Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

raba musu shi da jabeer ta fito ta mika musu tace gashi maza ku sha ku tafi gidan anty ma'u wanda bai shanye ba a gida zai zauna, suka karba suka fara rige rigen sha, salma da farida suka fita da gudu tun kafin su kai ďaki suke rige rigen faďin mummy yasha, suna karasawa ta toshe bakinsu tace ku rufemin baki ku wuce ku bani guri, suka wuce ciki suka dau nasu suna sha, zama oyiza tayi cikin farin ciki dan tasan yau babu makawa aikinta yaci tunda har sun tabbatar mata yasha,, har bayan isha tana kasa kunne taji ihu, amma shuru takeji hankalinta ya fara tashi,, karfe 9 lokacin taji dawowar alhj basheer ta mike ta fito ita da yaranta, zaune ta taddashi affan na kan ruwan cikinshi suna hira suna kyalkyace dariya kamar da sa'anshi yakeyi, wani abu ne ya tokare mata wuya wanda ta kasa controlling dinshi har ya kaita ga jan razanannan tsaki, taja hannun farida dake kokarin zuwa gurin babanta tace dalla wuce kuje ďaki, an faďa muku ta taku yakeyi, ai ku muna ya'ya ne a gidan nan amma ba ya'ya ba, alhj basheer ya dago da sauri yace haba safiya, me yasa kike faďin haka, da affan da su salma duk daya ne agurina, da karfi tace biyu ne, karka kara cewa ďaya ne, ka riga ka nuna musu tun yanzu basu da wata daraja a idonka saboda sun zo a ya'ya mata, nan ta shiga masifa kamar zata tsaga gidan, bakin ciki ne dankare a zuciyarta saboda yadda in tayi abu akan affan baya kamashi, alhj basheer bai kalleta ba ya kara rungume affan da ya tsorata ya mike ya wuce ciki ya barta anan tana bala'i...... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a gidan alhj basheer, kullum da sabon makirci da muguntar da oyiza ke fitowa dashi na tsafi da kuma na magunguna amma dayake rayuwarmu da mutuwarmu tana gurin rabbil izzati babu abinda ya faru da zeenatu da affan duk da wani lokacin in tayi tana cin nasara saboda ance tsafi gaskiyar maishi sai dai duk tsafin mutum in har ka dogara da Allah to ko ya kamaka na ďan lokaci ne zai sake ka, a yan shekarun da suka wuce oyiza ta kara karfi cikin kungiyar asiri dan yanzu haka tana cikin kungiyoyi masu karfin gaske guda hudu, zeenatu kuwa addua takeyi ba dare ba rana akan Allah ya kare su ita ďanta ya ďaurasu akan makiyansu... Affan da jabeer zaune ďakin hajja suna cin danwake, jabeer ya kalli affan yace kaii yau banga su anty salma a skool ba, affan ya juyar da kanshi yace ohoo musu wai dan daddy yace shi zai kaini zana C.E exams su su jira driver shine sukayi fushi mummynsu tace bazasu ba, Hajja dake gefe tana saka suwaitar kulu tace ca nakeyi ajinku daya da farida kenan bata rubuta jarabawar ba, jabeer yayi dariyar shakiyanci yace dondi kenan hajja, ay anyi mata repeating yanzu p4 take, Affan yace p4 din ma da ya aka bari ta kai, ni ay ban taba ganin wacce brain dinta baya ďaukar karatu irin farida ba cewar jabeer, Affan yace tabb ay wallhy gara farida a haka, dan anty salma knws nottn banda mugunta, ma'u ta ďeko dakin hajja da tsohon cikinta da kullum suke adduar Allah yasa zaunanne ne tace ashe baku wuce gida ba, na ďauka ma kun tsufa a gida, jabeer yace eh "Mama" sunan da yake kiranta dashi kenan saboda a gurinta ya girma bacci kadai ke maidashi gida", yanzu zamu tafi muna nan muna cin ďanwaken