Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

so dalilin da yasa na kara kiranki kenan dan inyi miki albishir, oyizah ta saki wata kara mai rikirtarwa ta mike ta shige ďaki tace esther jinin salma kuka sha, esther tace wai ko kin haukace ne, har kiranki fa nayi da safe kikace kina sane kika bayar, oyizah tace wayyyo na shiga uku, ni ba salma na bayar ba Afeeyah na bayar, ya za'ayi in bada salma, esther tace ha'a to ya akayi muka ga salma, oyizah tayi wurgi da wayar hannunta ta yaye zanin gadonta, nan tayi arba da farin kyalle, cikin firgici ta fara shafa kyallen tana fadin ya akayi wannan kyallen yazo nan gurin, waye ya kawo wannan kyallen nan,? waye ya kashe min salmata ta fadi cikin karaji,? da sauri farida ta shigo dakin ta riketa tana rarrashinta tace mummy dan Allah ki daina wannan ihun kinga mutane suna ta kara yawa, oyiza ta hankaďa ta tace sun ci kutumar ubansu mutanen, nan ta fara zage2 tana tsinewa mutanen da suka zo mata gaisuwa cikin ficewar hayyaci, saida farida ta kirah alhj basheer yazo ya lallabata da kyar sannan tayi shuru tana ajiyar zuciya, gaba ďaya ta dauki tunaninta kacokan ta maida shi gurin gano yadda akayi abin da ta shimfiďa ma Afeeyah ya dawo dakinta, yanzu su chummy basuyi ma diyarta lamuni ba suka zuke jininta ba tare da sun tambayeta ba, lallai sun taro match dan wallhy sai tasan yadda akayi wannan kyallen ya dawo dakinta sannan kuma sai ta nuna ma su chummy bacin ranta,, Tun ranar da salma ta mutu nutsuwa tayi ma oyizah tawaye, kullum cikin mafarke2 take tana bakin cikin yadda akayi aka bada ďiyarta a cikin kungiyarsu ita kuma shegiyar kungiyar mai lakabin sabo da kaza baya hana a yanka ta, in ba haka ba ay sunsan yadda takeson yayanta kamar yar ranta, a ranar da akayi uku ne ta fara shirin zuwa gurin meeting dan ta warware musu kuma a binciko mata dalilin da yasa wannan farin kyallen ya koma ďakinta..... Mrs tijjani shattima... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣2⃣ By Aysha Ya'u Kurah Karfe biyun dare suka hadu a gurin meeting kamar yadda suka saba, oyizah na zaune gaban chummy bayan ta gama masifarta sai cika takeyi tana batsewa, Chummy ta dafa kanta tace oyeee naji duk bayanan ki , kuma na fahimci fushinki, amma kinsan mu nan duk wanda aka kawo baya tafiya ba tare da munsha jinin shi ba ko, mistake din daga gareki yake tunda ke kika shimfiďa farin kyallen, oyizah cikin fushi tace ba a dakina na shimfiďa ba my lord a dakin yarinyar da na bada anan na shimfiďa bansan yadda akayi ya dawo ďakina ba, alhj sambo ya kalleta yace haba oyizah dan kin bada yarki daya shine kike ta wannan fushin, ni yayana biyu na bayar da kannena biyu da nake matukar so, a hassale oyizah tace abin da kake nema ne dole sai kayi wannan sacrifice din, ni ay na riga na bada nawa wannan kyauta na bayar saboda kungiya taji dadi, esther tace calm down oyee, chummy tace barta ta cigaba, ta manta duk abinda kungiya tayi mata ne, ta manta da irin rufin asirin da mukayi mata, ta manta da duk wani wanda zai tona asirinta mun kawar mata dashi saboda tasamu nutsuwa a gidan aurenta, ta manta yadda muka mallaka mata alhj basheer , ta manta yadda muka lalata rayuwar dan kishiyarta ita kuma muka mayar da ita matacciya alhali tana raye, oyizah ta sunkuyar da kanta kasa tace am sorry my lord, ni ba fushi nayi ba, kawai dai ina son in san wanda yayi min wannan