Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na kwance idonshi a lumshe da radio a gefenshi yanajin labaran karfe 7 kamar yadda ya saba kullum, bayan an gama labarai akan halin da kasarmu take ciki da kuma na kasashen ketare, sai aka sako labaran kwallon kafa, cikin kosawa ya mika hannu zai kashe radion saboda sam labaran kwallon kafa basa gabanshi, tsayar da hannunshi yayi sakamakon jin sanarwar hatsari da akayi anan hanyar shigowa gari wanda akace an tsinci gawar saurayi mai suna Jabeer Bara'u, wadanda suka cinci gawar sunyi saurin mikashi ga hukumar yansanda, yanzu haka yana can asibitin Aminu kano, ga duk wanda yaji kuma yasan inda yan'uwan baw----- ay malam Atiku bai karasa sauraro ba ya diro daga kan gado yana faďin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ko takalmi baisa a kafarshi ba ya fita waje da sauri jikinshi na rawa, a kofar gida ya samu alhj bara'u zaune kan dakali, da sauri alhj bara'u ya mike yace malam Atiku lafiya na ganka haka ko takalmi babu, Malam Atiku ya saki ajiyar zuciya yace tunda na ganka zaune lfy lau ay alhamdullh, wallhy wata sanarwa naji yanzu a radio akan wani hatsari da ya faru a daren jiya kuma sai naji an kira sunan jabeer shiyasa hankalina ya tashi, Alhj Bara'u ya mike yana salati kamar zararre, malam atiku yace alhj lafy, Alhj bara'u baki na rawa yace jabeer dina ne, jabeer dina ne wallhy, tun jiya muke neman layinshi bamu samu ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, malam atiku yace lahaulu wala kuwwat illa billah, alhj bara'u ya rike hannun malam atiku ya rasa ta inda zai fara sai janshi yakeyi yana fadin muje asibitin da suka ce, malam Atiku zaiyi magana parking din motar alhj basheer ya dakatar dashi, da sauri ya fito yace lafy alhj bara'u , alhj bara'u ido zuru2 yace jabeer ya tafi, alhj basheer cikin rudewa yace ina ya tafi, malam atiku yace karka yanke hukunci alhj muje asibitin tukunna, in shaa Allahu ma bashi bane, alhj basheer yace wani asibiti, malam atiku ya fada mishi abinda yaji a radio, alhj basheer da sauri yace kuzo mu tafi asibitin, alhj bara'u da bakinshi bai daina salati ba ya shiga motar jikinshi a sanyaye suka wuce Aminu kano T.H, Tunda suka shiga gaban alhj bara'u ke faduwa har suka karasa cikin mortuary, suna shiga aka nuna musu D.L din jabeer sannan aka karasa dasu inda yake, Juyawa alhj bara'u yayi da ya kalli gawar sau ďaya ya fara addua cikin sambatu kamar tababbe, D.L din kawai yake kallo yana jujjuyashi yanaso ya gasgata shin wannan gawar ďanshi ne da gaske ko mafarki yakeyi, dafashi alhj basheer yayi yana zubar da hawaye yace alhj muje kayi signn mu amshi gawarshi muje ayi mishi sutura, alhj bara'u bai kalleshi ba yace kaima mahaifinshi kaje kayi signn din, Allah ya amshi bakuncinshi yana gama faďin haka ya fita, nurse din dake tsaye a gurin ta fashe da kuka tace alhj kuje kawai no need, Allah ya jikanshi da rahama, nan aka gunguro gawar jabeer aka sata a ambulance suka wuce gida cikin jimami suna kallon alhj bara'u da ya kurawa d.l din jabeer ido, kallon motar aka dinga yi a layin wasu suka bita dan ganin inda zata tsaya, motar na tsayawa a kofar gidan, alhj bara'u ya fito da sauri ya shiga ciki, a parlor ya tarar da Abida Amirah na tsaye a kanta da ruwan tea da magani a hannunta, kallon Amirah yayi kamar babu abinda ya faru yace har yanzu baki shirya kin wuce makaranta ba, Amirah tace nayi wanka baba yanzu zan