tsohuwa, Ma'u ta juya tace ai ya kamata kuje gida ku faďa musu kun gama jarabawar sai kuma a ďan fita yawo tunda ba mata bane ku, suka rufe kwanon danwaken suka mike sukayi sallama da hajja da ma'u,, sun kusa da kofar fita kausar yar suwaiba tana rarrafe a tsakar gida tsirara ta mike ta rike wani abu tana dabo ta fetso kashi saura kaďan ya taba wandon Affan, da gudu suka fita jabeer na mishi dariya harda rike ciki yana tayashi dubawa ko ya taba wandonshi, dakyar ya karasa gida yana masifa ya wuce bayi saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya shiga ďakin mahaifiyarshi, zaune ya sameta tana waya ya zauna kusa da ita, sai da ta gama wayar ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace daga ina haka, yace gidan maman jabeer, tace ya jarabawar kun gama ko, yace mun gama umma sai dai ayi mana adduar samun nasara, tace addua kullum yinta akeyi Affan, saidai a ďaura, ni dai ina kara jaddada maka ka rike ibada da karatun qur'ani da tsoron Allah wadannan abubuwan in ka rikesu sun isheka duniya da lahira, yace in shaa Allah umma, Allah ya kara mana karfin imani, tace ameen, ya mike zai fita kenan Asiya ta shigo da sauri, tace ina wuni umma, zeenatu tace lfy lau dan asy, ya na ganki haka, tace ummi ce tace in zo in fada miki anty ma'u ta haihu yanzun nan tana can gidan ma, da sauri zeenatu ta mike cike da murna tace me muka samu, asiya tace nima ban sani ba, ta dauko hijab ďinta suka fita da sauri a ranta tana adduar Allah yasa zaunanne ne abin da ta haifa, tun kafin su shiga ciki kukan yarinyar ke musu kuwwa cikin kunne, kuka takeyi irin na jarirai da iya karfinta wata nurse a unguwar tana gyarata, Affan a kofar gida ya tsaya dan yana tsoron ya shiga ya kara arba da kausar dan bai sani ba ko wannan karan a jikinshi zatayi kashin, A cikin gida kuwa murna sukeyi lokacin an gama kimtsasu anyi ma mai jego allura tana kwance tana hutawa, duk makota anata shigowa tayata murna banda suwaiba da tace meye na barka a gurin gawa, mudai je zuwa nan da anjima itama zata bi layin yan uwanta su cike su bakwai, karaf wannan furucin na suwaiba ya shiga kunnen jabeer, hararta yayi ya mikama mamanshi babyn suka fita shida Asiya, a kofar gida suka hadu da affan suka wuce gidansu.. Anyi suna dai2 na masu rufin asiri, mai jego ta samu kaya da kudi masu yawan gaske haka mahaifinta ya samu kudi sosai haihuwar tazo mishi da goshi, jaririya taci sunan Hajja "Hajara" Abida tace a dinga kiranta da "AFEEYAH", suwaiba kuwa bakin ciki kamar zai kasheta da taga har kwana bakwai jinjira na raye ga kaya da kudi da uwarta ta samu kamar za'a bude shago dasu, sam ta kasa boye bakin cikinta har saida sukayi fada da Abida ta gaggaya mata bakaken maganganun da yasata shigewa ďaki ba shiri dan Abida ba kanwar lasa bace itama... Tun daga lokacin kullum sai suwaiba ta kasa kunne ko zataji kururwar mutuwar jinjinra amma shuru takeji ga jinjira har ta wuce wata bakwai kullum cikin koshin lafiya, Afeeya ta taso cikin kulawar mahaifiyarta da kakarta hajja, yarinyar duk wanda ya ganta sai yayi sha'awarta saboda kullum a tsaftace take kan nan nata baya rabo da kitso da ribbons saboda tana da yalwar gashi, gata yar lutuya goyonta gunin ban sha'awa,

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});