aikin ne, chummy ta janyo wani kokon tsafi ta fara bincikenta cikin kwarewa dan gano wanda ya canza farin kyallen, a wannan lokacin kuma Afeeyah na zaune kan dadduma tana kallon gabas tana rokon Allah ya karesu daga dukkan sharrin masu sharri, Babu irin duban da chummy batayi ba amma sam bata ga komai ba sai duhu da ya mamaye kwaryar, ajiye kwaryar tayi hannunta na rawa tace kaii oyee gaskiya na kasa gane ko waye, kar mu zurfafa bincike ko ma waye zamu gane shi wata rana, kedai kije ki cigaba da mulkinki kamar yadda kika saba tunda babu wanda ke taka miki birki, cikin damuwa oyizah ta ďago da niyyar faďin damuwarta akan Afeeyah amma ta kasa, daga ta bude baki zatayi magana sai taji wani abu na mata yawo a makoshinta, sai gab da asubahi suka fara bacewa suna komawa gidajensu, har lokacin bakin oyizah naso ta furta sunan Afeeyah amma ta kasa, gurin wata kwalba suka je wacce ke dauke da gunki a cikinta, d'aga kwalbar chummy tayi tana dariya ta mayar ta ajiye tace haka kishiyarki zata dawwama babu motsi a duk inda take, fanne da fanna dake cikin wata kwalba sukace saidai in bamu fita anan ba, wallhy muna fitowa zamu fasa kwalban nan, oyizah ta buga glass din tace to dan ubanku ku fito mu gani, fanne tayi dariya tace wit tym, chummy tace rabu dasu oyee tafi gida sa'a na tare dake a ko da yaushe, ta russuna kamar zata mata sujjada tace thank you my lord..... Kwanan salma biyar da mutuwa har lokacin oyizah bata walwala, kullum sai tayi kuka saboda yawan mafarkin salma da takeyi, alhj basheer da farida kaďai ke tausarta se kuwa a gurin meeting dinsu, sam ta tsani ganin Afeeyah dan gani takeyi sanadiyyar Afeeyah ta rasa yarta, jira kawai takeyi ayi sadakar bakwai tayi wani aikin akanta dan wannan karan da hannunta zata kashe shegiya, mugun shiri takeyi akan Afeeyah dan so takeyi tayi mutuwar wulakanci,,,, Afeeyah kuwa hankalinta kwance yake dan kula sosai takeyi da mijinta da take ganin yar nutsuwa a tare dashi kwana biyun nan, shi kanshi hankalinshi a kwance yake saboda daina ganin salma da yayi kwana biyu, karfe 5 na yamma ta gama girkinta sukayi wanka suka shirya cikin kyakyawar shiga sai kamshi sukeyi, dakin oyizah suka shiga Afeeyah ta tsuguna ta gaisheta tayi mata ya hakuri, ko kallonta oyizah batayi ba idonta nakan Affan tana hararar shi, boye fuskarshi yayi a bayan Afeeyah yana leken fuskar mummy da har lokacin bata daina hararar shi ba, mikewa Afeeyah tayi tace sai anjima mummy, oyizah ta bita da mugun tsaki tace za kici ubanki ne, Ta wani corridor taja shi tace yau ta nan zamu bi, kasan tunda nazo gidan nan ban hau gurin nan ba, yayi dariya yace to muje amma fa mummy tace akwai su lions a gurin, Afeeyah tace haba dai babu komai muje may be basa so ka hau ka fado ne, runtse idonshi yayi yace muje amma bazan bude ido na ba, dariya Afeeyah tayi taja hannunshi suka hau can saman gidan, sakin hannunshi tayi da sauri tana fadin Wowww amma gurin nan ya hadu, bude hannunta tayi ta lumshe idonta tana shakar iskar gurin flowers sai kaďawa sukeyi, da gudu taje bayanshi ta fara mishi cakulkuli tana faďin ka buďe idonka ka gani babu komai a gurin sai flowers masu kamshi, dariya yake ta kyakyatawa sannan ya buďe idonshi a hankali, wasu shuďaďďun abubuwa ya dinga gani suna mishi yawo a cikin kwakwalarshi da kwayar idonshi, sosai yake

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});