gama in---, sallamar su malam Atiku da wadanda suka shigo da gawar jabeer ita ta hana amirah karasawa, da sauri Abida ta mike tabisu da ido har aka shimfiďe gawar jabeer a kasa, cikin firgici ta karasa kan gawar zuciyarta na dukan uku uku ta tsuguna ta buďe fuskar da tayi faca2 da jini, runtse idonta tayi da sauri tana fitar da wani irin numfashi tace nasani jabeer, zuciyata ta sanar dani, Alhamdullilah da Allah yasa aka tsinci gawarka akan lokaci, Allah ya rahamceka jabeer, yadda ka faranta mana kayi mana biyayya Allah ya faranta maka a cikin kabarinka dan nan ne gidanka na gaskiya, Allah ya sanya aljanna firdausi ta zama makoma a gareka, ta shafa fuskarshi a hankali tace na yafe maka, na yafe maka jabeer, ta mike da sauri ta wuce daki alhj bara'u ya bita, Amirah kasa gasgata gawar tayi dan gaba daya ta kasa fahimtar abinda ake nufi, ta kalli su alhj basheer da suke sharar hawaye tace daddy, Abba, me ya samu yaya jabeer, alhj basheer yace Amirah addua zakuyi mishi dan wanda ya fimu sanshi ya karbi abinshi, Amirah ta saki kofin hannunta ta tsuguna a gabanshi tana kuka mai tsanani tana kiran sunanshi, da kyar alhj basheer ya rarrasheta yasa Dayyaba dake tsaye tana kuka ta shiga da ita ciki, Mahmud kanin Afeeyah ya shiga gida da gudu ya ajiye biredin da ya siyo a tsakar gida ya karasa ďakin hajja, hajja na zaune tana gyaran wake, Afeeya kuma tana kwance jikinta ya ďau zafi sosai saboda zazzabi, fadowa dakin mahmud yayi, hajja tace haba mahmu irin wannan shigowar ba sallama ay sai ka tsoratani, yace hajja motar gawa ta asibiti na gani kofar gidan alhj bara'u kuma naji mutane suna cewa yaya jab-- Afeeya ta diro daga kan gado tayi ma mahmud wani irin riko tace me ya sameshi, mahmud cikin jin zafin rikon yace ban sani ba mutane sunce sunga an fito dashi cikin jini... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣2⃣ By Aysha Ya'u Kurah Wurgi Afeeyah tayi da mahmud ta fita da gudu, duk irin kiran da hajja take mata baisa ta tsaya ba, da gudu ta shiga gidan ta tarar dasu baba ado zaune da wasu mutane sunyi tagumi a bakin gate, da sauri ta karasa kusa dashi tace baba ado me ya samu yayana?, baba ado ya kauda kanshi da sauri yana share hawayen dake zuba a idonshi, Afeeyah ta bar gurin da gudu ta shige cikin gidan, murďa kofar parlon tayi da karfi kamar zata balleta, tana shiga ta dinga bin mutanen dake parlon da kallo, ganin mutum kwance cikin jini a kasa yasa zuciyarta bugawa da karfi, a hankali ta fara motsa kafarta tana tafiya har ta isa gabanshi, tsugunawa tayi ta yaye abin da aka rufe mishi fuskarshi da shi, gaba ďaya hanyoyin sadarwa na jikin Afeeyah suka daina aiki sakamakon ganin fuskar jabeer, kallonshi ta tsaya yi bata ko kiftawa, alhj basheer ya taso ya karaso gurinta ya ďagota dakyar dan jikinta a sake yake kamar wacce bata da rai, zaunar da ita yayi akan kujera ya fara mata nasiha, ko kaďan bataji abinda yake cewa ba idonta na kan jabeer da alhj bara'u da mahaifinta ke kokarin ďaukarshi suyi mishi wanka, alhj basheer ya girgizata yace Afeeyah kina jina, lumshe idonta tayi lokacin da aka fita da gawar, alhj basheer zaiyi magana hajja ta shigo da gudu tana faďin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me yasamu jabeer alhj, na shiga uku na lalace, alhj basheer yace dan Allah hajja kiyi shuru kar gidan ya rikice adduarmu jabeer yake bukata ba

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});