Chapter 34
Chapter 34
kuďi, daki ta koma bayan ta gama sababinta tana kukan rashin sa'arsu ita da diyarta, malam Atiku ya fita ya barta, hajja kuwa ko dekowa batayi ba tana ďaki tana aikin rarrashi... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah Bayan isha'i Alhj basheer da kanshi yazo daukar Afeeyah, suna zaune da hajja da Asiyah suna rarrashinta suna kuma bata shawara akan ta kula da mijinta duk haukarshi mijinta ne kuma aljannarta na karkashin kafarshi, Asiyah tace yanzu kin zama kamar uwa a gareshi da taimakonki komai nashi zai fara daidaita, dole ki jajirce ki manta da ke yarinyace ki rike darajarki da ta mijinki kuma karki yarda wani ya raina shi a gabanki, Nasiha sosai sukayi mata har malam atiku ya shigo shima ya daura ya kuma yi mata tuni da riko da adduoi, sannan ya umurceta ta tashi suje ga alhj basheer can yana jiranta, mikewa tayi tana kuka Amirah ta miko mata sabon hijab dinta tasa Asiyah ta fesheta da turare ta riko akwatinta suka fito rakata, dakin suwaiba ta shiga yi mata sallama ko kallonta batayi ba ta cigaba da cin tuwon gabanta tana yan wake wakenta, tashi sukayi suka fita basu ko kulata ba, motar alhj basheer suka nufah suka sakata a baya ta rike hannun hajja sosai tana kuka tace saidai hajja ta shigo su tafi, dakyar malam atiku ya lallabata ta saki hajja sannan alhj basheer yayi sallama dasu suka wuce hajja na kuka tana ďaga musu hannu sai kace wacce zata bar unguwar,, Runtse idonta tayi da suka shigo harabar gidan tana karanto adduoi akan Allah ya taimaketa yayi mata jagora a cikin wannan sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, alhj basheer ya fito ya buďe mata kofa yace mun iso diyata, Allah yasanya alkhairi a farkon shigowarki gidannan, ya kuma dawwamar da farin ciki a cikin zaman aurenku har karshen rayuwarku, a zuciyarta ta amsa sannan ta sako kafarta kasa da bismillah, Zubur Affan ya mike daga kan kujera ya karaso kofa yana faďin daddy na ya dawo, yana buďe kofar ya hangosu da Afeeyah suna tahowa ya rugo da gudu yana cewa oyoyo barbie, chakk" ya ďagata cikin murna yana jujjuyata ya karaso cikin parlon da ita yana fadin mummy kizo ga barbie nah daddy ya kawo min, wani irin kuka Afeeyah ta fashe da shi yayi saurin sauketa yana nunama daddy hannunshi yana faďin ba ruwana daddy wallhy bani na sata kuka ba, alhj basheer yayi dariya yace kai ka sata kuka nima babu ruwana bari ma in tafi kar ace har dani, Affan ya zaro idonshi zaiyi ma oyizah magana tayi saurin jifanshi da mugun kallon da yasa shi ďauke kanshi ya ďago fuskar Afeeyah kamar zaiyi kuka yace ay bani na saki kuka ba ko,? Afeeyah tayi banza dashi ta cigaba da kukanta, alhj basheer yace zo nan diyata ki zauna rabu da shirmenshi, Afeeyah taja kafarta a hankali ta zauna a kasa kusa da alhj basheer Affan ma ya biyota ya zauna kamar zaiyi kuka, alhj basheer yace share hawayenki ki bude idonki ki gaisar da mamanki da kuma yayyinki, oyizah tayi saurin cewa ta mayar da idonta abinda muna tare kullum yanzu, alhj basheer yayi murmurshi yace haka ne, ya kalli Afeeyah yayi mata yar nasiha ya kuma roketa da ta kula da Affan ta rikeshi amana sannan yace suje oyizah ta nuna mata ďakinta, oyizah ta mike tace ma Afeeyah ta tashi suje, kafin Afeeyah ta mike Affan ya mike yace barbie tashi muje ďakinmu, Afeeyah