Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mulki akayi kenan, ke Amirah koma gurinki itama ta dawo gurinta, Amirah ta buďe kofar zata fita Afeeya tace saidai fa mu zauna tare a baya, amirah tace kaji ko yaya, wallhy tun ďazu nake ce mata ta dawo nan taki, kallonta yayi ta mudubi yayi dariya yace amirah shigo muje, suna isa kofar gida ta buďe motar ta shige ba tare da tabi takan kayan da ya siyo musu ba, Amirah ta kwashi nata kayan ta shige gida itama, jabeer ya gyara parking ya kwaso kayan ya fito dasu ya shiga gidansu, kwance ya sameta can karshen gadon hajja tayi ruf da ciki hajja na mata magana tayi banza da ita, jabeer ya zauna bakin gadon ya gaida hajja ta amsa tace yau kuma me kayi ma mutuniyar taka, jabeer yayi dariya yace wallhy babu abinda nayi mata rigima ce kawai, Afeeya ta ďago idonta a kankance tace har kana wallhy, ya kalleta yace to me akayi, tace nima bansani ba, ta mayar da kanta kan katifar ita kanta bata san me zata ce ya mata ba ita dai tasan taji masifaffan zafin ganinshi da tayi da wata, juyin duniya yayi ta faďa mishi abinda yayi mata amma sam taki ďago kai ma bare ta bashi amsa, hajja taja tsaki tace tashi ka tafi ka rabu da ja'ira da kanta zata nemeka, in ba iskanci ba babu abin da aka ma mutum ya hau fushi, to in kin ga dama ki fashe,, jabeer zaiyi magana ya ji wayarshi na ringing, ya mike da sauri yace hajja dan Allah ki rarrasheta kafin na dawo tun dazu Affan ke jira na, hajja tayi tsaki tace ni ban iya wacce ka iya ba, ya fita yana dariya. .. Sai bayan isha suka rabu Affan ya wuce gida, ya na sa kafarshi cikin gidansu yaji muguwar faduwar gaba, wucewa ciki yayi a hankali jikinshi a mace ya shiga dakin mahaifiyarshi, zama yayi ya dafe kanshi yana jiranta dan a tunaninshi tana bayi ne,, wani irin ihu yaji mai firgitarwa ya mike da sauri yana kasa kunne yaji daga inda ihun ya fito, kafa kunnenshi yayi a jikin toilet yaji ba alamar mutum a ciki, umma... umma.. ya kira sunanta sau biyu yaji shuru ya tura bayin, juyawa yayi da sauri da yaga bata yana kwala kiranta, muryoyin mutane ya dinga ji a can saman gidansu gurin shan iska, a hankali ya karasa gurin yana leke a tsorace saboda muryoyin da yaji harda ta maza a ciki, wani razanannan ihu ya saki haďe da faduwa kasa sumamme sakamakon abinda idanuwanshi suka gani..... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah A gigice oyiza da wasu maza suka saki zeenatu da babu alamar numfashi a tare da ita ta faďi timm a kasa, kan Affan sukayi da gudu oyizah ta ďago shi cikin tashin hankali tana faďin shikenan asirina ya tonu, na shiga uku na lalace, wani bakin kato ya yarda wuka da farin kyallen hannunshi yace yanzu ya zamuyi kenan, dayan cikin dakewa yace mu gama da mamanshi sai mu dawo kanshi, oyiza ta girgiza kanta tace Nooo mu fara dashi tukunna saboda kar ya farfaďo ya tona min asiri, bakin katon da naji sun kira da "BULADUNA" yace yanzu me kike so mu mishi, oyizah ta runtse idonta a zuciyarta tace "help me my lord", cikin mintina uku dabara tazo mata ta mike da sauri tace ku kama min shi, cikin rashin fahimta sukace ina zaki kaishi, ta nuna kasa da hannunta tace anan zai karasa, kunga babu wanda zai zargeni za'a ayi tunanin faďowa yayi by mistk,, A tare suka haďa baki