASTAGITHU ASLIHLI SHA'ANI KULLAHU WALA TAKILNI ILA NAFSEE ĎARFATU AYNUN" da dai taga abun kamar gaba yakeyi ta mike tayi hanyar parlo tana maimaita adduoi a bakinta, oyiza na zaune tana cin abinci zeenatu ta shigo da kyar, tace dan Allah safiya ki taimak--- ta kasa karasawa saboda wani irin nishi mai karfi da yazo mata, oyiza tayi tsaki ta juya tana adduar Allah yasa ki mutu ke da ďan cikinki, zeenatu kuka sosai takeyi ga wani ruwa dake bin kafarta, sallamar Abida taji nan taji kamar an sauke mata zafin wani bangaran, da sauri Abida ta karaso ta ajiye jabeer tace haba zeenatu ay da sai ki kirani a waya, zeenatu ta runtse bakinta ta rike hannun Abida dake kiran Ma'u a waya, da sauri ma'u ta shigo suka kamata, Abida ta kalli oyiza tace dadin abin nakuda Allah bai ďauke wa uban kowa ba, kowacce yar iska zata dandani nata in lokaci yazo, oyiza ta harzuka matuka ta mike tana bala'i suka fita sukayi banza da ita, drivrn gidan ya karaso da sauri suka wuce asibiti, Suna shiga Allah ya taimaketa batayi wata doguwar nakuda ba ta haifo ďanta namiji kyakykyawa mai kama da iyayenshi, likitoci suka shirya baby suka kimtsa mamanshi suka kwashe mata jini suka turota dakin hutu, murna a gurin su ma'u ba'a cewa komai, Abida ta kira Alhj basheer tayi mishi albishir, murnar da yayi a lokacin ba mai faďuwa bace, saida yaje gida ya shirya sannan ya fito zai tafi asibitin, oyiza ta fito rike da kugu tace ina zaka je, ya fadada fara'arshi yace hospital zeenatu ta haihu, oyiza ta kauda kanta tace Allah ya raya, yace ameen, har yayi gaba, ta tuna ta kwala mishi kira ya tsaya tace me ta haifa, yace baby boy, wani irin murdawa mararta tayi cikin ruďewa tace namiji kenan ta haifa,, yace eh mana, ya shiga mota cikin farin ciki ya wuce ya barta tsaye kamar an dasata hawaye masu zafi suna kwaranya a idonta.... ayshakurah.mywapblog.com Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah Ciki ta juya tana tafiya da kyar, ga bakin ciki ga kullewar mara, a gado ta kwanta tana kuka sosai kamar wacce akayi ma mutuwa, sai da tayi kuka ma'ishi sannan tayi shuru da tunanin itama fa cikin gareta kuma chummy ta bata assurance din namiji zata haifa, yanzu kawai abinda ya rage mata shine tasan yadda zatayi ta kashe jaririn nan tun kafin ya girma yasan kanshi, da wannan tunanin zuciyarta tayi wasai ta mike ta shiga wanka.. Kwanan zeenatu huďu da haihuwa kullum da daddare alhj basheer na makale a ďakinsu, duk wanda ya ganshi a kwanakin yasan farin ciki ne cike da zuciyarshi, haka mai jego na samun kulawa daga gurin makotanta da kanwar kakarsu Yadikko da tazo daga cameroon, a ranar da suka cika kwana shida da yamma sunyi wanka ita da baby yadikko ta debo rushi tasa garin "habbatis sauda" a ciki tana sa hannunta a hayakin in ya dau zafi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61