Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shaidan ne da kuma ganin mummy nayi, Affan ya janye kafarshi ya galla mata harara, cikin tsawa alhj basheer yace tashi ki bamu guri yau dinnan zaki bi uwarki dan ban sani ba ko ke din ma ta tsafin ce, fareeda ta rushe da kuka tana bashi hakuri, a hankali zeenatu tace alhj laifin wani baya shafar wani, duk wanda yaga farida yaga jininka dan haka hannunka bazai rube ba ka yanke ka yar ba, alhj basheer yayi saurin cewa saidai kuwa in bai isheni da wari ba, yanzu ke kina so in zauna da jinsin matsafa a gida, Baffa yace bashiru hakuri zakayi ya' dai taka ce dan haka dole ka riketa ku koya mata tarbiyar da addini ya koyar kuma ku aurar da ita, nan suka cigaba tattauna maganar cikin tsananin al'ajabi.... Cikin tashin hankali oyizah ta bayyana a gurin tsafinsu, kuka sosai takeyi a gaban chummy tana faďa mata duk yadda akayi har dawowar zeenatu da samun saukin Affan, chummy ta kalli oyizah cikin mamaki tace ya akayi haka ta faru, oyizah tace nima ban sani ba, komai na kayan aikina an kwasheshi a karkashin gado babu komai a gurin sai kasa, sai kuma kwalbar nan da yan iskan yarannan suka fasa nasan shiyasa zeenatu ta farfaďo, chummy tace na sakeyin wacce tafi tada karfi kin ganta can, oyizah cikin mamaki tace to ya akayi haka, chummy tace ni nafi mamakin na dakinki da wanda kika birne a bakin damo, oyizah tayi saurin ďago kanta tace nasan wanda zaiyi min wannan aikin, wannan yar iskar yarinyar ce zatayi min, wallahi I will not spare her, yanzun nan zanje asibitin da take in kasheta, chummy tayi murmushi tace daďina dake garaje, bakya tunani kafin kiyi abu, waye ya faďa miki suma yanzu zasu zauna, , ai sun riga sun san sirrinmu so sai munyi da gaske ta karkashin kasa musa ki koma gidanki sai ki aiwatar da ayyukanki cikin kwanciyar hankali, oyizah ta gyada kanta tace wallhi wannan karan mai zafin zanyi duk saina kashesu in mallake alhj da dukiyarshi muyi zaman mu tare har karshen rayuwarmu,,, chummy tace yauwa ashe kin gane, yau da daddare zamu fara aikin, kinsan akwai ďan tsoho da kika kawo to dashi za'ayi miki aikin, yanzu tashi muje gurin Dodo BELAH mu dawo kafin lokacin meeting yayi, oyizah ta mike zuciyarta wasai dan a tunaninta komai nata zai koma normal tunda CHUMMY tayi assuring dinta,,, oyizah sarkin sa'a........ Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah Kwance take kan kirjinshi ta cukwikwiyeshi tana kuka mai ban tausayi tana faďin "meyasa ka tafi ka barni na tsawon lokaci, meyasa baka daukeni mun tafi tare ba ka barni cikin wannan wahalalliyar duniyar mai cike da azzalumai marasa tsoron Allah, ta tsunguna a kasa kukanta ya tsananta tace dan Allah yaya jabeer karka sake tafiya ka barni, ba karamin wahala nake sha ba saboda rashinka, I grew up in your arms plss led me die in it, plsssss, ďagota yayi suna kallon cikin idon juna taga wani haske mai matukar kyau a cikin kwayar idonshi, a hankali taji yana faďin tafiyata bazata taba zama wahala agareki ba, naso kasancewa tare dake amma Allahn da ya hallicemu bai halicceki dan ni ba shiyasa ya ďaukeni domin ki kusanta da wanda yake makusanci na hakika a gareki, dama ni ba mazauni bane zuwa nayi in nuna kamannina in koma ga ubangijin talikai, tabbas nasan lokacin da nake da rai baki da wata matsalar rayuwa, yanzu kuwa nasan ko baki gama sanin meye rayuwa ba kinsan kadan daga ciki, mu'imuni ako da yaushe Allah na jarabtarshi ta