Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

uku a gurin ta hango tanimu mai Guga rike da bokiti a hannunshi, da karfi ta kwala mishi kirah ya taho da sauri ya tsuguna yace hajiya gani, Afeeyah tace dan dan Allah a ina zaka samo fatanya inason a shiga cikin nan ne ayi min digging dinshi naga kamar ana gyara sauran kullum banda nan, tanimu ya rike baki yace wallhy hajiya ko katakon gurin nan ba'a yarda mu taba bare ganye bare kuma har mukai ga hakeshi, Afeeyah tace to saboda me, yace wallahu aalamu, nima ban sani ba, Afeeyah tayi tsaki tace kira min mati naga shi ke kula da flowers din gidan, da sauri ya mike yaje ya kira mati suka taho tare, dakyar da yaudara tace ma mati yazo ya hake mata saboda alhj yace za'ayi shuka ne a gurin, jin alhj ne yace yasa mati zuwa dauko fatanya ya bude gurin ya fara haka tun karfi, gefe ta koma tana addu'a tana kallonshi, yana tsakiyar hakan ne ya jiyo taurin wani abu, da sauri ya dago shi da fatanyarshi ya fara girgijeshi kasar na kakkaba, Afeeyah na hango kafar ta gane ta dabba ce, da sauri tace mati ajiye dan Allah ka samo min ruwa in dauraye hannu na, dasauri ya ajiye yayi gurin pampo, cikin azama ta karasa tayi bismillah ta dauko wannan damon tayi cikin dakinta dashi ta naďe shi cikin wani zani ta turashi karkashin gado, tana komawa gurin ta tarar da farida na balbale mati da masifah, Afeeyah ta karaso da sauri ta kalli fuskar mati gwanin tausayi tace ya akayi ne mati, mati yace hajiya saida na faďa miki ba'a taba gurin nan kika dage sai na hake shi, gashi yanzu hakan na min barazana da aikina, Afeeyah ta kalli farida dake harararta sannan ta maida kallonta ga mati tace dama wannan ce ta dauke ka aiki, ya girgiza kanshi yace a'a, Afeeyah tace to dan me zatayi sanadiyar aikinka, naga dai wannan aikinka ne, ko alhj yasan baka gyara wannan flower, mati yace a'a bai sani ba, Afeeyah tace to maza ka cigaba da aikinka tunda dama dan albashi kakeyi, farida tace ke kuma asuwa dan uwarki, Afeeyah tace ni as uwarki dan ita uwar taki, fareedah ta rike baki cikin mamaki tace mummy kike zagi, Afeeyah tace uwata ce ita ko kuma kina tunanin uwa tafi uwa ne, kai mati cigaba da aikinka in ka gama kayi watering din gurin ka rufe ni ina da abin yi, farida ta hassala ta finciko Afeeyah da karfi tace wallhy yau sai naci ubanki a gidannan, duka duka yaushe aka haifeki da zaki tsaya kina gaya ma mutane magana, Afeeyah ta haďe rai sosai tace sakeni kar muyi creating sin a gurin nan, farida tace baza'a sakeki ba, Afeeyah ta buge hannunta da karfi tace dallah sakeni, farida ta daga hannunta cikin fushi zata mareta Afeeyah tayi saurin rike hannunta tace karki fara wannan gangancin dan wallhy bazamu kare faďan nan yau ba, ki bar ganinki katuwa wallhy babu abinda zaki dauka ajikina dan abun a zuciya yake, kuma sannan da kike cewa yaushe aka haifeni to bari kiji ko jiya aka diga maniyyi na na fito yau na fiki daraja a idon duniya saboda nayi aure kuma nasamu Apple of marriage, ke fa? har yanzu kina gida babu mashinshini bare har yayi yunkurin dauka, tayi wurgi da hannunta taja tsaki ta wuce ta barta tsaye idonta jajur.... Gurin Affan ta wuce yana zaune yana kallon kifayen dake cikin fishpond, runtse idonta tayi saboda tuno mafarkin da tayi, da sauri ta mike tayi hanyar ďaki tsigar jikinta sai tashi