Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Rabo Ajali Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kara zama shuru kafin ta tashi tayi musu sallama haďe da jaddada ma hajja akan ta kula da Afeeyah ta dinga cin abinci akai2, cikin mamaki hajja ta kalli Afeeyah tace kin ga matar nan yadda ta canza kamar ba ita ba, gaskiya naji dadin yadda ta nuna kulawarta gareki ga dukkan alamu ta saduda ta fara sonki, Afeeyah ta juyar da kanta gefe a zuciyarta tace kwarai kuwa tana matukar son kasheni hajja ai dole ta kula dani kafin hakanta ya cimma ruwa, buďe kulolin abincin hajja tayi tana fadin masha Allah irin wadannan namomi haka, Afeeyah tayi saurin mikewa tace hajja dan Allah a ina zan samu agwaluma ko cashew anan gurin, hajja tace aiko akwai wani mai agwaluma da na gani anan waje bari in duba Allah yasa bai tafi ba, Afeeyah tace ameen dan Allah hajja ya baki mai tsami sosai, hajja tace to ta fita da sauri, tana fita Afeeyah ta mike ta kwashi kulolin abincin tayi waje dasu ta zuba a bola tayi saurin komawa daki, ko minti biyar hajja batayi ba ta dawo da agwaluma cikin leda ta mika mata, kwanciya Afeeyah tayi ta dauki agwaluma daya ta fasa ta fara sha, salatin hajja ne yasata juyowa da sauri tace lafiya hajja, hajja tace kulolin ne naga babu komai, Afeeyah tace eh na cinye baki ga dama na mutum daya ta yi ba, hajja tace daga fita ta har kin cinye, Afeeyah tace eh mana to nawa abincin yake, hajja tace shine dan bakar mugunta ko naman baki ragemin ba, Afeeyah tayi dariya tace ke kuma nama ne aranki sai kace wata kurah, hajja tace waya sani ko kurar ce gaskiya kin shiga hakkina, Afeeyah tace karki damu hajja nah anjima nasan zamu samu wasu naman, hajja tayi tsaki ta tashi ta fita wanko coolers din... Bayan isha'i kaka liman ya dawo asibitin, sun dade suna hirah da hajja kafin ta basu guri shi da Afeeyah, kaka liman ya kalli Afeeyah yace dazu muna magana bamu gama ba na tafi, yanzu sai muyi sauri dan naji gobe za'a sallameku ko, Afeeyah tace eh, kaka liman yace nima goben zan koma, da fatan duk abubuwan da na fada miki dazu kin fahimcesu ko, Afeeyah ta gyada kanta, yace yauwa to yanzu sai ki faďa min abinda kika gani, nan Afeeyah ta faďa mishi duk abinda ta gani jiya da daddare, kaka liman ya jinjina kanshi yace wannan shine abinda nakeso Allah ya nuna miki dan nasan da na faďa miki hakan tun farko to tsoro bazai barki ki shiga gidan ba ma bare har tausayin affan ya shigeki ki yarda da taimakon da zakiyi, wannan abun da kika gani shi jabeer ya gani amma nashi ya banbanta da naki saboda shi yaji suna tsafin ne akan Affan da mahaifiyarshi, shin tunda kika shiga gidan kinji ko sau ďaya alhj yayi maganar zeenatu, Afeeyah ta gyada kanta, kaka liman yace to bashi ba ma har yan uwanta da makusantanta basa iya maganarta ko ke kin taba tuna ta tun bacewarta, cikin mamaki Afeeyah tace a'a kaka, kaka liman yace mugun asiri akayi mata, karyewar asirin na farko shine jin da jabeer yayi mata har ya sanar da ni, a aikin da nayi na gano laya ce aka turata cikin bakin DAMO aka binne ta anan cikin gidan da kuke, Afeeyah ta zaro idonta tace a cikin gidan? yace kwarai kuwa, sannan duk wasu asiran da tayi a cikin gidan ta binnesu da yawansu bansan takamaimai inda ta binne ba amma suna cikin gidan, in har Allah ya taimakemu muka san inda suke har muka ciresu to saukin abun yazo