Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuka, hajja ta zauna tana kuka tana fadin kukan ne babu mai iya hana shi fita alhj, ta kalli Afeeyah da idonta ke lumshe har lokacin ta riketa sosai ta kira sunanta har sau uku taji shuru, ta girgizata da karfi tace ki bude idonki Afeeyah, nasan abinda kikeji dan Allah kiyi tawakkali, kar wata cutar ta kama ki, dan Allah Afeey--- Afeeyah tace hajja me kika gani yanzu, kuka nakeyi ko me, ba tawakkalin nayi ba, me kukeso inyi, ku faďa min me zanyi yanzu hajja,, kome kukace inyi zanyi walhy, alhj basheer ya fita da sauri saboda kukan da yaci karfinshi yasan sam Afeeyah bata cikin hayyacinta, hajja cikin kuka tace addu'a zakiyi Afeeyah, addu'a jabeer yake bukata, Afeeyah ta bude idonta sosai tace hajja a ina zanyi adduar, hajja ta rungumeta tana sheshshekar kuka tace a bakinki zakiyi ta, Afeeyah tayi yake tace hajja kunce kar inyi kuka, kuma ku gashi kuna yi dan Allah kiyi shuru bari in shiga gurin ummi, hajja ta rike hannunta suka shiga gurin Abida inda makota suka kewayeta, tana ganin Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka fito daga idonta, Afeeyah tace ummi kuka kikeyi, daddy yace kar muyi kuka, ta kalli Amirah tace Amirah dan Allah ki faďa min yadda zanyi hawaye su fito a idona, Amirah ta fada jikinta tana kuka sosai, Afeeyah tace dan Allah ku fadamin yadda zanyi, zuciyata zata buga ku taimakeni inyi kuka ko zan samu saukin nauyin da zuciyata tayi, Alhj bara'u ne ya shigo ďakin shima idonshi jajur yace Abida kuzo kuyi mishi addu'a an gama shiryashi, Abida kanta a kasa tace kuje kawai rahamar ubangiji ita kadai nake mishi fatan samu a kabarinshi, Afeeya ta mike ta fita da gudu a tsakar gida taga gawar an shiryata cikin likkafani, da gudu ta karasa bata lura da mutanen da sukayi dafifi a gurin ba ta faďa kan gawar tana shafawa, a hankali tace yaya jabeer alkawarin da kayi min kenan, meyasa zaka tafi ka barni, saida nace maka mu tafi tare kaki yarda ka tafi kai kadai yanzu ka faďamin yadda za'ayi in cigaba da rayuwa babu kai, meyasa bakayi tunanin abin da mutuwarka zata haifar a cikin zuciyata ba, dan girman Allah yaya jabeer ka tashi karka tafi ka barni, kai kaďai gareni, malam atiku ya matso kusa da ita ya dafata yace Afeeyah Allah baya barin wani dan wani yaji daďi, Allah ba ruwanshi da duba shakuwarku, Allah ya kaddara--- ta katseshi ta hanyar bige hannunshi tace wace irin kaddarace wannan, meyasa bata daukeshi tun kafin inzo duniya ba, sai yanzu zata zo ta dauke min shi a lokacin da nake bukatarshi, ta mike tsaye tace abba dan Allah ka fadamin yadda zan iya cigaba da rayuwa, kasan dai bazai yiwu ba, malam atiku ya rungume yarshi yana kuka sosai, yace Afeeyah nasan yadda kikeji, ta sakeshi tana girgiza kai tace wallhy abba babu wanda yasan yadda nakeji sai yaya jabeer, ta kankameshi tace kai kadai kasan yadda nakeji, dan Allah ka tashi, duk rashin imaninka sai ka zubar ma da Afeeyah hawaye, babu yadda ba'ayi a banbareta jikin gawar ba amma abin ya faskara tana kwance kanshi tana sambatu babu ko ďigon hawaye a idonta, dago kanta tayi saboda ganin mutum yayi kneel down a gefenta yana shafa tun daga kafar jabeer har kanshi, kallonta yayi yana kaďa kanshi hawaye na fitowa a idonshi yace barbie yau kwana 9 banga abokina ba, yanzu kuma naga sun rufeshi da fararen kaya ina zasu kaishi, kice mishi ya