Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dan wani lokacin yakanyi abubuwa irin na masu hankali, alhj basheer yayi murmushi yace hakane doctor, Allah dai ya kara bashi lafiya, dr musah yace ameen alhj, mikewa alhj basheer yayi yace to mu zamu wuce dan inada inda zani, dr musah yace to sai anjima alhj, nan suka fita dr musah ya bi Affan da kallon mamaki... Affan ne zaune a kan kujera a palour ya haďa kai da gwiwa yana kuka sosai harda sheshsheka, mamakin al'amarin nayi a zuciyata nace shi kuwa wannan tababben ko kukan me yake yawan yi tun ranar da aka kai Afeeyah asibiti oho,, a hankali naji yana faďin sai na dauki fansar kisarku, bazan kyale duk wanda yakeda hannu a cikin kisan ku ba, wannan yakin ni zan karasa shi cikin kankanin lokaci in shaa Allahu, sosai yake kuka yana faďin wadannan kalaman, cikin kidima na kureshi da ido a zuciyata nace anya wannan bai samu sauki ba, anya ba basaja yakeyi ba kuwa?, Da sauri na maida computer cikin kwakwalwrta baya zuwa ranar da Afeeyah ta aiwatar da ayukanta na karshe wanda yayi sanadiyyar zuwanta asibiti, da sauri na ciro yar makallaliyar camerar da ke makale a dakin oyizah na kunna, cikin mamaki na fara dauko muku rahoton abin da ke ciki, da naso in boye muku kamar yadda Affan ya boye ma su daddy sai naji wayar "Badiyya Aliyu" tana gargadina akan in rubuta muku komai har coma, da fullstop. kamar yadda "bingel" takeyi, Da sauri na dauki wayata na shiga typo muku abin da na gani mai ban mamaki, cikin bacci naga Affan ya rike kanshi yana juyi anan inda yake kwance a kasa, a hankali bakinshi ke motsi yana faďin umma, Jabeer, daddy, can kuma naga ya matse kanshi da karfi yana faďin wayyo ummana, sun kasheta, sun kasheta, sun kashetaaaaaaaa.... ya faďi da karfi hade da mikewa zaune zufa duk ta jika mishi jikin shi, waige2 ya fara yi a rude yana fadin ina ne nan, waya kawoni nan,, ya maza ya mike ya buďe kofar dakin a firgice ya farayin hanyar dakin zeenatu, ihu ya jiyo a side dinshi yayi saurin daukar hanyar gurin, yana zuwa kofar dakin yaji oyizah na faďin "kamar yadda na kawar da zeenatu da jabeer" kema haka zan kawar dake, lekawa yayi dan ganin ko dawa take, a gigice ya ja baya saboda ganin Afeeyah da yayi bakinta duk jini, a ruďe yace yaushe jabeer ya mutu, me Afeeyah takeyi a nan gidan, yanzu ummanshi ta mutu kenan, tambayoyin da ya dinga ma kanshi kenan idonshi na ambaliyar hawaye, da sauri yaja baya ya boye ya shiga dawo da abubuwan da suka faru dashi shekaru uku da suka wuce, babu abinda idonshi ke hangowa sai lokacin da ya tarar da kartin maza su biyu sun bankare mahaifiyarshi suna shirin shaketa da farin kyalle gabansu cike da kayayyakin tsafi mummy kuma tazo da wuka tana kokarin dab'a mata a wuya,, , shi dai yasan tun daga lokacin bai kara sanin inda hankalinshi yake ba sai yau da ya farka ya kuma tarar da wani tashin hankalin, me jabeer yayi mata ta kasheshi, wani irin kuka ya kufce mishi mai ban tausayi ya mike da niyyar komawa dakinshi ya ceci Afeeyah daga kaidin oyizah, har yakai kofar ďakin ya hango oyizah da wata a bakin kofar, da sauri ya juya yayi hanyar dakin da ya farka ya ganshi a ciki ko zai samu makamin da zai iya yakar ta dashi, yana shiga dakin yaji karar waya, da kamar bazai dauka ba, sai kuma yayi saurin dauka, ba"a bari yayi magana ba daga daya bangaren, murya yaji