dan mun riga mun gama wasu ni da jabeer karashen ne wannan kuma sune masu wahalar, Afeeyah ta jinjina kanta tace to kaka ya za'ayi musan inda tayi binne binnen, kaka liman yace shine yanzu abinda nake tunani, hannu yasa a aljihu ya ciro wata bakar leda, bude ledar yayi ya fito da wasu layu guda biyu da wani ruwan turare sai garin magani, layun ya fara mika mata yace rike wadannan layun, dafatan zaki jajirce akan duk abinda zaki gani, Afeeyah tayi kulu kulu da ido tace kaka banyi yarinya da daukar wannan kasadar ba kuwa, kaka liman yayi dariya yace Afeeyah kenan sai kiga abinda zakiyi ni bazan iya yinshi ba saboda wani lokacin kwakwalwar yaro tafi ta babba kaifin rike abu, Afeeyah ta gyada kanta tace to Allah ya bani juriyar iyawa yace ameen abinda ya kamata ki fadi kenan, wadannan layun a karkashin pillown ki zaki sasu, in zaki kwanta kiyi alwala kiyi sallah kiyi addu'a sosai akan Allah ya bayyana miki guraren da akayi wadannan binne binne, sannan ki shafa wannan turaren a jikinki ki kwanta kina mai kyautata niyya, in shaa Allah cikin kwana bakwai Allah zai nuna gurin da suke, duk wani abun tsoron da zaki gani na rokeki ki daure kar wannan tsoron ya sare gwiwarki, ke kadaice garkuwar bayin Allahn nan, in har kika sare to ki sani babu wani wanda zai iya daurewa yayi wannan aikin, Afeeyah ta gyaďa kanta tace in shaa Allahu kaka zan daure, nasan ina tare da Allah da kuma kai, yace masha Allah, sannan wannan maganin ki dinga ba Affan yana sha, kafin kwana bakwan nan zai dinga yin wasu abubuwa wadanda zasu dinga dawo dashi cikin hayyacinshi ya dinga tunanin abubuwan mamakin da suka faru dashi a shuďaďdun lokuta, kin gane bayanin ko, Afeeyah ta gyada kanta tace eh na gane, to amma kaka yaya zanyi in na gansu, kaka liman ya mike yace wannan kuma shawararki ce, in kiga zaki iya ciresu ki taimaki uba da kakar abin dake cikinki to in kuma zaki barsu su dawwama a haka nidai na gama nawa yanzu naki kadai ya rage sai mu barma Allah sauran, Afeeyah tace to kaka nagode sosai, ya miko mata wayarshi yace samin numberki kiyi flashing in wani abu ya shige miki duhu kya nemeni, Afeeyah ta amsa tasa mishi numbrta sukayi sallama ta bishi da kallo har ya bace ma ganinta , ganinshi kadai yana kwantar da hankalinta, badan tsufan shi ba da babu abinda zai hana a kirashi da jabeer dinta.... Mrs tijjani shattima..... [15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah Karfe 9 na safe aka sallameta suka ďunguma zuwa gida a motar alhj basheer, oyizah na zaune a parlonta tana gyara farce hankalinta sam ba'a kwance yake ba dan tun jiya take jiran jin mummunan labari game da Afeeyah amma shuru gashi har gari waye, Shigowar motar alhj basheer ne yasa ta mike ta kwashe kayan gyaran kumban dan taje ta tarboshi ko zataji wani labari a gurinshi, tana buďe kofar parlon tayi tozali da mai taurin kashi wato Afeeyah, kallon mamaki ta tsaya yi mata a zuciyarta tace to ko karya hajja take mata yarinyar nan bata ci abincin ba, Afeeyah ta katse mata zancen zucin da takeyi tace ina kwana, oyizah ta sauke ajiyar zuciya tace lafiya lau ta juya ciki bata ko bi takan hajja dake rike da kaya ba, Side dinsu ta wuce tana kallon hanya ko zata ga Affan, da bismillah ta murďa kofar dakin suka shiga ita da hajja, bayi

Table of Contents

Chapters

61 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});