buďe idonshi inason muyi magana, I missd him so much, sai a lokacin Afeeyah ta kara maida kanta kan jabeer ta fara kuka mai tsanani tana fadin maganganun da ita kanta bata san suna fitowa daga bakinta ba, Affan ma duk da baya cikin hankalinshi yaji a jikinshi wani mummunan abu ya samu abokinshi, da kyar aka iya banbare Afeeyah jikin gawar jabeer, ana sashi cikin makara ta kara fashewa da kuka tana faďin dan Allah ku dawo min dashi wallahi zai dawo gareni, dan Allah karku fita dashi, ta dinga fisge2 jikin wadanda suka riketa tana fadin a dawo dashi ko ya mutu a bar mata gawarshi, suna shashi a mota Afeeyah ta saki wani gigitaccen ihu ta faďi kasa sumammiya.... Mrs tijjani shattima.... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah A hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai, dishi2 take gani tayi saurin mayar dasu ta runtsesu tana fitar da wani irin wahalallen numfashi, muryar Anty Asiya ce yasa ta kara bude su ta kalleta, anty Asiya ta shafa kanta idonta cike da kwalla tace sannu Afeeyah, babu inda yake miki ciwo, ta lumshe idonta tana girgiza kai hawaye na zuba a gefen idonta, anty Asiya ta fara yi mata nasihar da daga ji itama na karfin hali ne, saida ta daďe tana mata nasiha sannan ta tashi ta fita, da sauri safnah ta dawo gefenta ta rike hannunta tana zubar da hawaye tace Afee, Afeeyah ta kara runtse idonta hawaye na gangarorowa cikinsu kamar an saki ruwan pampo, Safnah ta kwanta a jikinta cikin muryar kuka tace don't stop dis tears Afee let it flow nasan yadda kikeji, cry as much as u can, Afeeyah ta kara fashewa da kuka, suka dinga yi ita da safnah dake jin mutuwar ta ko ina a cikin jikinta, sun daďe suna kuka kafin safnah tayi shuru ta mike tana kallon Afee, safnah tace Afee tashi kiyi sallah kinsan fa bakiyi azhar ba gashi har la'asar ta wuce, dakyar Afeeyah ta gyaďa mata kai tace shikenan safnah sun kaishi sun birne min shi ko, shikenan ni yanzu bani da wani sauran gata a duniya ko, dan Allah safnah ki roka min Allah in mutu in bi shi dan wallhy bazan iya rayuwa ba, Goggon daura ce ta shigo cikin dakin ta zauna gefensu tace zaki iya rayuwa Afeeyah, wannan kukan da kikeyi babu wanda zai hanaki yinshi domin shine kadai ne zai rage miki raďađin da kikeji, ki sani jabeer yayi mutuwar da ko wane musulmi zaiso yayita, ya mutu a daren alhamis aka kaishi ranar jumma,a, ya mutu a hanyarshi ta ziyara kuma da kyakykyawar niyya a zuciyarshi, ko wannan muka tuna ya isa yasa mu ji dadi saboda yayi mutuwar da akeso, tashi maza kije kiyi sallah ki karfafa zuciyarki kiyi mishi adduar samun rahama wannan ita kaďai ce hanyar da zaki nuna tsantsar soyayyarki gareshi yanzu, Afeeyah ta gyaďa kanta ta mike dakyar ta shiga bayi.. Karfe biyu saura motar oyizah tayi parking a cikin gida, tayi mamakin rashin ganin "saunanta" a waje yazo tararta kamar yadda ya saba, ciki ta wuce cikin farin ciki tana kwala kiran sunan Affan, salma da farida ta tarar a parlor suka yi mata sannu da zuwa, ta amsa haďe da zama tace ina "rakumi na" yau banga yazo yi min oyoyo ba, salma ta tabe baki tace yana can gidan rasuwa kinsan Abokinshi dan girman kan nan ya wullah,, oyizah cikin tashin hankali ta mike tace how comes ya fita daga gidan nan, farida tace nayi mamaki nima mummy, Alhj basheer yayi gyaran murya ya fito daga

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});