Chapter 14
Chapter 14
saidai fa akwai azabar kuka da masifaffen kwuiya, banda mamarta da hajja babu wanda take yarda ya ďauketa a duniya sai jabeer, shima dan tana ganinshi kullum a dakinsu kuma yana fita da ita yawo, sam bata yarda da affan dan ko ya miko hannu zai ďauketa in ta soma tsala ihu bata taba yin shuru har sai taga baya gurin, wannan dalilin yasa kullum ya shiga gidan sai yasan yadda akayi yasa ta kuka ta hanyar daukanta ta karfin tsiya,, Afeeya na da shekara biyu jabeer yasa babanshi yasata a makarantar da suke zuwa lokacin suna js2, dakyar ma'u ta yarda dan gani takeyi kamar wata hidimar ta ďaura musu, tare suke zuwa makaranta in sun dawo ya wuce gidansu da ita sai can yamma yake mayar da ita gida, duk wani kuďin break da ake bawa jabeer akan afeeya yake karewa, gata sosai takesha gurin yan samarin biyu duk da har lokacin bata cika yarda da affan ba, salma da farida ba karamin tsanarta sukayi ba, in suna cikin mota ta kallesu sai su sakar mata harara, turo baki takeyi a tsiwace irin na yara itama ta rama sai tayi lamoo a jikin jabeer ta runtse idonta dan kar su daketa, haka a skul ko takata yaro yayi bai sani ba ko yafi karfinta sai ta bishi ta rama in ya daketa taje ta faďa ma jabeer, in kuma tafi karfinshi to ta samu nama dan sam bazata raga mishi ba.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah ★ bayan shekara 6★ Jabeer ne ya fito daga makarantar (buk) cikin motarshi "vibe pontiac" da L a jikinta saboda har lokacin bai kware sosai ba, waya sukeyi da Affan da ya tafi karatu egypt wata uku da suka wuce, hira sukeyi sosai cikin jin dadi da kewar juna, saida yayi parking dai2 skool din su Afeeyah sannan sukayi sallama, can ya hangota cikin yara suna dambe ita da wata yarinya yara na ihu suna musu waka, da sauri ya karasa gurin ya raba fadan ya riketa tana kuka saboda yarinyar tafi karfinta karfin hali ne kawai irin nata, fisge2 ta shiga yi ita dole sai an barta ta buga ma yarinyar dutse, tsawa jabeer ya daka mata ya rike hannunta da karfi yace wuce mu tafi ko in zaneki a gurin nan, ta kalleshi cikin mamaki dan bai taba mata magana mai karfi ba bare tsawa, yace baki ji abinda nace bane, ta saki wani razanannen ihu tana buga kafa tana kuka sosai kamar wacce ake yanka ta, tsaki yayi ya ďauketa tana tirjewa ya turata cikin mota, Safna kawarta ta miko mishi school bag da L.B dinta yasa aciki ya zagaya ya shiga, dago kanta tayi tana kuka ta hango wasu yara suna mata gwaloo, haba nan ta fara kicin kicin bude kofar tana bugawa tana ihu kamar zata tsaga motar, kashe motar yayi ya janyota jikinshi yana rarrashinta tana zillewa,. dakyar ya rarrasheta yace ta faďa mishi abin da ya haďa su, kumburo baki tayi tace dukana tayi wai dan ban sani ba na yaga mata littafi shine har da cire min beets din da mama tasa min, kuma taja min gashi da karfi, murmushi jabeer yayi dan yasan tana sane ta yaga littafin yace banason karya fadamin gaskiya tsokanarki tayi kika yaga mata ko? ta turo baki ta gyaďa kanta, yace nasani ay, kuma shine dan rashin gaskiya kika fito kuna dambe ko, bana hanaki faďa ba? idonta ya fito waje tace to ay sune suke fara neman fada na, ya zaunar da ita kan kujera ya tada mota yace munyi faďa yau babu ruwana