Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 50

Chapter 50

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sukayi a gefenta gaje ta fara shafa kanta tana faďin sannu hajiya, wani ihun ta kara saki tana faďin zasu kasheni, zasu kashe Affan, Gaje kije ki dauko min shi, gashi can zasu kashe shi, wayyo Allah nah zasu kashe min ďana, cikin sauri Ayyu tace indo maza je ki kirah malam kice mishi ya taho maza ta farfado..... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah Cikin sarkewar murya malam maina yace dagaske kike indo, jiki na rawa indo tace walllhy kawu da gaske nake, mikewa yayi ya gyara takalman kafarshi yayi sallama da abokanshi suka wuce gida, Yana shiga ya tarar har lokacin zeenatu na ihu sosai, da sauri ya karaso ya zauna ya umurci indo da ta kawo mishi ruwa, nan da nan ta fita ta kawo mishi ruwa ya jika wani ganye ya daďe yana tofa addu'a a cikin ruwan sannan ya mika ma Ayyu da take rike da ita yace ta ta bata tasha, dakyar suka iya ďagata suka bata tana ihu tana zubarwa, a haka har Allah yasa ya shiga cikinta, kwantar da ita sukayi suna shafa mata ruwan tayi wani irin kakari haďe da amai mai yauki, tana gama aman suka gyare mata jikinta suka kwantar da ita har lokacin idonta a rufe yake, saida suka tabbatar ta samu nutsuwa sannan suka tashi suka fita a dakin suna tattauna yadda zasu billowa al'amarin.... Tun a hanya kan alhj basheer ke sarawa a zuciyarshi yana tunanin wani abu da yayi ma rayuwarshi gibi kuma yakeson tuno shi, yana isa gida ya wuce ciki yana kallon ko ina na gidan, a hankali ya fara bin dakin zeenatu da kallo komai na rayuwar da sukayi a baya ya shiga dawo mishi har lokacin da aka nemeta aka rasa, tambayar zuciyarshi ya shiga yi akan ko an ganta, ko ta mutu ne, meyasa kwata2 ta bace a cikin kwakwalwarshi, da sauri ya karasa kofar ďakin ya murďa yaji ta a rufe, kitchen ya wuce shi kanshi ya rasa me zaiyi a kitchen din, yana shiga ya tarar da oyizah tsaye tana tsiyaya fresh milk a kofi, wani irin kallo yayi mata wanda shi kanshi baisan yayi shi ba, a hankali yace safiya ina zeenatu? har yanzu ba'a ganta ba? ko ta mutu ne,? saboda tsananin ruďewa saida oyizah ta kusa ajalin glass cup din hannunta tace alhj wace zeenatun, alhj basheer yace zeenatu nawa kika sani a rayuwarki, cikin in ina tace to ni ina zan san in--- kafin ta karasa magana wayar alhj basheer ta katseta, da sauri ya dauka yace ina wuni baffa, daga ďaya bangaren ya amsa yace bashiru shin ina labarin zeenatu, dazun nan tunaninta ya fado min bayan dogon lokaci har yanzu babu wani labari game da ita, alhj basheer cikin damuwa yace tunanin da na gama yi kenan baffa, gaba daya na rasa yadda akayi har tunaninta ya bace min, Baffa yace na cire rai da ita bashiru, addu'a kawai zanyi mata akan Allah ya kai rahama kabarinta, shekara uku babu amo babu labari, alhj basheer yace baffa baza'a cire rai da ita ba in har tana da rai, yanzu addu'a kawai zamuyi akan Allah ya bayyana ta in kuma bata raye Allah ya jikanta, sun dade suna jimamawa a waya sannan suka kashe alhj basheer ya fita daga gidan da sauri ba tare da ya kalli oyizah ba... Ajiye kofin tayi da sauri ta wuce daki cikin tashin hankali, kai kawo ta dinga yi idonta yayi jajur tace tabbas mati ya hake wannan damon, cikin