Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kar ka bawa kowa kaji, bakin suwaiba ya kasa rufuwa tanata godiya kamar wacce akayi ma kyautar aljanna, oyiza tace haba ba komai ay zaman tare ya wuce komai nima kin min abinda ya fi wannan, har gate ta raka suwaiba tana kallon Abulbait saida ya shanye tass sannan ta juya gida, Suwaiba da rawa ta shiga gida tanata ďaga kuďin sama tana nunawa ma'u dake ma Asiya yar Abida kitso, rawa takeyi tana habaici wai wata saidai bauta amma bata samun kudi, kullum aikinta renon yayan da ba nata ba daga a bata ragowar abinci sai a bata na batarwa, Ma'u ko kallonta batayi ba ta karasa ma asiya kitso tayi mata wanka ta bata abinci ta goyata kafin mamanta ta dawo daga gurin aiki,,, Tun bayan isha'i Abulbait ke kakarin amai kamar zai amayar da yayan hanjinshi, jike jike suwaiba ke tayi mishi tana bashi amma ina amai yaki tsayawa, kudin da oyiza ta bata ta kalla a zuciyarta tace nasan yanzu in nace zan kaishi asibiti zan kashe fin dubu biyu, ta maxa ta mayar dasu tace inaa a gida zaka zauna bari in jiķa maka tazargade dan da gani aman hakori ne, tashi tayi tana bincika tazargade bata gani ba, ta duba ko ina na dakin amma bata ganshi ba kuma tasan tana dashi ko dazu ta ganshi, mikewa tayi ta fita da gudu ta shiga gurin hajja dan bata rabo dashi, hajja ta dubo ta mika mata tace Allah ya bashi lafiya, tace ameen ta fita da gudu, tana shiga ďaki ta tarar da gawarshi bakinshi duk ya baci da jini, wani irin ihu ta saki tana jijjigashi tana kiran sunanshi, da gudu hajja da ma'u suka shigo cikin dakin, ganin Abulbait ya daga musu hankali hajja ta daukeshi tana dubashi ko da sauran numfashi, girgiza kanta tayi tace saidai kiyi hakuri suwaiba Allah ya karbi abinshi, ta kara sa ihu tana kuka tana birgima kamar tababbiya, dakyar aka lallasheta tayi shuru akayi mishi wanka aka suturceshi malam atiku ya daukeshi ya kaishi dakinshi yayi kwanan keso acan... Aiki sosai chummy takeyi ma oyiza akan ta samu cikin ďa namiji, tace mata ta nesanci alhj basheer har tsawon kwana uku, a ranar na hudun ne zata bata magani sai tasa ya kusance ta, haka kuwa akayi oyiza ta kauracewa shimfidar alhj basheer gashi mabukaci gashi kuma ta hanashi kusantar zeenatu, abin na damunshi amma haka ya daure dan kar ya bata mata rai.. Suna zaune a kofar gidanshi shi da alhj bara'u suna hirar rayuwa, alhj bara'u ya tuno da wani tsumi a motarshi ya shiga ya dakko ya mikawa alhj basheer daya, alhj basheer yace na menene wannan, alhj bara'u yayi dariya yace goggo ta aikomin shi daga daura maganin basir ne, alhj basheer ya fara sha yace lallai wannan irin bauri haka da basu sa zuma ba dakyar zai shawu, sai gurin sha ďaya suka rabu kowa ya shiga gidanshi, a parlor ya tarar da oyiza cikin wata matsiyaciyar shiga mai tada sha'awa, karasowa yayi kusa da ita ya zauna, matsawa tayi sosai tace meye haka kuma, idonshi yayi ja yace ki taimakeni safiyya, , tayi tsaki ta mike tace in taimakeka akan me, nifa banason jaraba na fada maka kayi min hakuri na tsawon 3dys jibi ne fa , ni banason gajen hakuri walhy, ta wuce ciki ya bita da sauri tayi maza tasa keyy ta datse dakin,, ya koma ya zauna cikin tashin hankali, mararshi yaji tana murďa mishi sosai ya rasa yadda zaiyi sai juyi yakeyi, kamar an mintsileshi ya mike rike da mararshi ya wuce dakin