Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ganin abubuwan da suka taba faruwa a gurin kuma yake ganinsu kamar zanen cartoon, fuskar zeenatu ce take mishi gizo yanata so ya gano ko wacece saboda dishi2 yake ganinta, rike kanshi yayi dasauri bakinshi na rawa a hankali ya furta U-M-M-A,..... .. Mrs tijjani shattima... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah Maimaita sunan ya dinga yi yana ja da baya kanshi na juyawa saboda yadda abubuwan ke zuwan mishi cikin kwakwalwarshi, a firgice Afeeyah ta kamashi tana faďin me ya faru, girgiza kanshi yayi da karfi ya runtse idonshi yace dan Allah ki sakko dani ki kaini ďaki, Afeeyah cikin tsoro ta rike hannunshi taja shi tana waigen gurin ko itama zata ga abin da yake gani, daki ta wuce dashi ta zaunar dashi ta tsuguna a gabanshi har lokacin bai buďe idonshi, a hankali tace ka buďe idonka, kara runtse idon yayi yana girgiza kanshi, Afeeyah tace a daki fa muke ka bude idonka ka gani babu komai anan, a hankali ya fara bude idonshi har ya bude su gaba ďaya ya saukesu a kan Afeeyah, Afeeyah tace kaga ni ba komai ko, ya gyaďa mata kai, tace to me ka gani a can saman, ya ďaga kanshi sama yace babu komai sai fan, Afeeyah ta dawo kusa dashi tace ina nufin a sama inda muka je, rufe idonshi yayi shi kanshi yana son tuno abinda ya gani duk da bai gansu clear ba amma yasan ya gane fuskar ďaya a cikinsu,, bude idonshi yayi dan ya kasa tuno fuskar da ya ambaci sunanta a sama, kallon Afeeyah yayi yace ni ban ga komai ba, Afeeyah tace kagani mana, baza dai ka faďa min ba ko, ya tabe baki yace ni na manta kome na gani, Afeeyah tace to shikenan, tashi muje muyi sallah magriba tayi, ba musu ya mike ya bita fuskar da ya gani a sama tana ta mishi gizo amma sam ya kasa tuna ta.... Zaune take a gefen gadonta rike da turaren da kaka liman ya bata a hannunta tana shafa shi tana addu'a kamar yadda ta saba, tofe jikin Affan tayi da addu'a sannan ta kwanta tana istigfari har bacci yayi gaba da ita,,,, Mafarki***** Tafe take a cikin gidan tana bin inda bata taba bi ba tun zuwanta gidan a zuciyarta tana yabawa da kyau da tsarin gidan,, Kamar giftawar walkiya ta hango wani katon DAMO yana bin wata mata tana gudu tana salati haďe da ihun neman ďauki, da sauri ta bisu tana addu'a zuciyarta cike da tsoron wannan damon dan bata taba ganin suffa irin tashi ba, ja da baya tayi saboda yadda ta hango wannan damon ya hankaďa matar cikin wani kewayayyen flower bed ya haye kanta, tun tana jiyo ihun matar har ta daina jiyowa saboda matar ta nitse ciki sai tashin kura mai karfi kawai take gani,,, a firgice ta juya jikinta na rawa ta hango wannan damon ya fito daga cikin flower bed din yayi gurin fishpond, yana zuwa gurin ya rikiďa ya koma kifi ya shiga ciki,, a hankali ta tako ta leka cikin ramin ta hango kifayen sun cure kansu sun zama kifi ďaya, a gigice ta koma baya tana sauke numfashi tana fadin "innalillahi wa inna ilaihir rajiu'n," dan ganin yadda kifayen nan suka cure ba karamin daga hankalinta yayi ba, cikin sassarfa tayi hanyar daki, anan ne ta haďu da wani tashin hankalin dan ganin wata guntuwar halitta tayi a kofar ďakin oyizah tayi wuf ta shige ta kofa ba tare da ta buďe ba, nan jikinta ya fara rawa ta leka ta window ta hango wannan halittar ta haye gado ta nutse cikin katifar, wata dariya taji