Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abinda suka ce sai gab da magriba malam atiku ya fita suma suka tashi suka je yin alwala... Tun daren ranar take zuba idon ganin jabeer shiru har kofar gida ta fito ta tsaya tana kallon kofar gidansu ko zata ga fitowarshi amma ko giftawarshi bata gani, kullum ta dawo skull sai ta tambayi hajja ko yazo, in hajja tace bai zo ba nan zata fara sababi tace hajja kawai ki fadamin ko kin fita yazo baki nan ko kuma kina baccinki bakisan yazo ba, hajja saidai tayi tsaki tayi banza da ita ta cigaba da abin da takeyi, Afiya ta damu sosai da rashin ganin jabeer ji takeyi kamar ta mutu saboda rashin ganinshi haka kawai zata zauna taki cin abinci tayi ta kuka hajja bata ko kallonta bare ta rarrasheta.. Yauma kamar kullum a cikin sati biyun da tayi bata ga jabeer ba tana zaune ta haďa kai da gwiwa tana rero kuka hajja ta ajiye mata abinci a kusa da ita ta zauna gefenta ta kira sunanta, bata dago ta kalleta ba ta cigaba da kukan da takeyi, hajja tace to shikenan tunda bazaki saurareni ba dama jabeer ne,,, ta ďago kanta da sauri tace me ya sameshi hajja, hajja tace yana nan cikin koshin lafiya baki ga yadda yayi kyau ba, dazu kina makaranta yazo yace in faďa miki yana gaisheki in ya samu lokaci nan da wata daya bayan kin gama jarabawa zai zo ku gaisa, idonta ya ciko da kwalla tace hajja wata daya? Hajja tace eh mana, ba yace kince ya tafi gaba da birnin sin ba, to ba wasa nake mishi ba afiya ta faďi haďe da fashewa da kuka, hajja tace ay ko shi da gaske ya ďauka, Afiya ta maida kanta cikin gwiwoyinta cikin kuka tace shikenan kar ma yazo din dama nasan so kawai yakeyi ya kasheni, hajja ta gimtse dariyarta tace kull kar na kara ji, duk laifinki ne meyasa in yayi miki magana bakya ji, Afiya tace to ba nace na daina ba kema shaidace yau sati biyu kenan banyi fada da kowa a gidan nan ba kuma suna tsokanata meyasa baki faďa mishi haka ba, da wani abun nayi da yana zuwa zaki fada mishi amma saboda nayi abun kirki shine kika ki fada mishi, Hajja dariya taci karfinta sosai ta mike ta fita tana dariya ita kaďai, Afiya ranta ya kara baci ta kwanta tanata kuka harda sheshsheka tana tausayin kanta dan tasan in bata ga jabeer ba nan da kwana biyu to tabbas zata iya mutuwa,,, muryar hajja taji tana kwalawa Mahmud kanin kausar kira, ya taho da gudu yana buga ball yace hajja gani, tace Gidan Alh Bara'u zan aikeka, Afiya ta mike zubur ta dakko hijab dinta ta fito tace zanje hajja, hajja ta kalleta tace da wannan kumburarren idon zaki shigar musu gida, Afiya tace eh dashi zan shiga ni dai ki fada min sakon, hajja tace to ay sai kije ki shiga din mu gani zonan mamu kaji ta miko mishi kullin magani tace kace a aikawa Asiyah nayi mata bayanin amfaninsu, ya karba yace to hajja, bin bayanshi Afiya tayi ta hađe rai tace bani, jikinshi na rawa ya mika mata hajja tace Afiya karki fita gidannan haka ko uniform baki cire ba, bata saurari hajja ba ta fita dan so kawai takeyi yau ko ta halin k'ak'a taga jabeer.... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tana fitowa tayi tafiya kadan ta fada gidansu jabeer, gaisawa tayi da Ado mai gadi, yace yar lelen jabeer kwana biyu kinyi wuyar gani, tace wallhy baba ado mun kusa fara jarabawa ne, yace au too to Allah ya bada sa'a, tace Ameen ta wuce ciki idonta kan motar jabeer tasan tabbas yana ciki, kai tsaye ta wuce dakin Ummi ta murda ta shiga hade da sallama, amsa sallamar yayi haďe da ďago kanshi suka haďa ido, kallonshi ta tsaya yi idonta cike da kwalla shi kuwa murmushi yake mata yana mai jin dadin ganinta, girgiza kanta tayi ta wuce kitchen inda taji buruntun ummi, ummi na ganinta ta fadada fara'arta tace Afee yan matana, Afiya ta tsuguna ta gaisheta, ummi ta amsa haďe da ďagota tace kin gujeni kwana biyu ko ďan girki kin daina zuwa tayani, afee ta sunne kanta tace wallhy ummi jarabawa zamu fara yanzu bana fita amma ay nazo ran Saturday bakya nan, ummi tace eh kwarai naje daura, ya hajja, afiya tace tana gida ita ta aikoni wai gashi a kaima anty Asiyah, ummi ta karbi maganin tace Allah sarki kice mata an gode sosai kinji, afiya ta gyaďa kanta sannan tace bari in tayaki wanke wanken, ummi tace aiko nagode kamar kinsan na gaji, ga dayyaba har yanzu bata dawo ba, Afee ta fara wanke2 tace ummi Amirah fa, ummi ta wanke hannunta tace tana can kaduna gidan Asiyah har yanzu bata dawo ba, Afeeyah tace Allah ya dawo da ita lafiya, ummi tace Ameen yar albarka ta fita ta tarar da jabeer zaune yana latsa waya tace au ashe baka fita ba, yace walhy ummi nagaji ne sosai, tace ay da gajiya ni bari in ďan kwanta kafin la'asar, yace to ummi Allah huta gajiya tace Ameen ta wuce ciki,, saida ya tabbatar ummi ta kwanta sannan ya mike ya shiga kitchen ďin, tana tsaye tana goge kwanukan da ta wanke tana mita tana girgiza kai, dariya ta bashi a zuciyarshi yace yau ya shiga uku da masifarta, karasawa kusa da ita yayi ya dauki plates din da ta goge zai jera tayi saurin rikesu tace malam ka ajiye ni ban sa ka ba, yace ay nasan baki sani ba tayaki kawai zanyi, tace to banaso ko dole ne, yayi murmushi yace dole ne mana in ban tayaki aiki ba wa zan taya, tayi tsaki tace wacce ka samu a cikin sati biyu nidai ka fita kawai, da nasan ma zan sameka a gida da ban shigo ba, yayi dariya haďe da rike kafadunta yace makaryaciya dan ki ganni ne ma kika yarda aka aiko ki, tace God forbid, in ganka inyi maka me, yace kiji daďi mana in kuma bakiji dadin ganina ba kalli cikin idona ki faďa min, ta ďago a tsiwace zatayi masifa suka haďa ido tayi saurin sauke kanta saboda wani abu da ta gani a cikin kwayar idonshi, yayi murmushi yace nasan kinyi missing ďina, cikin muryar shagwaba tace ni banyi missn dinka ba, yace um um fa karki sani in tafi gurin da bazaki kara ganina ba, muryarta ta fara rawa tace me ya rage kuma tunda har ka iya yin sati biyu baka neme ni ba, ya dago kanta ya kalli idonta da hawaye ya fara zuba a cikinsu yace bake kikace in tafi ba, ta dunkule hannunta ta buga a kirjinshi da karfi tace to ba wasa nakeyi ba, shine ka daina bari in ganka baka ma damu da halin da zan shiga ba kasan ko kwana ďaya ne in ban ganka ba banajin daďi ni nasan yanzu ka daina sona tunda har ka iya yin sati biyu baka ganni ba kuma ka zauna la-fiya ta karasa fadi cikin kuka mai tsanani, kwantar da kanta

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});