ta tsofaffi cikin rudewa tana cewa ina fatan kina nan lafiya Afeeyah, nayi wani mummunan mafarki akanki, ki tabbatar kin mike kinyi sallah dan komai na iya faruwa cikin daren nan, a hankali Affan yace waye ke magana, daga daya bangaren kaka liman yace kai din waye, Affan yace nine Affan, kai fa, cikin mamaki kaka liman yace Affan nine, kaka liman ne na daura, Affan ya fashe da kuka yace kaka kana ina aka kashe min jabeer, me jabeer yayi kuka bari aka kasheshi, kaka liman yayi kabbara da karfi yace Affan ka dawo cikin hayyacinka, Allah mai iko, ka daina kuka wannan maganar ba ta waya bace yanzu ina matarka, a gigice Affan yace wacece matata kaka, kaka liman yace Afeeyah itace matarka wacce take dauke da cikinka,! wacce ta yarda ta aureka cikin larura domin ta kubutar dakai daga cikin masifar da kake ciki,! wacce ta fara zame ma matsalarka ciwon ido,! nan ya takaita mishi duk yadda akayi ya auri Afeeyah da kuma irin taimkon da tayi mishi, zaman dirshan Affan yayi yana kuka sosai yace kaka babu mamaki itama bazata rayu ba don gata can sun ritsata a daki zasu kasheta, innalilliahi W.I.I.R kadai kaka liman ke iya fada yana sauraren kukan da Affan keyi, a hankali yace ka kwantar hankalinki Allah zai kareta ko don Rabon dake jikinta, karar da tayi ne yasa shi saurin kashe wayar ya mike zai fito yaji mahaifinshi ma ya fito, jingina yayi da bango yana zubar da hawaye har suka fita da ita suka sata cikin mota, kara kira kaka liman yayi Affan ya dauka yace ta kasheta kaka, gashi can sun tafi kaita asibiti da daddy, da sauri kaka liman yace bata mutu ba, na fada maka bazata mutu ba sai wannan rabon ya taka duniya, kayi saurin bin su karka sake ka barta ita da wannan matar dan zata iya yi mata illah, kuma karka nuna ma kowa kaji sauki domin yin hakan kamar ka bata goma ne daya bata gyaru ba, da sauri Affan ya fita, musababbin binsu asibitin kenan, ajiyar zuciya nayi dana gama tariyowa sai kuma nayi gaba har zuwa inda na tsaya muku wato inda Affan ke kuka yana fadin sai ya dau fansa.... Allah ya baka ikon karasa yakin nan Affan domin wannan kawar Bilki Nabayin Hatsabibiyace..... Mrs tijjani shattima...... [15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tafe take cikin motarta tana neman tsohon almajirin da zata bashi sadaka ta saceshi ta kaima chummy suyi bandaro da jininshi domin ta samu sa'ar kashe Afeeyah,, tana karya kwanar Gyaďi2 ta ga wani tsohon almajiri tukuf da kwaryar bara a hannunshi, parking tayi ta sakko ta dunkule dubu biyu hade da farin kyalle ta bashi, godiya ya dinga mata sannan ya juya mata baya, nan take ya bace ma ganinta, cikin murna ta shige mota dan duk tunaninta hakanta ne ya cimma ruwa, da murnarta ta koma gida ta wuce dakinta ta rage kayan jikinta, muryar Alhj basheer taji yana kwala mata kirah da karfi, da sauri ta fito dan jin abinda ya faru, kauda kanshi yayi dan a yan kwanakin nan sam baya kaunar ganin fuskarta wani lokaci ma tambayar kanshi yakeyi daliilin da yasa ya aureta, mutunta ta kawai yakeyi saboda darajar aure da kuma yarshi, badan haka ba da tuni yayi ma kanshi katanga da ita, kallonshi tayi tace alhj ka kirani kuma kayi shuru, yace eh baki zanyi daga cameroon zuwa anjima, ina son ayi musu girki, ta bata rai dan ta tsani wani dan uwan alhj basheer ya

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});