Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

uku a haka sannan ta daki wani katon dutse ta tarwatse a kasa dai2 lokacin ruwa mai karfi ya tsuge haďe tsawa, mutanen gurin kowa ya kunna full light dinshi suka karasa kusa da motar jiki na rawa saboda basu taba ganin accident irin wannan ba, ba karamin dagargajewa motar tayi ba, nan da nan suka fara kokarin ciro mutumin da suka gani a gaban motar, da kyar suka iya ciro jabeer saboda wani karfe da ya shige cikin hancinshi ya bullo ta kanshi, kuka mutanen gurin sukeyi suna salati saboda sun tabbatar da wanda suka ciro a cikin motar nan bashi da sauran rai, da sauri suka soma bincika aljihunshi dan motar babu abin dauka a cikinta, driving licences suka gani sai kudin da ya baci da jini ko ta ina, farar shaddar jikinshi ma babu wanda zaice fara ce dan duk ta koma ja, basu samu adress dinshi jikin d.l din ba sai dai sunanshi, daukarshi sukayi cikin mota suka shigo cikin garin kano suka zarce police station dashi,, (innalillahi wa inna ilahir rajiun) A kuma dai2 wannan lokacin Affan na zaune kusa da daddynshi suna dan taba hira duk da rabin hirar tasu shirme ce, a hankali ya karkatar da kanshi yana kallon daddy idonshi ya ciko da kwalla yace daddy yau ma kaga har dare yayi abokina baizo ba, ya kalli inda ya tara wasu fararen duwatsu guda 8 na kirga yace daddy kagani yau kwana 8 kenan, alhj basheer ya shafa kanshi yace kayi hakuri Affan kasan yanata shirye shiryen biki dole ka rage ganinshi, Affan ya marairaice fuska yace to daddy ni yaushe zaka min aure, alhj basheer yayi dariya yace duk ranar da ka shirya Affan, Affan yayi dariya shima yace daddy ay na shirya, daddy yace to wacece matar, Affan ya rufe idonshi yana girgiza kai fuskar Afeeyah nata mishi yawo a cikin kwayar idonshi da kwakwalwarshi, yayi saurin bude ido yace Barbie din jabeer, daddy ya kara sautin dariyarshi yace wacece kuma barbie, Affan yace AFEEYAH, daddy yayi dariya yace Afeeyar da jabeer zai aura, Affan ya gyada kanshi yana dariya yace eh daddy ay yace zai bani ita ta dawo nan gidan da zama, daddy yayi dariya yace to naji tashi kaje ka kwanta kaga ruwa na neman tsugewa, Affan ya mike yana murna yana fadin daddy zai aura min barbie.. dariya alhj basheer yayi ya mike ya wuce dakinshi dan oyizah tayi tafiya tun da safe.. Affan na shiga ďaki ya haye kan gado yanata wakar abu ďaya, tsawar da akayi mai karfi tayi daidai da faďuwar gabanshi, mikewa yayi daga kan gadon ya leka window yana kallon ruwan da ya tsuge kamar da bakin kwarya, Affan cikin tsoro ya rike kirjinshi dake tsananin bugu ya fita da gudu yayi dakin daddy, da kyar daddy ya lallabashi suka kwanta tare amma fa bacci ya kaurace a idonshi dan daga ya runtse idonshi to fuskar jabeer zai gani yana kuka mai tsanani.. Hakan ta kasance da Afeeyah, wannan tsawar da akayi ita ta farkar da ita daga baccin da bata san tayi ba mai cike da mafarkai, agogon wayarta ta duba taga 9:56 ta zauna tana sauraron zubar ruwan sama tana kara duba agogo kirjinta na harbawa da sauri, 10:20 ta kira wayar jabeer taji ta akashe, a hankali ta koma bayan hajja ta kwanta tana duba wayarta ko zata ji kiranshi shuru taji har 11 ta gota, a hankali ta fara rero kuka tana kiran sunanshi, kamar a mafarki hajja taji kukan ta farka da sauri tace yanzu ke