an saki mai karfi haďe da guguwar da ta fito da wani mugun bakin hayaki daga karkashin gadon, da sauri ta juya zata koma ďaki taji haushin karnuka a bayanta, tana waigawa taga bakaken karnika sun fi ďari sun doso inda take suna haushi kamar zasu tsaga gidan, a razane ta fara gudu tana fadin "hasbunallahu wa ni'mal wakil," bin ta karnunkan suka fara yi da gudu suna kara yin haushi, tana zuwa kofar dakinta taji an taďiyeta ta fadi kasa sosai, ja baya ta farayi tana kara karanto adduoi da karfi tana kuka, wani irin tsalle wani katon kare yayi zai hau kanta, a razane ta runtse idonta ta saki ihu mai karfi haďe da tashi daga baccin da takeyi, Affan ta gani a zaune yayi tagumi yana kallonta, kauda kanta tayi ta janyo wani zani a gefenta tana share zufar da ta jikata tana fadin "'A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min ghadhabihi wa 'iqaabihi, wa sharri 'ibaadihi, wa min hamazaatish-shayaateeni wa 'an yahdhuroon."" Singlet ďinshi yasa a gefen kunnenta yana share mata zufar da take gangaro mata daga kanta, juyowa tayi ta kalleshi tace har ka tashi, karfe hudu fa yanzu, ya karkatar da kanshi gefe idonshi ya ciko da kwalla saboda mafarkin mahaifiyarshi yayi amma sam ya kasa tina mafarkin, da sauri tasa hannu tana share mishi kwallar idonshi tace menene,? A hankali ya kwanta lamo a jikinta yana kara zana fuskar zeenatu a cikin kwakwalwarshi,, shafa kanshi ta fara yi tana karanto addu'a tana tofa mishi a kanshi har bacci ya ďaukeshi, haka suka kasance a wannan daren Afeeyah bata koma bacci ba dan tana matukar tsoron ta runtse idonta ta kara yin wani mafarkin.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah Washe gari sukuku ta gama aikinta, sai da suka karya sannan ta kirah kaka liman tayi mishi bayanin abubuwan da ta gani a cikin mafarkinta, cikin mamaki yace na faďa miki mugun tsafine dankare cikin gidan nan, yanzu gurare uku zakiyi aikin kisa a ranki Allah na tare dake, ki tabbatar yau kinsa an hake wannan flower duk abinda kika gani a ciki ki cire shi, sannan ki tabbatar wadannan kifayen yau basu kwana a gidan nan ba, kisan duk irin dabarar da zakiyi kisa a fitar dasu daga cikin gidan a wanke gurin ya zamana ba komai a ciki, sannan guri na uku shine mai wuyar, yadda zakiyi ki shiga wannan dakin nata har ki iya bankade karkashin gadonta, Afeeyah dai ta gama tsorata matuka idonta ya ciko da kwalla tace kaka duka suna da wahala, wallhy har yanzu jikina rawa yakeyi, yace nasani jikata nasan suna da matukar wahala amma Allah zai mayar maki dasu masu sauki daga kin fara, dan Allah karki ji tsoro zan tayaki addu'a ina daga nan, Allah zai taimakeki saboda niyyarki mai kyau ce, kisan duk yadda zakiyi ki bankade na karkashin gadon nan dan duk wasu alkadaranta anan suke, in mun gama da wannan zan fassara miki na karnunakan nan, jiki a sanyaye Afeeyah tace to kaka nagode sai anjima, yace to sai anjima Allah yayi miki albarka tace ameen kaka... Karfe 11am ta fito daga ďakinta ta fara bin hanyar da tabi cikin mafarkinta, sannu a hankali take tafiya har saida kafarta ta sada ta da wannan kewayayyen flower bed ďin da farida ke raya shi da ruwa babu dare babu rana,, karasawa tayi gurin flower ta leka ciki dan tasan duk dabarar da zatayi a hake mata gurin, ta kai minti

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});