zeenatu, tana zaune tana addua tana kai kukanta gurin Allah ya murda kofar ya shigo, waigowa tayi ta kalleshi ta mike da sauri saboda yadda taga idonshi yayi ja, karasawa tayi kusa dashi cikin damuwa ta rikeshi tace lafy me ya sameka, kankameta yayi yana fitar da wani wahalallen numfashi yace ki taimakeni zeenatu, dan Allah ki taimakeni in sauke nauyin da rataya a wuyana akanki saboda ina cikin mawuyacin hali, ta rikeshi sosai itama tace babu taimako tsakanin mata da miji, duk lokacin da kake bukatata a shirye nake in amsa kiranka, ya sauke ajiyar zuciya yace Allah ya miki albarka zeenatu, nan suka shiga faranta ran junansu, tabbas zuciyarshi tayi missing zeenatu ta ko wane bangare amma ya rasa meye ya tokare wani shashi nata har baya iya kyautata mata, Alhj basheer ya ji dadin wannan daren saboda yayi gamsuwar da ya dade baiyi ba, ga zeenatu ma haka abin yake domin ganin daren tayi kamar duk yafi sauran darurruka amma ta dangantashi da missing din mijinta da tayi, sai da yayi wanka a dakinta yana sa mata albarka sannan ya fita cikin tsananin ciwon kan da yarasa dalilinshi, a daren ranar Alhj basheer da zazzabi mai zafi ya kwana saukinta ma ya sauke wani nauyin, sai kawai yaji da na zazzabin..... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah Satin Alhj basheer daya yana zazzabi har saida yasha allurai, zeenatu ke kula dashi dan oyiza na fushi dashi tun da ta ganshi ya fito daga dakin zeenatu a ranar, Ga kuma maganin da chummy ta bata ya wuce ka'idar amfaninshi saboda ciwon da yakeyi, a ranar da taga alamun yaji sauki ne ta fara neman hanyar da zatayi amfani da maganin har ya kusanceta, haka kuwa akayi sai da tasan duk yadda tayi da kissa da yaudara har ya kusanceta,, oyiza ta kasance cikin farin ciki a wannan dare dan gani take ma har ta haifi ďan komai ya dawo under her... 4mnts ltr Zeenatu ce zaune suna hirah da Abida dake da tsohon ciki, Abida ta kalli zeenatu tace matar nan fa ni ban gane miki ba, tun wata biyu da suka wuce kika wani canza kikayi fresh, yanzu kuma gaba daya kin cika famm sai kace me ciki, zeenatu ta shafa cikinta tace sai kace yin cikin wasan yara ne, ko sign fa ban taba ji ba, Abida tace ji ki da wata magana, akwai cikin da haka yake ba'a taba ganeshi sai in ya fito da kanshi kuma wallhy alamu sun nuna cikin nan ya dan dade a jikinki, zeenatu tayi dariya sosai tace to doctr Abida naji bayaninki, dama ana jini in ana da ciki, Abida tace nawa akayi kedai ina zuwa, gida ta shiga ta dauko ragowar "pt strip" din da tayi amfani dashi farkon cikinta sannan ta dawo ta bata kwalba tace taje tayi fitsari, zeenatu ta mike tana dariya tace Abida kenan wahala kawai zaki bawa kanki, Abida tace tunda ba ke zaki wahala ba meye na compln, ta yi dariya hade da shiga bayi tayi fitsari ta fito ta mika mata kwalbar, Wani irin ihun murna Abida tayi da taga postive, ta kalli zeenatu tace wallhy nayi tunanin hakan, wayyo dadi kasheni, zeenatu a ruďe ta shafa cikinta tace kina nufin ciki gareni, u mean akwai halitta mai rai a cikina, Abida tace sosai ma kuwa in baki yarda ki shirya gobe kafin na tafi karbar hutun haihuwa muje asibiti, zeenatu idonta ya ciko da kwallar farin ciki tace Abida bansan irin farin cikin da zanyi ba in har wannan maganar taki

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});