Chapter 44
Chapter 44
ta wuce ta cire kayan jikinta tayi wanka ta dauro alwalar walha, ta windon bayin ta hangoshi zaune gurin fishpond idonshi kyar a cikin ruwan baya ko kiftawa, murmushi tayi ta fito daga bayin, sai da tayi sallah ta shirya cikin bakar jallabiya sannan ta fita gurinshi, A hankali ta karasa gurin tayi saurin rufe mishi ido da hannunta, shafa hannun yayi cikin firgici yasa ihu yana ďaga kafarshi dan kar ya faďa cikin ramin kifin, da sauri ta toshe mishi baki tana dariya tace nice matsoraci, juyowa yayi ya kalleta nan take ya saki dariyar farin ciki ya rungumeta yace ina kika tafi ki barni, ta dago fuskarshi tace ina daddy yace maka ya kaini, ya shagwabe fuska yace mummy tace min bazan kara ganin ki ba, jiya suka dinga min ihu anty salma har da duka na, Afeeyah tace am sorry gani na dawo daga yanzu babu wanda zai kara maka kallon banza ma bare har ya dukeka tashi muje kaci abinci, ya mike da sauri yana dariya suka wuce daki... Da sauri oyizah ta bar gurin dan kar Afeeyah ta ganta, wani irin bakin ciki ne yake taso mata a cikin zuciyarta, shin me zata ma wannan yarinyar ta daina ganinta kwata2 a rayuwarta, a cikin yan kwanakin nan ganin yarinyar nan shine abinda yafi komai bakanta ranta, aiki biyu kenan tayi akanta kuma duk masu karfi amma basu kama ta ba, tabbas wannan gara inyi mata me kankat, tabbas yau ne numfashinta na karshe a duniya dan barin Afeeyah a duniya barazana ce a gareta dan yarinyar na neman fin karfinta, a tarihin rayuwar oyizah tun tana karama babu abinda ke tsaya mata a gaba bata kau dashi ba dan haka wannan karan Afeeyah bata isa ta rusa sa'arta ba, da wadannan tunanin ta karasa ďaki ta zauna neman mafita, wani sashi na zuciyarta ya bata amsar cewar ta bada Afeeyah kawai su "chummy" suyi bandaro da jinin tsinaniyya, in ba hakan tayi ba to kuwa tana zaune kwado zai mata kafa,, dariya tayi cikin gamsuwar shawarar da zuciyarta ta bata, nan ta mike ta fara shirye2 kafin dare yayi ta sadaukar da jinin ďiyar ma'u da malam Atiku, To oyizah muje zuwa muga zaki iya da Afeeyah... Cikin jindadi suka kammala cin abincinsu na dare wanda hajja ta aiko musu, bayan sun gama ta jiko maganin da kaka ya bata ta bashi yasha dakyar yana sha yana furzarwa, saida ta nuna mishi bacin ranta sannan ya sha da yawa, yana gama sha ta gyare gurin ta dawo ta zauna suka fara yar hira, murďa kofar suka ji anyi suka waiga suna kallonta, da fara'a ta karaso gurinsu tace amarya da ango, sannunku da hutawa, Afeeyah ta kau da kanta tace yauwa, oyizah ta zauna gefensu tace Afeeyah ya kamata ki ďan leka gida ki gaishesu dan gani nayi tunda kikazo gidan nan baki shiga ba, daga nan sai ki dan zaga da Affan yaga gari ko ya kikace, Afeeyah tace hakane mummy amma ay naga affan baya fita ko, oyizah tace shiyasa nake so ki ďan fara fitar dashi yayi refreshing, Afeeyah tace to duk yadda kika ce, ta mike ta dauko hijab dinta tace tashi muje, ya tashi yana kallon oyizah alamun yana so ya tambayeta yaje ko a'a, gyaďa mishi kai tayi alamar yaje, dariya yayi ya bi bayan Afeeyah suka fita, dariyar jin dadi oyizah tayi ta rakasu har gate sannan ta juyo da sauri tayi dakinta ta kwaso kayan tsafinta ta nufi side din su Afeeyah, Tafiya takeyi da sauri saboda manta Turaren da tasa a ranta duk ranar