Afeeya har yanzu baki bar kukan nan ba, wani irin iskanci ne wannan, Afeeyah tace hajja sha ďaya fa ta wuce kuma shi ya cemin goma da wani abu zai dawo, hajja cikin masifa tace shikenan kuma ana wannan ruwan in ya dawo sai yaki zuwa ya huta yazo gurinki saboda gaki yar gwal ko, Afeeyah ta shige jikin hajja tana kuka sosai tace hajja fa ya kashe wayar shi ne, kuma tun jiya fa ban ganshi ba, dan Allah ki taimaka min wallhy bazan iya bacci ba in ban ganshi ba, hajja taji tausayinta sosai tace to yi shuru ya isa haka, kinga yanzu dare yayi babu mamaki wayarshi ta mutu babu charge kuma bayason yazo ya sameki kina bacci kinga kuma ruwa akeyi kina son ya fito cikin ruwan nan ne, Afeeyah ta girgiza kanta, hajja tace to ki mishi uzuri gobe nasan tun kafin ki tashi daga bacci zaizo kinji, Afeeyah ta gyada kanta tana share hawaye haďe da ajiyar zuciya, hajja ta kwantar da ita tace yi addu'a kiyi bacci, Afeeyah ta fara karanto adduoi hawaye na zubo mata ta gefen idonta a zuciyarta tana jin haushin jabeer na kin cika alkawarin da yayi mata, yanzu haka zanyi bacci banganka ba yaya jabeer, atlst ko waya ya kunna naji muryarshi zan dan rage wani zafin abinda ta dinga fadi a zuciyarta kenan, baccin ranar a gurin Afeeya rabi da rabi ne, saboda duk farkawa saita duba wayarta taga ko ya kirata, ( Allah sarki Afee zanso ace kinsan gani da muryar jabeer ma bazaki kara ji ba bare har kiga missd call dinshi,) Abida ma juyi take tayi idonta na kan agogo, babu irin kiran da batayi ma wayar jabeer ba amma taki shiga, Alhj bara'u yace Abida ya kamata ki cire duk wasu tunani a ranki kiyi addu'a ki kwanta kiyi bacci in shaa Allahu babu abinda ya sameshi babu mamaki mota ce ta bashi matsala, Abida tace matsalar mota sai tasa ya kashe wayarshi yasan dole hankalin mu zai tashi alhj, alhj bara'u da shi kanshi daurewa yakeyi yace kinsan sharrin netwk mu zuba ido zuwa da safe mu gani, Abida dai uhum kawai tace saboda yadda takejin nauyi a kirjinta, rungumeta yayi ta baya yana faďa mata kalamai masu kwantar da hankali dan in ya bari tasan shima hankalinshi a tashe yake to fa zata kara daga hankalinta fiye dashi ma, Kaka liman ma ya kira har sau uku yaji ko ya iso, shima hankalinshi a tashe yake saboda jin har lokacin jabeer bai isa gida ba... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Washe gari tunda alhj Bara'u ya idar da sallah yake zaune kan dadduma, hankali tashe ya kalli Abida da ta zuba tagumi tana jan carbi yace Abida har yanzu wayar yaron nan bata shiga ba ko, Abida ta gyada kanta kawai tana kallonshi, yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah dai yasa jabeer lfy yake dan bai taba irin wannan abun ba, ko wayarshi nada matsalar charge ay duk inda yake bazai rasa wayar da zai kiramu ya sanar damu halin da yake ciki ba, Abida tace uhummm zuciyata tana faďamin duk inda jabeer yake ba lafiya yake ba, alhj bara'u yace ki daina faďin haka, haka kawai zuciyarki ta dinga kitsa miki mugayen tunani, ya mike tsaye yana duba lokaci yaga 7 har ta wuce ya fita daga dakin yayi hanyar waje, Abida ta share kwallar data ďan fito daga idonta tace ya Allah ka sassauta min zafin da nake ji a zuciyata ka bani ikon jure duk wani abu da zanji game da jabeer, Malam Atiku

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});