sukace Good idea, gaskiya oyee u are very sharp shiyasa kungiya take ji dake, tayi murmushi tace "Lts make it snppy", kar wani yazo ya cim mana thou nasan ba kowa a gida, cikin rashin imani da rashin ganin tsawon ginin bene hawa huďu suka wurgo Affan ta kai,, su kansu saida suka runtse idonsu saboda ganin tsayin gurin amma dayake zuciyarsu a kangare take nan da nan suka sake suka juyo gurin farin kyallen da zeenatu take, a firgice suka haďa baki suka ce ina ta shiga, oyizah ta kwalalo ido tana duba ko ina a gurin amma basuga koda sawun kafar zeenatu ba bare ita,, hankalinsu yayi masifar tashi suka shiga duba ko'ina na cikin gidan amma basuga zeenatu ba, oyizah ta buga tagumi tace to ina ta shiga, bana tunanin da kafarta ta tashi saboda ko sanda Affan ya ganmu Kurwarta na gurin chummy, to waye zai dauke gangar jikinta? Buladuna yace oyee kin tabbatar babu kowa a gidannan, tace babu kowa, su farida sun fita sannan na aiki mai aikinta guri mai nisa I don't think ta dawo kuma ko ta dawo ay baza ta hawo nan ba, dayan cikin kosawa yace mu tafi kawai tunda mun samu abinda mukeso me zamuyi da gangar jiki, buladuna yace hakane, lets go oyee, cikin rashin kuzari ta bisu kan buzun tsafinsu suka bace daga gidan.. Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da chummy tace kurwar zeenatu ko 5mints baiyi ba ta nemeshi ta rasa, oyizah idonta yayi jawur tace to ina yaje,? kodai ya koma jikinta ne, shikenan asiri na ya tonu,,, Chummy tace calm down oyee, duk inda take yanzu hankalinta baya jikinta, saidai tana tare da wacce take mata addua yanxu haka, wannan dalilin ne kadai ya hanani dawo da ita, amma zansa suyi nesa sosai kuma zanyi mata abin da har ta mutu bazata taba motsi ba bare ta tashi ta dawo ta tona mana asiri, oyizah ta dafe kanta tace my lord wacece wacce suke tare yanzu ďin, chummy tace na kasa gane ko wacece, but koma wacece tanada kusanci da gidan, oyizah ta shiga kogin tunani, a zuciyarta tace to wacece wannan za ta dauke zeenatu, ita dai tasan babu wacce keda kusanci da zeenatu sai Abida to ko Abida ce ta dauke ta, wata zuciyar tace to ta ina abida ta shigo gidan da daddare, ta dinga tunanin da baida amsa ta kara kallon chummy cikin tsananin damuwa tace my lord ya akayi har ta samu damar guduwa,, Chummy bata iya bata amsa ba ta kalli wani katon glass din da ta tura Fanne da Fanna tayi kwafa cikin takaicin abinda sukayi mata, dariya fanne tayi tace munci dubu sai ceto, sai dai ki rufemu anan dan wallhy indai muna bude babu wani rai da zai kara salwanta a gurinku, oyizah taji kamar zata shakesu sabo takaici amma babu hali, ta kalli chummy tace my lord ya kamata a gama da yarannan if not zasu dinga bata mana aiki, chummy tayi murmushin mugunta tace very soon oyee,,, saida suka gama tsaface tsafacensu sannan kowa ya bace itama '"chummy" ta tafi gurin jigajigan matsafa na gaba da ita dan samo sababin lakanin tsafi... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tsaye take cikin zauren gidansu tana leken kofar gidansu jabeer ko zata hango shi, tun bayan magriba take tsaye a gurin amma har bayan isha'i bata hango inuwarshi ba, juyawa tayi zata koma ciki kamar zatayi kuka taji an rike hannunta

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});