da xata gida zata kaima mahifinta, tun a parlor ta gane akwai mutum a bed room dinta, labewa tayi ta leka a hankali, ba karamin firgici ta shiga ba ganin oyizah tsaye a gefen gadonsu tana shimfiďa farin kyalle a kasan katifarsu, da sauri ta fita daga dakin lokacin da taga ta dauko zanin gadon su ta mayar ta shimfidashi yadda yake, a guje ta fita ta samu affan a inda ta barshi murya na rawa tace muje, ya kalleta yace ina turaren, dakyar ta saita kanta tace muje dai gobe zan kai mishi.. Sai goma saura suka dawo gida, babu wanda Afeeyah ta faďa ma abin da tagani dan ta riga ta gama kudira abinda zatayi tana komawa gida, suna shiga ta zaunar da Affan a parlor ta kunna mishi tv tace kar ya tashi bari ta gyara cikin dakin, tana shiga daki ta yaye zanin gadon da bismillah ta ciro farin kyallen ta naďe zanin gadon ta ajiyeshi gefe sannan ta fito ta kalli affan tace ina zuwa bari in mayar ma da mummy zaninta, yace to ya cigaba da kallon cartoon dinshi, tana fita tayi hanyar ďakin mummyn cikin sanďa dan tasan yanzu tana gurin daddy, a hankali ta murďa kofar ďakin ta shiga da addua a bakinta, da sauri ta yaye zanin gadon tasa farin kyallen kamar yadda taga oyizah tayi sannan ta maida zanin gadon ta shimfidashi yadda yake tasa kai ta fita daga ďakin da sauri..... Mrs Tijjani shattima [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tana komawa daki ta tarar da Affan na gyangyaďi a kan kujera, da sauri ta shiga ďaki ta canza zanin gado ta tofe ko'ina da addu'a ta sa layun karkashin pillownta sannan ta shiga bayi ta ďauro alwala ta fito ta wuce parlor ta tarar har ya bingire a gurin yana bacci, tashin shi tayi a hankali ta kaishi ďaki ta tofeshi da addu'a ta rufeshi da bargo sannan ta shimfiďa dadduma tayi raka'a biyu, a gurin ta zaune har pss 2 tana addu'a tana tunanin abinda oyizah tasa mata a karkashin gurin kwanciyarta, a zuciyarta tace koma meye ya kare miki can Allah ya kara tsaremu daga sharrinki, mikewa tayi tana hamma ta hau gado ta kara shafa addu'a sannan ta kwanta tana kara rokon Allah ya nuna mata guraren da akayi binne binnen nan dan alfarmar annabi da hasken al qur'ani.... Ke dai kinji kunya wallahi, mutum yayi ta tusa sai kace bodari gaba ďaya kinyi polluting iskar ďaki,,, salma ke magana da karfi hancinta a toshe ta doshi parlor, fareeda ta biyota tana dariya tace ashe ba dadi kullum kike kumbura min ciki cikin dare, salma tayi tsaki ta zauna tace wallhy bana irin wannan haba wannan irin tusa haka sai kace ana kwasar kashi, fareedah ta kwashe da dariya ta koma daki tana faďin oho dai in kinga dama ki dawo ďaki ki kwanta dan 12 ta wuce, salma tace wallhy bazan kwana a dakin nan ba dan bansan wace iri zaki kuma saki cikin dare ba, fareeda ta shige ďaki tana dariya, mikewa salma tayi ta leka dakin da affan yake kwana taganshi kaca2 tayi tsaki ta wuce dakin oyizah, da murnarta ta shige ďakin ganin mummy bata ciki, kwanciya tayi akan gadon ta cigaba da chattn din da takeyi, sai gurin biyu na dare bacci yayi gaba da ita... Tun asuba esther ke kiran wayar oyizah bata ďaga ba saboda wani nannauyan bacci da yayi gaba da ita, sai gurin bakwai da rabi ta tashi babu sallah bare salati, agogon gefenta tayi saurin kallo taga 7:34
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61