takeyi, da sauri ya biyota dakin yana tambayarta me ya faru, a hankali take maida numfashi tace wallhy na tsani ganin kifayen nan, dan Allah muje gurin daddy yasa a fitar dasu daga gidan nan, Affan ya bata rai yace kifin mummy ne fa, bazata bari a fitar dasu ba, Afeeyah ta fara kakarin amai ta mike ta shiga bayi tana kakarin karya tana kuka kamar zata mutu, da gudu ya tafi dakin daddy yana fadin daddy kazo Afeeyah zata mutu, da sauri ya tashi ya fita yace tana ina, Affan yace tana bayi daddy, da gudu ya shiga dakin ya tarar da ita kofar bayin tana haki kamar da gaske, karasowa yayi da sauri yace me ya sameki, Affan yace daddy wai kifayen nan ne ke bata tsoro, Alhj basheer yace wani irin tsoro kuma, Afeeyah tace wallhy daddy kullum sai nayi mafarkinsu bana iya bacci da daddare, alhj basheer yace subhanallahi to gaskiya gara a fitar dasu daga gidannan dan kar su shafi lafiyar dan cikin ki, oyizah da ta shigo dakin dan taci uban Afeeyah akan abinda tayi ma farida tace baka isa ba wallhy, babu wanda zai fitar min da kifi, ance dole sai kinje gurin ne bare ki gansu, Afeeyah ta kara narkewa tace amma mummy ay a gidan suke, dan Allah kiyi hakuri a fitar dasu wallahy suna firgitani cikin dare, oyizah tace to zanga uban da ya isa ya fitar min da kifaye daga cikin gidan nan, alhj basheer yace haba safiya, ni bansan amfanin kifayen nan ba, ace shekara uku ana kiwon kifaye basa girma saidai su dinga cin abinci kullum, gaskiya yanzu za'a fitar dasu daga gidan nan kije can fili na na Na'ibawa ki cigaba da kiwata su, oyizah tace haba alhj yanzu saboda yarinyar nan tace bata son abu shin--- yayi saurin katseta yace saboda kar mu shiga hakkinta ita da abin da ke cikinta karki fassara maganar dan Allah yasa kai ya fita.., oyizah ta kalli Afeeyah ranta a bace ji takeyi kamar ta shaketa ta huta, mikewa Afeeyah tayi tana gyara jikinta tana murmushi tace mummy bakiji daddy na kiranki bane, oyizah ta harareta sama da kasa tayi kwafa tace billahil lazi sai kin gane ba'a shiga gonata, tasa kai ta fita, Afeeyah tace gonarki na nawa kuma, ta karshen ta rage in shiga in saki nometa da hannunki.. Karashe 54 Ba karamin tataburza akasha da oyizah ba gurin fitar da kifayen nan, saida alhj basheer ya nuna mata matukar bacin ranshi sannan ta yarda aka kwashesu ruwan ciki na yauki da kyar aka gama kwashewa, ana sakin ruwan wani irin wari ya gauraye gurin kowa a gurin saida ya toshe hancinshi, da gudu mati ya ruga ciki ya samu oyizah zaune tayi tagumi yace hajiya an gama kwashewa, wani irin harara ta sakar mishi cikin tsawa tace dazu saboda ka rik'a shine ka hake flowers din dana hanaku tabawa ko, mati ya marairaice fuska yace alqur'an hajiya sani akayi, tace ka fada min abinda ka hako a gurin, yace na rantse da---- babu abinda ya hako mummy, Afeeyah ta katseta, tace a gabana ya gama gyarawa akwai abin da kika binne a gurin ne, oyizah ta dafe kanta ta dago tace kan ubanki na binne, Afeeyah tayi gaba tana dariya tace kan ubana tauri gareshi, oyizah ta kalli mati tace bace min da gani banza shashasha, da sauri ya mike ya fita yana bata hakuri, wani irin juyawa taji kanta nayi saboda abin da ke shirin faruwa da ita yau, farin cikinta daya da mati yace bai hako komai ba, to ya zatayi da wadanan kifayen tsafin

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});