dake, dama na siyo miki cake kuma na fasa baki, ta rike mishi hannu tana kuka tace zan daina, yace bazaki daina ba kullum haka kike faďa, ta kwantar da kanta kan hannunshi tace Allah zan daina gobe, yayi dariya yace to naji in kika kara me zan miki, ta boye fuskarta tana dariya tace hakuri zakayi mana, ya kwashe da dariya yace yarinyar nan kin raina ni da yawa, yaja motar suka wuce.. Tsayawa yayi ya siyo ma Ma'u dake fama da ciwon 'koda' tun wata biyar da suka "fruits da rake" dan shi take yawan sha ance yana wanke infection din 'koda', sannan suka wuce gida, Tun kafin ya kai kofar gidan ya hango cikowar mutane, karasowa yayi jikinshi a mace yayi parking a gefe can ya hango maza sunata alwala ana jimami, bai bi takan fruits din da ya siyo ba ya dauko schl bag da lunch box din Afeeyah ya kama hannunta zasu shiga ciki, ta dinga waige2 tana cewa yaya jabeer baka dakko ma mama raken ba,. bai kulata ba ya jata suka shiga ciki, a tsakar gida ya tarar da taron mata cikin hijab kowacce tayi tagumi, dakin Ma'u ya shiga nan ya tarar da tashin hankali, kallon mutanen dakin yakeyi ya karasa kusa da mamanshi yace ummi me ya faru, ina mama,? Abida ta share hawayenta ta nuna mishi ma'u kwance cikin likkafani, matsawa kusa da ita yayi da sauri ya bude fuskarta ya fashe da kuka sosai yana kiran sunanta, Afeeya ta matso kusa dashi jikinta a sanyaye ta rikeshi itama tana kuka, rungumeta yayi sunata kukan da ya kara sa mutanen gurin kuka, Abida cikin kuka tace ya tashi ya wuce gida, kin tafiya yayi ya haďa Asiya da Afeeya suka wuce gidansu shi kuma ya zauna akayi mata sallah tare dashi aka kaita gidanta na gaskiya,, mutuwar ma'u ta girgiza jabeer sosai saboda ba karamin shakuwa sukayi ba, ita taci kashin shi tun yana karaminshi har yasan kanshi saboda mahaifiyarshi ba mazauniya bace.. Tun daga lokacin rikon Afeeyah ya koma gurin hajja dama acan take rabin zamanta ko sanda mamanta ke da rai, jabeer kuwa wata sabuwar kulawa yake bawa Afeeyah wacce take mantar da ita rashin uwa, gaba ďaya ya daina mata faďa kuma ya hana kowa yi mata faďa, ko an kawo kararta saidai ya basu hakuri yace ay yarinyace, sosai ya shagwabata, basu rabuwa ko da na kwana ďaya ne in kuwa tafiya ta kamashi in har ya tafi to ranar ba cin abinci babu bacci, wani lokaci ma har ciwo takeyi, shiyasa yake tsoron duk wani abu da zai sa yayi tafiya ya barta, haka su zeenatu da Abida ba karamin kula sukeyi da ita ba dan sun ďauke mata komai duk da malam atiku shima yana iya kokarinshi yaga ya debe mata kewa, suwaiba kuwa mutuwar ranar ne ya taba ta amma anayin uku shikenan ta sake tama manta da wata ma'u a rayuwarta, ganin Afeeyah da kuma jarabar rashin hakurinta su kadai suke tuna mata da ta taba yin kishiya... Mrs tijjani shattima.. [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah Yar Kyakyawar budurwa ce zaune cikin bakar doguwar riga mai adon jaa a parlon ummi, duka shekarunta baza su wuce 14 ba amma in ka ganta zaka rantse ta kai 16 saboda kayataccen jikin da makerin yammata ya fara kerashi, bazan iya fadin kyawun fatarta ba saboda ya zarce misali, ita dai ba fara bace kuma sam bata dauko hanyar bakake ba, wani irin colour ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61