kowane bangare, duk wanda ya kansance cikin farin ciki a kullum to tabbas ya binciki kanshi domin duniya kurkukun mu'imuni ce sannan aljannar kafiri, kafiri marar tsoron Allah, ko wanda ke sabawa Allah shi kaďai ne ke samun farin ciki marar yankewa a duniya, akwai lokacin da zamu shiga farin ciki amma cikin lokaci kalilan sai bakin ciki ya maye gurbin wannan farin cikin, to ki sani duk musulmin dake yawan shiga cikin jarabawar Allah lallai ba karamar soyayya bace tsakanin wannan bawan da Allahn shi, domin shiga kunci ga musulmi kankarar zunubi ne, wasu kuma zaki ga basu da wata damuwa komin zunuban da sukeyi ba shi zai hana Allah ya barsu cikin farin ciki ba, sannan kome suka nema suna samunshi kamar su suka tsara rayuwarsu, to wadannan Allah ya barsu da kansu ne har sai sun tuba, kullum mu'imunin kwarai yana cikin jarabawar ubangiji masu tsananin rabo su ke cinye jarabawar dari bisa ďari, ya share mata hawayen idonta yace zanso Afeeyata ta zama daga cikin masu cinye jarabawar ubangiji a koda yaushe, zanso ki daina yawan zubar min da hawaye domin hawayen basu kara komai sai wahalarwa ga kyakyawan idanuwanki, zanso ki manta batun soyayyata a matsayin wanda zai aureki ki sanya soyayyar yaya a zuciyarki domin samun tsaftattaciyar addu'a daga gareki, ki kular min da Affan kamar yadda zaki kula dani domin ni da shi bamu da wata maraba kuma nasan zai kula dake kuma ya kaunace fiye da yadda ni nayi, ki yawaita istigfari domin istigfari yana kusanta bawa da ubangijinshi kuma mai yawan yinshi zai kasance kullum cikin nutsuwa da walwala, cikin sheshshekar kuka Afeeyah ta buďe baki zatayi magana jabeer ya sa hannu ya rufe bakin yace karki ce min komai ga Affan can yana jiranki zaku tafi gida, nagode sosai da ziyara, cikin kuka ta cire hannunshi a bakinta tace dan Allah yaya jabeer ka tsaya kaji abinda zan faďa maka, girgiza kanshi yayi yana mata murmushi hasken hakoranshi suka rufe idonta ta durkushe a gurin tana kallonshi cikin hasken tana kuka sosai tana kiran sunanshi, wata sassanyar iska ta shiga kaďawa a gurin har hasken jabeer ya bace ma ganinta, runtse idonta tayi tana kuka sosai tana faďin dan Allah karka tafi ka barni, Hannu taji cikin nata ana murzawa a hankali sannan taji saukar ruwa a kan hannun, a hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai ta saukesu kan Affan dake zaune kusa da ita kanshi a kan hannunta yana zubar da hawaye, lumshe idonta tayi hawaye na zuba ta gefensu ta fara tuno mafarkin da tayi akan jabeer, meyasa ya tafi bai tsaya yaji abinda zance mishi ba, meyasa be bari nasan abinda zan faďa mishi ba, shikenan bazan kara ganinshi ba har in koma ga Allah, to ni yaushe zan mutu, wayyo Ya Allah ka dauk---- Affan yayi saurin toshe mata baki da hannunshi yasa hannu yana share mata hawayen dake gangarowa daga cikin idonta, buďe idonta tayi ta kalleshi tasa hannu ta ďan ture hannunshi cikin muryar kuka tace kukan me kakeyi, da mamakinta sai taji ya kwanto jikinta yace kukan abin da kikeyi, a hankali tace ai bakasan kukan da nakeyi ba, ya ďago jajayen idanuwanshi yace nasan har duniya ta naďe bazaki taba yin kukan komai ba in ba na rashin jabeer ba, cikin mamaki ta kureshi da ido hawaye ya kara zirarowa a cikinsu cikin rawar murya tace kasa--- ya fashe da kuka yace nasani Afeeyah, nasani, nasan jabeer ya tafi ya barni, nasan bazan sake ganin fuskarshi mai dauke da

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});