ta mike tabi bayan oyizah da ya"yanta zuwa side din Affan, saida tayi addu'a sannan ta shiga ciki ba tare da ta ďago kanta ba, oyizah ta kalli Affan da ke binta a baya tace to bita zaizai wuce ka tafi daki, Affan ya bata fuska yace ay nan ne yanzu ďaki na, Salma ta daka mishi gigitaciyar tsawar da tasa shi fita da gudu, dariya suka watse dashi suka dawo da kallonsu kan Afeeyah, oyizah ta ďago kumburarriyar fuskarta tana mata kallon banza tace "so called Amarya," farida ta kwashe da dariya tace su amarya man gyaďa, salma ta hada rai tace kuna dariya ne, ay sai ta samu damar raina mu, mummy ki bata warning din da zaki bata mu wuce dan wallahi na mugun tsanar ganin yarinyar nan, oyizah tace me kike ci na baka na zuba, ta kalli Afeeyah tace nasan dalilinki na auren Affan bai wuce saboda dukiya ba, to kin makaro yarinya saboda ke da Affan kunyi ma juna nisa kamar tsakanin gabas da yamma saboda Affan is under my control sai abin da nace mishi, Sannan kisa a ranki aikatau ne ya kawoki gidannan ba zaman aure ba, salma tace gud mummy dama tunda "Gaje" mai aikin shegiyar mum din Affan ta tafi bamu kara samun mai aiki mai tsafta ba yanzu tunda mun samu wannan sai muyi manage, oyizah kwarai kuwa, yanzu zan fara miki lissafin daily works din gidannan, karfe 5 in kika tashi ba ruwana da sallarki in kinga dama kiyi in kinga dama ki barshi, fareeda tayi saurin cewa mummy wannan small gal din ma ay sallah bai wajabta akanta ba, salma tace tell her ooo, oyizah tace oho in taga zata wahalar da kanta tayi to tayi nidai amin aiki, girki shine first, sai gyaran kitchen, gyaran ďakin yara, sai parlor, tsakr gida da sauransu akwai maza masu yi, Farida tace mummy wannan special secret flower bed din naki da nake bashi ruwa plss spare me ki kara mata shi a aikinta, da sauri oyizah ta kai mata duka hade da yi mata dakuwa, farida ta toshe bakinta tace sorry mummy sannan ta fita da gudu, oyizah ta gama lissafa wa Afeeyah duk aikin da zatayi a gidan hade da concrete warning na in ta saba aiki ko daya ne she will be in fr it, Afeeyah dai gyada kanta kawai takeyi hawaye na kwaranya a idonta, har sun sa kai zasu fita oyizah ta juyo tace lastly babu ruwanki da rayuwar Affan, ban yarda ku kebe tare ba bare har ki yaudareshi da wadannan shanyayun idanuwan naki, salma tace haba mummy wannan mahaukacin meye zai rude shi, oyizah ta harareta tace shi dutse ne ba mutum ba, mahaukata ma ay suna da feelings tunda akwai zuciya a kirjinsu, dan haka na horeki da kebewa dashi bare har--- ta yi saurin dafe kanta tace bana ma fata dan har abada,,, salma tace har abada me, oyizah ta jata suka fita tace muje ďaki in faďa miki.. Suna fita Afeeyah ta fashe da kuka tana kiran sunan jabeer, kuka sosai takeyi har saida jiri ya fara dibanta sannan ta zauna bakin gado, saida ta gama tunane tunanenta sannan ta mike a zuciyarta tace Allah yasa yawan aikin da suka bani ya kasheni in huta, drawer dake dakin ta bude zata sa akwatinta taga kaya masu tarin yawa wadanda ba dinkakku ba harda na bacci, cire hijab dinta tayi ta shiga bayin dake ďakin tayi wanka ta fito tana tsane kanta da towel, tsawar da aka saki tayi daidai da bude kofar ďakin, da sauri ta waigo tana kallonshi yana kokawa da mukullin kofar alamun yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61