sauri ta bazama gurin tsafinsu domin neman mafita... Gidan alhj bara'u ya shiga shi kanshi yayi mamakin tsawon shekarun da suka dauka ba tare da an nemi zeenatu ba, Abida harda kukanta dan kamar yadda ake shafe rubutu a allo haka aka shafe babin zeenatu cikin kwakwalwar mutane,, a ranar saida suka je gurin malamai hudu duk inda suka je sai anyi bincike ace tana raye amma bata cikin hayyaci da nutsuwarta, , addu'a sosai suka baza makarantar almajirai da gurin malamai, alhj basheer bai koma gida ba sai can dare gurin 11.. Afeeyah najin shigowarshi ta dauki hijab dinta dama ta shirya duk yadda zatayi yau tasa daddy ya barsu su kwana a dakin oyizah, wani macijin roba ta dauko ta turashi karkakashin kujerar da Affan ke zaune hankalinshi na kan cartoon, zama tayi kusa dashi tace manya kallon har yanzu bai isa ba, yayi dariya yace yanzu za'a gama yau bana jin bacci ina zaki naga kinsa hijab, tace sallah na idar shine ban cire ba, a hankali ta daura kafarta kan tashi tana mishi waiwaiyi, da sauri ya matsar da kafarshi ya kalli gurin dan ganin abunda ke mishi yawo a kafa, wani irin tsalle ya daka hade da ihu mai karfi ya runtse idonshi yana tsalle yana faďin wayyo daddy maciji, Afeeyah tayi saurin dauke macijin ta boyeshi taja hannushi a rude suka fito suna ihu tare, da gudu daddy da oyizah suka fito suna fadin lafiya, Afeeyah tace daddy maciji ne a dakinmu yana can ya shige karkashin gado, a ruďe alhj basheer yace maciji, Affan yace eh daddy har ya hau min kan kafata, alhj basheer yayi hanyar dakin, Afeeyah tayi saurin cewa daddy karka je ya sare ka, ka bari zuwa gobe in Allah ya kaimu sai a nemo masu wasa da macizai su dubashi, Alhj basheer yace hakane kuma amma a bar maciji ya kwana a daki, wai ni ta ina ma shigo, Afeeyah tace nima tunanin da nakeyi kenan, alhj basheer yace yanzu dai bazaku kwana a dakin ba zo muje bangaren safiya ku kwana daki daya, oyizah tayi saurin cewa alhj dakin da na bawa Affan cike yake da kaya a ina zasu kwana, alhj basheer yace ba ga dakinki ba tunda ba a ciki kike kwana ba, yau kadai ne fa gobe zasu koma dakin su, oyizah ta kumbura fuska tace sam baze yiwu ba alhj, akan me daki na privacy na in bar wata ta kwana a ciki, alhj basheer cikin mamaki yace Afeeyan ce wata, oyizah ta galla ma Afeeyah harara tace ba nufi na kenan ba alhj, alhj basheer yace na riga na gama magana suje can su kwana, Afeeyah ta kalli oyizah tayi murmushi tace to daddy ko za'a bude mana can dakin umma sai mu gyara mu kwana a ciki, hankalin oyizah ya kara tashi dan tasan in Affan ya shiga wannan dakin to komai zai iya faruwa, da sauri tace kuzo muje ku kwanta a nawa dakin, Afeeyah tace a'a mummy kar mu takura miki da dai munje dakin umma, oyizah tayi mata kallon zaki sani yau cikin dare, tace muje babu komai, ciki suka shige alhj basheer ya wuce side dinshi oyizah ta kai su Afeeyah nata zuciyarta cike da mugayen kulle kullen data gama shiryawa akan Afeeyah.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah Suna shiga dakin Afeeyah ta cire hijab dinta ta kalli Affan dake tsaye har lokacin a tsorace yake tace zo ka kwanta mana, ya karaso gurin gadon zai hau tayi saurin tare shi tace karka kwanta kan gadon mummy kaga ita

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});